Tawassuli (Kamun Kafa)3
Tawassuli (Kamun Kafa)3
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Ibn Taimiyya Da Mabiyansa
Ibn Taimiyya da mabiyansa suna cewa: Neman addu'a daga Manzo ya kebanta ne da zamanin rayuwarsa ne a duniya kawai, don haka wannan ba ya halatta bayan wafatin Manzo! Haka ne zai yiwu mutum ya ziyarci Manzo, sannan ya yi addu'a a gefen kabarinsa sannan ya nemi abin da yake so a wajen Allah.
Dangane da amsar wannan magana kuwa zamu yi fadakarwa a kan cewa, dole ne a fahimci matsayi da darajar Manzo a wajen Allah, wato matsayin da zai sanya al'ummar musulmi masu zunubi su zo wajensa domin ya nema musu gafarar Ubangiji ta yadda addu'arsa karbabba ce.
Shin wannan matsayi da daraja ta Manzo ya samu asali ne daga jikinsa ko kuwa wani abu wanda ya shafi rayuwar duniya, ta yadda sakamakon wafatinsa zai kawo karshe, ko kuwa wannan matsayin sakamakon tsarki da daukakar ruhinsa ne?
Ra'ayi na farko kuwa ya saba wa hankali da shari'a, domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a cikin bahsin rayuwar barzahu mun ga yadda ya kasance cewa; hakikanin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sannan mun ga cewa ruhin mutum bayan rasuwarsa zai ci gaba da rayuwa a rayuwar barzahu, wato mutuwa ba yana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba ne da rayuwa a wata duniyar ta daban. Don haka matsayi da daukakar Manzo ta samo asali ne daga girma da daukaka na ruhinsa, don haka bayan wafatinsa wannan matsayi yananan kamar yadda yake lokacin da yake a raye.
Sannan a bahsimmu da ya gabata mun tabbatar da kasantuwar alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ta yadda suna jin duk abin da muke fada.
Tare da kula da abin da muka ambata, ayar da muka ambata a baya ba ta kebanta da lokacin rayuwar Manzo ba, kuma riko da hakan wani abu ne marar dalili. Sannan zamu tambayi wadanda suke inkarin kamun kafa da Manzo da cewa: me ya sanya bai halatta a yi kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa ba? Shin don ya kasance ne duk wani girma da daukaka da kusanci ya samu ne a gare shi sakamakon yanayin jikinsa ne, ta yadda sakamakon rasuwarsa wannan matsayin da kusancinsa a wurin Allah zai kawo karshe?! Shin mutuwa shi ne karshen rayuwar mutum ta yadda Manzo bayan wafatinsa ba shi da sauran rayuwa?!
Shin sakamakon wafatin Manzo shi kenan ba mu da sauran wata alaka da shi?!
Amsar dukkan wannan tambayoyi kuwa ita ce; a 'a, don haka dole ne mu amince da cewa kamun kafa da Manzo a dukkan lokuta guda biyu (rayuwa da rasuwarsa) babu bambanci.
Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa, Sheikh Khalil Ahmad saharnafuri ya tattara fatawowin malaman AhlusSunna 75 dangane da halascin kamun kafa da Manzo.
A cikin wannan littafi da muka ambata a sama, an yi Karin bayani da cewa: A nazarimmu da manyan malamammu shi ne, ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan hanyoyi wajen neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, sannan yana daya daga cikin muhimman ayyuka masu lada kuma wata hanya ce domin samun matsayi da daraja madaukakiya. Wannan kuwa wani umarni ne wanda yake kusa na wajibi da farillai na shari'a, madamar isa zuwa ga hakan ba zai janyo tsanani ko asarar rayuwarka ba. Kamun kafa kuwa da annabawa da waliyyai da manyan bayin Allah, shahidai da siddikai, a cikin addu'a a lokacin rayuwarsu ne ko kuwa bayan rayuwarsu ya halatta.
Tambayoyi Da Amsoshi
Dalilai a kan halascin kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa wani abu ne wanda ya bayyanar mana. Amma dangane da hakan akwai wasu tambayoyi wadanda dole ne mu bayar da amsarsu.
Tambaya ta farko: Shin neman addu'a daga mamaci shirka ne?
Wasu suna tunanin cewa neman addu'a daga wanda yake raye, wato yana iya yin addu'ar wani abu ne wanda ya halasta, amma yin haka ga mamaci shirka ne. Amma shin wannan tunani daidai ne?
Abin da ake nufi da shirka kuwa a cikin wannan tambaya da tagabata shi ne shirka a cikin ibada, (hadallah da wani a cikin bauta) wato neman addu'a daga mamaci yana nufin yi masa bauta kenan.
Wannan tunani na sama sam ba ya inganta, saboda:
Na farko: Idan neman addu'a ga mamaci yana nufin yi masa bauta, to wannan ya nuna cewa neman addua'a daga mutumin da yake a raye shi ma yi masa bauta ne domin kuwa babu bambanci, domin kuwa neman addu'a ne tare da kaskantar da kai, don haka wadanda suke ganin neman addu'a daga wanda yake raye ba ya nufin bauta masa ba ne, don haka dole ne su amince da cewa yin hakan bayan rasuwa ma ba yana nufin bauta ba ne, ballantana ya zama shirka ko sabanin tauhidi.
Na biyu: A cikin fasali na hudu na wannan littafi mun bayani a kan ma'anar ibada bisa dalilai na hankali, ta yadda muka nuna cewa ba duk neman wani abu ko addu'a ko makamancinsa ba ne ibada. Abin da ake nufi da ibada shi ne wani nau'i ne na girmamata musamman wacce take tare da wata akida ta musamman, wato mutum ya dauki wanda yake kaskantar da kansa a gare shi a matsayin Allah, wa'iyazu billah, ko kuma mutum ya dauka cewa wani abin halitta ne yake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan Allah kamar yadda masu bautar gumaka suke dauka.
Amma girmamawa da kaskantar da kai wanda ya koru daga wannan akida marar tushe, ta yadda mutum yana ganin wanda yake girmamawa a matsayin wani bawan Allah ne, kuma wanda yake da kusanci zuwa ga Allah, sakamakon haka ne yake kamun kafa da shi yana neman addu'arsa, sam ba a kiran wannan bauta, ballantana ya zama shirka da Allah.
Tambaya ta biyu: Shin neman addu'a daga mamaci ba shi da wani amfani?
Daya daga cikin abin da masu inkarin wannan al'amari suke kawowa shi ne, mutumin da ya mutu sam ba shi da ikon da zai iya biya wa mutum bukatarsa. Saboda haka neman wani abu daga wanda ya mutu sam wani abu ne marar amfani.
Amsa: Tushen wannan tamabaya yana komawa ga yadda mutum yake ganin duniya, wato kamar cewa wannan duniyar da muke gani ita kawai ce duniya bayan wannan babu wani abu, wdan da suke kuma ganin cewa mutum da zarar ya mutu shi kenan babu sauran wata rayuwa, don haka wadanda suka gabata sama ba su da wata rayuwa, don haka neman wani abu daga gare su wani abu ne marar amfani.
Amma tare da kula da ka'idojin da muka ambata a sama, amsar wannan tambaya a fili yake, haka ne mutum da ya mutu ba shi da rayuwa irinta duniya, amma yana da wata rayuwar ta lahira, sannan tare da izinin Ubangiji yana iya amsa na bukatocinmu.
Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu?
Wadanda suke da wannan tunani suna ganin tsakaninmu da wadanda suka rasu akwai wani abu wanda ya kare tsakanimmu, wanda Kur'ani yake ambata da barzahu. "A bayansu a kwai barzahu, har zuwa ranar tashin kiyama". Don haka kirammu ba zai isa zuwa gare su ba.
Amsa: Barzakh a harshen larabci ba tana nufin shamaki ko hijabi ba, wato ana nufin shamaki wanda yake hana su dawowa zuwa rayuwar wannan duniya, ba wai abin da zai hana su alaka da wadanda suke a raye ba. tare da kula da ayar da take da alaka da barzahu muna iya fahimtar wannan al'amari kamar yadda Kur'ani yake cewa:
"Zuwa lokacin da mutuwa zata zo wa daya daga cikinsu, zai ce: Ubangiji ka mai da ni zuwa duniya, domin kuwa zanyi aiki mai kyau a cikin abin ya ragu gare ni, sam ba haka ba ne kawai magana ce wacce mai yin ta yake fada".
Tare da kula da abin da mamaci yake fada shi ne Kur'ani yake ba shi amsa da cewa: "A bayansu akwai abin da ya kare su ta yadda ba zasu koma ba har zuwa ranar kiyama". Saboda haka wannan shamaki na hana dawowa a duniya ne, ba wanda zai hana wadanda suka rasu ba su yi alaka da wadanda suke a raye.
Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu?
Kur'ani yana kamanta yadda mushirikai suke da matattu, manufarsa kuwa da wannan shi ne, kamar yadda matacce ba ya jin magana, masu shirka suma haka suke, a kan haka ne yake cewa: "Lallai kai ba ka iya jiyar da matattu" "sannan ba ka iya jiyar da wadanda suke cikin kabari" Dangane da kamanta mushirikai da matattu dangane da rashin jin magana, muna iya cewa wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa cewa an kamanta mushirikai da matattu.
Amsa: Babu shakka a cikin kowace kamantawa ko misaltawa a kwai wata fuska da abu guda biyu a kan kamanta su, misali lokacin da za a ce Ali kamar zaki yake, tabbas a nan an dauki fuskar jarunta ne aka siffanta Ali da zaki domin kuwa duka guda biyun suna da wannan siffa. Saboda haka a nan zamu ga menene fuskar da ta sanya a kamanta matacce da mushiriki?
Tabbas babu yadda za a ce ta fuskar cewa sam ba su ji ko kadan, domin kuwa idan muka dauki hakan cewa mamaci ba ya ji, to shi ma mushiriki zai rasa wannan halitta ta ji ke nan, ga shi kuwa mushiriki yana jin maganar Manzo da ma ta sauran al'umma.
Saboda haka wannan kama da ta sanya aka kamanta su da wani abu daban, wannan kuwa shi ne rashin sauraren magana mai amfani. Wato kamar yada kiran wanda ya mutu zuwa ga aiki mai kyau ba shi da amfani, domin kuwa lokacin aikin ya riga ya gabata, haka nan kiran mushrikai zuwa ga aiki mai kyau ba shi da wani amfani, domin kuwa sam ba su da niyyar amsa wannan kira, tare da lura da ayoyin da suke magana a kan rayuwar barzahu zamu iya fahimtar wannan hakika.
Saboda haka magana guda a nan ita ce, kiran mushrikai zuwa ga imani kamar kiran wadanda suka mutu ne zuwa ga aiki mai kyau. Don haka kiran wadannan gungu guda biyu (Mushrikai da matattu) sam ba zai samu wata riba ba. Mushiriki yana ji amma ba shi niyyar karbar gaskiya, mamaci shi ma yana ji amma lokacin aiki ya riga ya wuce yanzu lokacin sakayya ne ga abin da mutum ya aikata ne.
Abin burgewa a nan shi ne almajirin Ibn Taimiyya wato Ibn Jauziyya, shi ma a cikin littafinsa (Arruh) ya fassara wannan aya da ake tambaya a kanta kamar yadda muka fassara. Yarda da wannan tafsiri da Ibn jauziyya ya yi, yana nuna kaucewa daga ra'ayin malaminsa Ibn Taimiyya a kan wannan magana.
7-Kamun kafa Da Mutane Tsarkaka Da Mutane Masu Daraja
Bahsin da ya gabata an yi magana ne dangane da kamun kafa da addu'ar mutane masu tsarki da daraja, wato wanda yake da wata bukata yana neman su yi masa addu'a domin Allah ya biya masa bukatarsa, wato addu'arsu zata sanya ya samu kusanci.
Amma abin da muke magana a kansa a cikin wannan Bahasi shi ne yin kamun kafa da su kansu don samun kusanci zuwa ga Allah madaukaki. Wato mai neman biyan bukata ba tare da ya nemi addu'arsu ba domin ya samu biyan bukatarsa, sai ya yi kamun kafa da su domin kasantuwarsu suna da matsayi a wajen Allah, sakamakon haka sai ya nemi abin da yake bukata a wurin Allah madaukaki, ta hanyar wannan matsayi da daukaka da suke da su a wajen Allah, sai Allah ya biya masa bukatarsa. Wannan nau'in kamun kafa kuwa ana yin sa ta hanyoyi daban-daban kamar haka:
Ya Allah don matsayin da suke da shi a wurinka!
Ya Allah don kusancin da Masoyanka waliyyanka suke da shi a wurinka!
Ya Allah albarkacin manzonka da iyalansa tsarkaka!
A cikin dukkan wadannan jumloli shi kan shi mutum wanda yake da matsayi a wurin Allah da siffofinsa masu kyawu su ne zasu sanya a biya wa mutum bukatarsa, bayan shaharar wannan nau'i na kamun kafa, akwai ruwaya ingantacciya da ta zo a kan haka wacce ake kira da "dharir"harda kuwa wadanda suke da sabani a kan wannan al'amari sun tafi a kan ingancin wannan ruwaya. Domin kuwa mun kawo yadda aka kafa hujja da wannan hadisi zamu kawo wannan hadisi a nan kamar haka:
Usman Bn Hanif yana cewa: Wani mutum makaho ya zo wajen Manzo (s.a.w) ya ce ya manzon Allah ka yi mini addua'a Allah ya ba ni waraka. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Idan kana so zan yi maka addu'a idan kuma zaka yi hakuri shi ne abin da ya fi.
Sai wannan makaho ya ce ka kira Allah ka yi mini addu'a! A wannan lokaci sai Manzo ya ce: ka je ka yi alwala mai kyau, sannan ka yi salla raka biyu ga wata addu'a nan ka karanta.
Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da manzonka Muhammad wanda yake annabin rahama ne ina kamunka kafa da shi a wurinka! Ya manzon Allah ina Kamun kafa da kai a wajen Allah domin ya biya mini bukatata. Sai Manzo ya ce: Ya Ubangiji ka biya masa bukatarsa domin ni.
Ibn Hanif yana cewa: Mun kasance a wajen Manzo ba tare da tsawon lokaci ba sai wannan mutum ya shigo a wajenmu kamar bai taba samun matsalar ido ba. Kafa hujja da wannan hadisi kuwa ya samo asali ne ta hanyar kasantuwar ingancin dangane da kuma ma'anarsa wacce take a fili.
Amma ta bangaren dangane da wannan hadisi kuwa Tirmizi yana cewa: wannan hadisi ne mai kyau kuma ingantacce. Ibn maja shi ma wanda ya ruwaito wannan hadisi yana cewa: wannan hadisi ne ingantacce. Sannan cikin sa'a shi ma Ibn Taimiyya ya tafi a kan ingancin wannan hadisi. Rufa'i wanda yake daya daga cikin marubutan wahabiyawa kuma na wannan zamani yana cewa: Babu shakka a kan kasantuwar ingancin wannan hadisi kuma mashahuri ne.
Saboda haka dangane da sanad ko danganen wannan hadisi babu sauran wani kace-nace. Saboda haka a nan abin da ya yi saura shi ne muyi bincike dangane da ma'anarsa a kan halascin wannan nau'i na kamun kafa.
Domin kuwa bayyana wannan ma'ana zamu tunatar da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Menene makaho ya nema a wajen Manzo?
2-Domin ya samu biyan bukata wane irin Tawassuli ko kamun kafa da Manzo ya koyar da shi? !
Cakuda wadannan abubuwa guda biyu zai sanya a kasa gane gaskiyar al'amarin, babu shakka wannan makaho ya roki addu'a daga Manzo, wato ya yi kamun kafa da addu'ar Manzo, a nan babu sabani a kan hakan.
Magana kuwa tana nan a cikin abin da Manzo ya koyar da wannan makaho, a cikin wannan addu'a da Manzo ya koyar da shi ya nuna masa ne ta yadda zai yi kamun kafa da shi kansa manzon, wato ya sanya Manzo tsakiya a tsakaninsa da Ubangiji, ta yadda sakamakon haka Allah ya biya masa bukatunsa. Sheda kuwa a kan hakan shi ne jumlolin da suka zo a cikin hadisin wadanda suke nuni da hakan. su ne kuwa kamar haka:
1- "Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da annabinka" wato ina rokonka da annabinka kuma ina fuskantarka da annabinka. Wace jumla ce ta fi wannan bayyana a kan cewa mai addu'a yana hada Allah ne da manzonsa wajen neman biyan bukatarsa.
A nan yana nuna ya yi kamun kafa ne da shi kansa manzon sakamakon girmansa a wajen Allah yake neman biyan bukatunsa.
2-jumlar "Muhammad annabin rahama"
Wannan jumla tana nunawa a fili cewa Manzo wanda yake rahamar Ubangiji ce a bayyane, shi ya sanya yake kamun kafa da wannan rahama da Ubangiji zuwa ga Allah.
Abin mamaki a nan shi ne irin wannan al'amari ya sake faruwa a zamanin Usman. Sannan matsalar mutumin da yake neman biyan bukata a wannan lokaci ta warware ne ta hanyar wannan addu'a, amma akwai bambanci kadan cewa wanda ya koyar da wannan addu'a a lokaci na farko shi ne Manzo da kansa, amma alokacin na biyu Usman Bn Hanif ne, a nan zamu kawo cikakken abin da ya faru daga mu'ujamul kabir na Dabarani kamar haka:
Wani mutum a zamanin hukumar Usman ya je wajen Usman domin wata bukata tasa amma bai samu biyan bukata ba, wata rana wannan mutum sai ya hadu da Usman Bn Hanif kuma ya gaya masa abin da yake damunsa, sai ya ce masa: ka je ka yi alwala ka yi salla raka biyu, sannan ka ce:
"Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzommu Muhammad annabin rahama, ya Muhammad ina kamun kafa da kai zuwa wajen ubangijinka don a biya mini bukatata".
Sai ya aikata wannan aiki, sannan ya tafi wajen Khalifa sai kuwa ya biya masa bukatarsa, sai ya sake haduwa da Usman Bn Hanif, ya tambaye shi danganen wannan addu'a, sai ya ce masa wata rana mun kasance a wajen Manzo (s.a.w) sai wani mutum mai ciwon ido ya zo wajen Manzo ya nemi ya yi masa addu'a, sai Manzo ya koyar da shi abin da na koyar da kai.
3-Jumlar "Ya Muhammad ina fuskantar Ubangiji da kai".
Wannan lafazi na "da kai"yan nuna kamun kafa ne da shi kansa Manzo din, saboda haka duk da cewa ya roki Manzo addu'a, amma ba shi ne matsayin shedarmu ba a nan. Amma a cikin abin da Manzo ya koyar da shi akwai shi kansa Manzo wanda yake rahamar Allah ne a cikin halitta, kuma shi ne silar biyan bukatar wannan makaho. Sannan jumlar "Ka ba shi lafiya don girmana" ita ma tana nuni ne ga sakamakon girman za a wajen Allah, zai samu biyan bukatarsa.
Wata kila a fahimci cewa wannan jumla ta sama tana nufin cewa; Ya Allah! Ka karbi addu'arsa da na yi masa, amma zahirin wannan hadisi ba ya nuna cewa Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a, domin kuwa ya koyar da shi ne addu'ar kamar yadda muka yi bayani a sama. Ballantana Manzo ya bukaci Allah ya amsa addua'r da ya yi masa don girmansa a wajen Allh. Idan kuwa da Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a bayan addu'ar da ya kowar da shi, to tabbas da wannan babban sahabi ya ruwaito wannan addu'a ta Manzo.
Bayan wannan ma idan mun dauka cewa bayan addu'ar da Manzo ya koyar da wannan makaho shi ma ya yi wa makahon addu'a, a nan ba zai cutar da kafa hujjar da muka yi ba da wannan hadisi, domin kuwa ba muna magana ne ba a kan addu'ar da Manzo ya yi masa. Domin kuwa muna kafa hujja ne a kan addu'ar da Manzo ya koyar da makaho ta yadda ya koyar da shi yadda zai yi kamun kafa da shi kansa Manzo sakamakon matsayi da daukaka da yake da shi a wajen Allah.
Idan da zaka bai wa wani masanin harshe wannan hadisi wanda ba shi da wata masaniya a kan haka, babu abin da zai fahimta bayan kamun kafa da Manzo (s.a.w) a wajen Allah madaukaki.
Ibn Taimiyya da mabiyansa lokacin da suka fuskanci wannan hadisi sun yi kokari su kawo matsala dangane da ma'anar wannan hadisi dangane da jumlolin da suke nuni a kan kamun kafa da Manzo a fili, sai su ce yana nufin addu'a ne, suna cewa:
Jumlar da take cewa: "Ina fuskantarka da manzonka" sai su ce wai ina fuskantarka da addu'ar manzonka.
A wannan akwai wani abin da ba a fada ba wannan kuwa shi ne sun yi hukunci ne sakamakon akidar da suke da ita tun da farko na haramcin kamun kafa da waliyyan Allah, amma wannan tawili nasu sam bai dace ba da jumlolin da muka ambata dangane da hakan.
Idan kuwa gaskiya ne makaho ya yi kamun kafa ne da addu'ar Manzo, to me ya sa Manzo ya ce masa ka ce: "Muhammad annabin rahama" sannan ya ce masa ka ce: "Ya Muhammad lallai ina fuskantarka"
Bayan wannan idan muka dauka ma'anar wannan yana nufin addu'a ne, to wannan zai bata tsarin jumlar.
Alusi Bagdadi (ya rasu 1270) wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yada wahabiyanci a nan yana mika wuya zuwa ga gaskiya, inda ya tafi a kan cewa kamun kafa da waliyyan Allah Manzo ne ko waninsa ba shi da wani laifi, da sharadin cewa mu dauka wannan mutumin yana da matsayi ne a wajen Allah .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012