Tawassuli (Kamun Kafa)1
Tawassuli (Kamun Kafa)1
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Tsarin duniya yana bisa ka'idoji da dalili a kan komai, saboda haka duk wani abu wanda zai faru a duniya yakan faruwa tare da dalili wanda ya kebanci shi abin da ya farun, sannan shi ma wannan abin da ya faru zai tasiri ga wani abu na daban, tasirin da wani abu yake sanya a cikin wani daban duk yana faruwa ne da izinin Allah madaukaki. Allah shi ne wanda ya halicci duniya sannan ya sanya alaka tsakanin abubuwan da suke duniya ta yadda wasu sukan yi tasiri a cikin wasu. Babu shakka rana tana bayar da wani sinadari wanda sauran halittu suke amfani da shi don su rayu, haka nan wata yana bayar da haske, sannan wuta tana bayar da zafi. Dukkan wadannan abubuwa suna yin tasiri ga waninsu, sannan akwai alaka ta musamman tsakanin rana da wata da wuta da kuma abin da suke bayarwa. Sannan dukkan wannan tasirin da ake gani babu wanda yake sanya shi sai Allah wanda shi ne ya halicce su, sannan kuma shi ne ya sanya wannan alakar da take akwai abin da yake faruwa tsakanin abubuwa daban-daban, kuma dukkansu suna samuwa daga gare shi maudakaki. Sakamakon haka ne wani lokaci yakan dauke tasirin da abu yake da shi, kamar yadda ya dauke zafin wuta ga annabi Ibrahim (a.s) ya kuma daidaita ta tamkar wani lambu mai sanyi, wannan kuwa duk don ya nuna cewa daga gare shi ne dukkan wannan tasirin na hakika yake da kuma niyyarsa ne.
Daga wannan bayanin muna iya daukar sakamako cewa: duk wani abu wanda yake faruwa a cikin duniya muke ganinta, a lokacin da muke ganin cewa ta samu ne daga wani abu daga cikin abubuwan da suke a cikin duniya, a daida- wannan lokacin kuma suna zuwa ne daga Allah kuma aikinsa ne. Sannan wannan abin bai saba wa hankali ba ta yadda za a ce ba zai yiwuwa ba. Domin kuwa Allah shi ne wanda yake da cikakken iko yake kuma yin wani abu ba tare da taimakon wani ba, amma dukkan wani yayin da zai aikata wani abu sai da taimakon Allah. wato duk abin da suke aikatawa tare da izinin Allah suke aikata shi, don haka muna iya cewa su ne suka aikata kuma muna iya cewa Allah ne domin kuwa a hakikanin gaskiya shi ne ya aikata, domin kuwa da bai bayar da izini ba, ba za ayi hakan ba.
Sannan kowa ya san daya daga cikin matakan tauhidi ko kadaita Allah shi ne kataita Allah a cikin halitta, wato babu wani mai halittawa sai Allah madaukaki, amma duk da haka kadaita Allah a cikin halittawa ba yana nufin kore duk wani tasiri daga wani abu ba, wato ma'anarsa shi ne halitta ba tare da dogara da wani ba, shi kadai ne yake iya yin haka, sannan duk wani tasiri na sauran wasu halittu yana samuwa ne da izinin Allah.
A cikin wasu ayoyin an yi nuni da dukkan wadannan nau'o'i guda biyu na yin tasiri. Misali aiki guda a daidai lokaci guda ana a jingina shi zuwa ga Mutum, sannan kuma ana jingina shi zuwa ga Allah, duk da cewa aiki guda yana gangarowa ne kawai daga abu guda. Amma tunda wadannan masu aikin daya yana karkashin daya ne babu matsala, wato daya shi ne na asali dayan kuwa yana bin na asalin, saboda haka babu abin da zai hana hakan.
Allah yana cewa wa Manzo (s.a.w): "Ba kai ne ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa". A nan Kur'ani yana jingina aiki guda daya zuwa ga masu aiki guda biyu kamar haka:
1- Lokacin da ka yi jifa.
2- Allah ne ya yi jifar.
Dukkan wannan jinginawa guda ta yi daidai kuma ta dace da wurin, domin kuwa aikin Manzo ya faru ne da taimako da izinin Allah, saboda haka jingina wannan aiki guda daya ga dukkansu ya yi daidai. Sannan kamar aiki guda a jingina shi ga Allah sannan a jingina zuwa ga wani daban ya zo da yawa a cikin Kur'ani. Amma a nan kawai zamu bayar da misali guda biyu kawai:
1-Kur'ani a lokaci guda yana jingina rubuta ayyukan bayi zuwa ga mala'iku, sannan a wani wurin daban yana jingina wannan aiki zuwa ga Allah madaukaki.
2- A wani wuri ana jingina daukar rayukan mutane zuwa ga mala'ikun mutuwa, amma a wani wuri ana jingina wannan aiki zuwa ga Allah. Wadannan ayoyin suna bayyanar da yadda tsarin halitta yake karkashin ka'idar tasiri da mai tasiri, ta yadda abubwan da suke fauwa suke tasiri tsakanin juna. Amma dukkan wannan tsari suna jingina ne zuwa ga Allah madaukaki, sannan a karkashin nufinsa da izininsa suke ci gaba da rayuwarsu. Saboda haka duk wani abu wanda yake yin tasiri a cikin tsarin duniya, yana karkashin rundunar Ubangiji ne sannan kuma aikata abin da Allah ya umurce su ne. Sannan Allah kawai ne ya san yawan wannan runduna ta Allah.
Tare da la'akari da wannan bayani, wanda yake matsayin nuni daga wahayi, (cewa babu mai halitta da gaskiya sai Allah) sakamakon binciken dan Adam na ilimi (ta yadda suka tabbatar da yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu a cikin duniya) ba ya nuni da sabani a kan abin da muka ambata kokadan. Wadanda suke ganin wahayi ya saba wa ilimi ko kuma addini ya sabawa ilimi, ba su yi kyakkyawar fassara ba ne a kan hakan. Ko kuma sun yi wa ilimin zamani mummunar fahimta. Da wata ma'anar kuwa, duk wadannan abubuwa guda biyu na kasa sun dace kuma sun yi daidai su ne kamar haka:
1-Imani da kadaita Allah a cikin halittawa cewa babu wani wanda yake yin wani abu ba tare da dogara da wani ba sai Allah.
2-Tasirin wasu abubuwan a cikin wasu ayyuka dukkansu suna faruwa ne da izinin Allah da nufinsa. Idan muka ga wadannan asali guda biyu wani lokaci suna karo da juna, wannan ya samu asali ne ta yadda wasu suke fassara kadaita Allah a cikin halitta da wata ma'ana wacce ba ta inganta ba. Ta yadda suke daukar babu wani mai yin wani abu sai Allah kawai, wato duk wani mai yin wani abu, ba shi yake yin abin ba, kawai Allah ne yake yin komai, dan Adam ba shi da hannu wajen yin ayyukansa (nazarin Asha'ira). Ko kuma kamar yadda wasu suke ganin bayan wadannan abubuwan da muke gani a cikin duniya suna da tasiri ga wasu abubuwa, babu wani da sunan Allah wanda yake da tasiri a cikin duniya, wato duk abin da mutum ya yi daga gareshi ne babu hannun Allah a cikin. (Nazarin wadanda ba su yarda da wani abu ba a bayan wannan duniyar da muke gani).
Saboda haka dukkan wannan fahimta guda biyu kuskure ce kuma ba ta inganta ba, wanda dukkan biyun yana nuni ne ga takaitawa da kuma wuce wuri. Rashin ingancin fahimta ta biyu kuwa ya faru ne sakamakon yadda suke ganin duniya kawai ta takaita ne ga wannan duniya da muke gani kuma muke iya jinta, wato ba su yi imani da duniyar gaibu ba, wanda ba ya bukatar wani Karin bayani. Domin kuwa a nan muna magana ne da wadanda suka yi imani da Allah kuma suna ganin rashin ingancin akidar daukar wannan duniyar ita ce kawai kuma babu wani abu a bayanta. Amma rashin ingancin fahimta ta farko kuwa yana komawa ne ga wasu daga cikin malaman akida wadanda suka tafi a kan wannan fahimta, alhali kuwa Allah madaukaki a fili yana nuna yadda halittu suke da tasiri a cikin rayuwa, wajen faruwar wasu abubuwa. Sannan kuma kowa zai iya shaida hakan domin kuwa wani abu ne wanda muke gani da idanummu.
Saboda haka ta yaya zamu ki yarda da tasirin da halittu suke da shi a cikin rayuwa, shi kuwa wahayi yana bayyana gaskiyar wannan al'amari. A matsayin misali yana bayyanar da ruwa a matsayin wanda yake da tasiri wajen rayuwar tsirrai, kamar yadda yake cewa: "Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya gina muku sama, Kuma yana saukar da ruwa daga sama, sannan yana fitar da 'ya'yan itatuwa daga ruwa wadanda arziki ne a gare ku. "
Saboda haka nufin Allah ya yi rigaye a kan cewa duk da cewa dole ne mutum ya yi imani da cewa komai yana zuwa ne daga Allah, amma duk da haka mutum dole ne ya tanaji wasu abubuwa wadanda zasu kai shi zuwa ga cimma abin da yake nema.
Wannan asali da ka'ida kuwa, tana gudana har da abubuwan da suka shafi shiryarwa da makamantansu, sakamakon haka ne Allah madaukai ya bai wa mutum wata halitta a cikin zatinsa wacce zata taimaka masa wajen yin imani da Allah, haka hankali, annabawa da malamai da masana da makamantan wannan, Allah madaukaki ya sanya su a matsayin wadanda zasu yi mana jagora domin mu samu shiriyar Ubangiji. Kamar yadda ya kasance a wasu wurare a cikin Kur'ani mai girma Allah yana bayyana cewa shiriya wani abu ne daga gare shi, kamar inda yake cewa: "Yana batar da wanda ya so yana kuma shiryar da wanda ya so" .
Sannan wani wurin yana cewa: "Lallai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya".
Sannan babu karo da juna don an jingina shiryarwa zuwa ga dukkansu su biyun, wato asalin shiryarwa yana ga Allah, sannan Manzo wanda yake kamar sila ne na aiwatar da wannan aiki, babu laifi a jingina wannan aiki zuwa gare shi.
Takaitaccen tunanin wasu wadanda suke aibata kasantuwar tasirin wasu halittu ya samu asali ne sakamakon rashin fahimta mai kyau a kan koyarwar Kur'ani mai girma kamar yadda suke ganinsa ya saba da azirtawar Ubangiji da kuma tawakkali da shi, don haka ne ba su iya fassara koyarwar Kur'ani ba da kyau kamar yadda ya kamata.
Kasantuwar tasirin wasu daga cikin abubuwan halitta, sama ba ya karo da tawakkalli ko kadaita Allah a cikin tafiyar da al'amura, haka nan a cikin kadaita Allah a cikin ayyukansa. Domin kuwa a wajen mutum mai tauhidi wanda kuma yake da ilimi, dukkan wasu abubuwan da suke tasiri a cikin rayuwa suna yin wannan tasiri ne a karkashin inuwar Ubangiji da izininsa. Sannan yana ganin duk wani tasiri da yake a cikin duniya yana bayyana nufin Ubangiji wanda ba shi da iyaka wajen aikinsa kuma wanda ya halicci duniya baki daya.
Sannan dangane da bukatun ruhi da na zahiri a wajen hakan, babu wani bambanci. Sakamakon haka ne Allah yake umurtar masu imani da su tashi domin su yi kamun kafa a wajensa inda yake cewa: "Yaku wadanda kuka yi imani, ku ji tsoron Allah, sannan ko nemi tsani zuwa gare shi, Kuma ku yi jihadi a tafarkin Allah ko kun rabauta".
A nan dole mu yi bincike a kan ma'anar wannan tsani da aka ambata a aya ta sama me ake nufi da shi?
Marubuta kamusun lugga sun bayani a kan yadda ake amfani da lafazin wasila cikin harshen larabci kamar haka:
1-Makami da matsayi: a wani hadisi Manzo (s.a.w) yana cewa: "Ku nema mini matsayi a wajen Allah"
2- Kusanci zuwa wajen Allah.
3- Samar da abubuwan da zasu kusantar da mutum ta yadda zai samu kusanci zuwa ga Allah.
Tabbas ma'ana ta farko ba ita ake nufi ba a nan, domin kuwa matsayin da Manzo yake da shi a wajen Allah babu wanda yake da shi, kuma babu wanda zai samu kamarsa. Saboda haka dole ne mu fassara wannan aya da daya daga cikin ma'anoni biyu na karshe, kuma ga dukkan alamu wannan aya tana daukar ma'ana ta uku ne, domin kuwa abin da yake tabbatar da hakan bayan an yi umarni da neman tsani, yana yin umarni da jihadi wanda yana sanya kusanci zuwa ga Allah. Sannan wannan ya zo a cikin hadubar Imam Ali (a.s) wanda ya dauki ma'anar tsani da cewa shi ne riko da abin da zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangiji, inda yake cewa: Mafificin abin da masu neman kusanci zuwa ga Allah zasu nemi kusanci zuwa gare shi, shi ne yin imani da shi, da manzonsa da yin jihadi a tafarkin Allah, sannan da tsayar da salla domin kuwa hanya ce kuma shari'a ce, sannan fitar da zakka.
A cikin wannan huduba ta Imam yana kawo wajibai na shari'a wanda yake nuna cewa su ne suke kusantar da mutum zuwa ga Allah. Ayar da aka ambata a sama, tare da hukuncin hankali tana yi mana nuni ne tana cewa: Dan Adam, wajen samun daukaka ta ruhi kamar kusanci zuwa ga Allah, kamar yadda ya kasance yana neman abin da zai biya bukatunsa na duniya, suma haka dole ne ya nemi abin da zai kusantar da shi zuwa ga wadannan abubuwan da yake bukata na ruhi, sannan ba tare da wannan ba mutum ba zai iya cimma abin da yake bukata ba.
Abin da yake akwai a nan shi ne abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah dole shari'a ce zata bayyana su. Domin kuwa hankalin dan Adam ba zai iya gano wadannan abubuwan ba, ta yadda zai gano abubuwan da zasu kusantar da shi zuwa ga Allah da abubuwan da zasu kai shi zuwa ga gafara da makamantansu, sannan bai kamata ba a nan wani ya yi tunanin cewa da wannan ayar ne kawai za a iya kafa hujja a kan ingancin kamun kafa da annabawa da waliyyai. Wannan aya kamar wata ka'ida ce ta baki daya wacce kuma hankali yake hukunci a kan ingancinta, amma dangane da abubuwan da zasu kusantar da mutum ko su sanya ya samu gafara ko ya samu biyan bukatunsa na ruhi, hankali ba zai iya gane wannan ba, saboda haka dole ne Allah ko manzonsa da ma'asumai (a.s) su bayyanar da hakan. Kamar yadda imam a huduba ta sama yake bayyanar da cewa imani da Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah, da tsayar da salla da bayar da zakka suna daga cikin muhimman abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012