Muassasar alhasanain (a.s)

Yin Ceto2

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Yin Ceto2

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Neman Ceto Daga Masu Ceto Na Gaskiya

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Neman ceto daga masu ceto na gaskiya wani abu ne wanda ya shahara tsakanin al'ummar musulmi tun daga zamanin Manzo har zuwa zamanin da muke a cikinsa, sannan babu wani daga cikin malaman musulunci da ya yi inkarin neman ceto daga masu ceto na gaskiya. Sai kawai mutum biyu su ne kamar haka:
1-Ibn Taimiyya a farkon karni na takwas.
2-Muhammad Bn Abdul wahab a cikin karni na sha biyu.
Dukkan wadannan mutane guda biyu sun hana neman ceto daga masu ceto na gaskiya inda suke cewa: Annabawa da waliyyai da mala'iku suna da hakkin yin ceto a ranar tashin kiyama, amma dole ne a nemi wannan ceto ga wanda yake shi ne mamallakin ceto wato Allah (s.w.t) ga abin da Ibn Taimiyya yake cewa: Ya Ubangiji, ka sanya mana annabi da sauran bayinka na gari masu ceto a gare mu ranar kiyama, don haka ba mu da damar mu ce ya Manzo ka cece mu! Kafin mu kawo dalilan da suke kawowa wajen hani a kan neman ceto, zamu fara kawo dalilan da suke halasta hakan daga Kur'ani da Sunna:
1-Neman Ceto Neman Addu'a Ne
Neman ceto daga Manzo ko wani daya daga cikin manyan bayin Allah ba wani abu ne wanda ya wuce addu'a da neman gafara ba daga Allah madaukaki, sakamakon matsayin da suke da shi a wajen Allah zai sanya addu'arsu ta samu karbuwa a wajen Allah madaukaki, ta yadda mai zunubi zai samu gafarar Allah sakamakon haka. Don haka neman addu'a koda kuwa daga dan'uwa mumini ne ai ba shi da matsala ina ga ace neman addu'a daga manzon Allah. (s.a.w) Idan muna cewa: "Ya kai mai matsayi a wajen Allah, ka cece mu a wajen Allah" (wato ka nema mana Allah ya yafe mana zunubbammu).
Lafazin shafa'a saudayawa ya zo a cikin hadisi da ma'anar addu'a mai yawa, haka nan marubucin Sahih Bukhari a cikin littafinsa ya kawo babi guda biyu, daya daga cikinsu yana magana ne a kan rokon musulmi daga shugaba, daya kuwa ya zo ne dangane da rokon mushrikai daga musulmi, ya yi amfani da lafazin "Shafa'a" a cikin wadannan babuka guda biyu. Wannan shi ne abin da ya kawo farkon duka babin guda biyu kamar haka:
A-Idan suka nemi "shafa'a" daga shugaba don ya rokar musu ruwan sama bai kamata ba ya ki karbar rokonsu".
B-Idan mushrikai suka nemi "shafa'a" daga muminai yayin fari.
A nan bayyane yake cewa kalmar "shafa'a" wacce take nufin ceto a nan tana bayar da ma'anar addu'a, haka hadisin da Ibn Abbas ya ruwaito daga Manzo (s.a.w) ga abin da yake cewa: "Duk lokacin da mutum ya mutu mutum arba'in daga cikin musulmai wadanda ba su shirka da Allah suka halarci jana'izarsa, sai Allah ya karbi "shafa'arsu'da suke yi masa" .
Shafa'ar wadannan mutane wadanda suka halarci jana'izarsa bai wuce addu'ar da suke yi masa ba yayin da suke masa salla suna cewa: Ya Allah ya gafarta masa!
Don haka idan har ma'anar shafa'a ko ceto shi ne yi wa mutum addu'a me zai sanya ya zama haramun.
2- Hadisin Anas Da Neman Ceto
Tirmizi wanda yake daya daga cikin marubutan sannan ya ruwaito hadisi daga Anass Bn Malik yana cewa: Na roki Manzo Allah cewa ya cece ni ranar kiyama, sai ya ce, zan yi hakan, sai na ce masa ina ne zan neme ka? Sai ya ce: ka neme ni a kan siradi.
Anass sakamakon yakininsa da matsayin Manzo ya nemi ceto daga gare shi Manzo kuma ya yi masa alkawari, sam bai zo ba ga tunanin Anass cewa wai neman ceto wani abu ne wanda yake shirka.
3-Sawad Bn Azib da neman ceto
Sawad ya kasance daya daga cikin sahabban Manzo kuma ya yi wa Manzo waka yana neman ceto daga gare shi ga abin da yake cewa: Ya manzon Allah ka kasance mai cetona ranar kiyama, ranar da ceton wasu ba ya da dai-da- da fatan dabino ba ya amfanar da Sawad.
4-Imam Ali (a.s) da neman ceto daga Manzon Allah (s.a.w)
Lokacin da Imam Ali ya gama yi wa Manzo wanka, sai ya bude fuskarsa ya ce masa: "Uwa da ubana fansa gareka, Ka kasance a raye ko ba a raye ba ka tuna mu a wajen ubangijnka".
Larabawa sukan yi amfani da wannan jumlar "ka tuna ni a wajen ubangijinka" da ma'anar ceto, kamar yadda annabi Yusuf yake cewa wanda suka zauna kurkuku tare yayin da aka fito da shi daga kurkuku, yake ce masa "ka tuna da ni wajen ubangijinka" .
Daga karshe zamu yi tunatarwa a kan cewa ayoyi da hadisan da suka zo dangane da kamun kafa da annabawa, dukkansu suna bayar da ma'anar ceto ne, don haka babu bukatar maimaita su a nan.

Dalilan Masu Haramta Neman Ceto
Masu haramta neman ceto suna kafa hujja da wasu dalilai wadanda zamu kawo wa masu karatu kamar haka:
1-Neman ceto shirka ne
Suna cewa: Dole ne muce ya Allah ka sanya mu cikin wadanda zasu samu ceton Muhammad (s.a.w).
Saboda haka sam ba mu da hakkin da zamu ce: Ya Muhammad ka cece mua wajen Allah. Tabbas Allah ya bai wa Manzo damar yin ceto, amma ba mu da ikon da zamu ce ya Allah ka cece mu, don haka dole ne mu nemi ceto a wajen Allah wanda ya ba shi damar ceto.
Amsa: Ayoyin Kur'ani sun yi bayani a kan cewa masu bayar da sheda da gaskiya zasu yi ceto a ranar kiyama, wato zasu kasance masu ceto a ranar kiyama (amma tare da izinin Allah) a inda yake cewa;
"Wadanda suke kiran wanin Allah sam ba zasu samu ceto ba, sai kawai wadanda suka bayar da sheda da gaskiya suna sane"
Kalmar "Illa" da ta zo a cikin wannan aya tana kebance kawai wadanda suka mallaki yin ceto.
Abin da kuwa ake nufi da mallakar ceto kuwa shi ne wadanda suke da izinin yin hakan daga Allah madaukaki. Tambaya a nan shi ne tun da Allah madaukaki zai bayar da wannan izini ga wasu daga cikin bayinsa, menene matsala don mai laifi ko zunubi ya nemi wannan ceton daga wadanda aka ba dama.
Duk da yake neman ceto ba yana wajabta karba ba ne, amma wannan wanda yake da izinin yin ceto karkashin wasu sharudda zai cece wanda ya nemi ceton. ABin lura a nan shi ne maganar da shugaban wahabiyawa yake yi inda yake cewa: Allah ya bai wa waliyyansa damar ceto, amma ya hana mu da mu nemi ceton daga gare su.
Na farko; cikin wace aya ce Allah ya hane mu da mu nemi ceto daga masu ceto na gaskiya? Idan wannan hani saboda cewa neman ceto shirka ne, kamar yadda muka yi Bahasi a baya dangane da shirka, zamu iya fahimtar cewa sam wannan ba shirka ba ne, domin kuwa wanda yake neman ceto ba ya ganin wanda zai cece shi amatsayin Allah ko wani mai tafiyar da ayyukan Allah, kawai mutum yana ganinsa ne a matsayin wani bawan Allah mai matsayi a wajen Allah, domin kuwa yana ganin cewa duk wani abu yana gangarowa ne daga Allah, ballantana wannan ya zama shirka, domin kuwa ba bauta ba ne ga mai ceton.
Na biyu: Wannan magana ta shugaban wahabiyawa tana warware kanta, domin kuwa idan har Allah ya bai wa waliyyansa wannan hakki da dama na ceto me zai sanya kuwa ya hana su amfani da wannan damar da ya ba su, wato ya hana al'umma su nemi wannan ceton daga gare su.
2-Shirkar mushrikai da neman ceto daga gumaka
Dalilinsu na biyu a kan haramta neman ceto daga waliyyan Allah shi ne cewa: Dalilin da ya sanya mushirikai zamanin Manzo suka yi shirka, sun kasance suna neman ceto ne daga gumaka, ga abin da Kur'ani yake cewa dangane da hakan: "Sun kasance suna bautar abin da ba ya cutar da su kuma ba ya amfanar da su, kuma suna cewa wadannan su ne masu cetommu a wajen Allah" .
Saboda haka duk wani nau'i na neman ceto daga Manzo ko waliyyan Allah kamar neman ceton mushrikai ne da suke yi daga gumaka.
Amsar wannan kiyasi kuwa a fili yake domin:
Na farko: tsakanin wannan neman ceton guda biyu akwai bambanci a bayyane, mushrikai suna kiran gumaka a matsayin alloli, sannan kuma suna ganin su ne suka mallaki ceto da kansu.
Amma su kau musulmai masu kadaita Allah sun dauki annabawa a matsayin bayin Allah, kuma sun yi imani da cewa sunsamu wannan izinin ceton ne daga Allah madaukaki, kuma shi ne mamallakin wannan ceto na asali. Don haka ta yaya za a dauki wannan neman ceton guda a matsayin guda daya?
Na biyu, mushrikai suna bautar gumaka ne, bayan sun bauta musu suke neman ceto daga gare su, sannan wannan aya tana nuna wadannan abubuwa guda biyu ne, (wato bauta da neman ceto) aiki na farko kuwa inda ayar take cewa"suna bautar wanin Allah"aikin na biyu kuwa"Suna cewa wadannan su ne masu ceton a wajen Allah. Alhalin su kuwa musulmai suna bauta wa Allah shi kadai, bayan bautar Allah makadaici sai su nemi ceto daga waliyyansa.
Daga wannan ne zamu fahimci cewa, kwatanta wannan neman ceton guda biyu wani abu ne wanda sam ba shi da tushe.
3-Neman ceto daga mamaci wani abu ne wanda ba shi da wani amfani
Dalilinsu na karshe a kan hani da neman ceto, shi ne mutumin da ya mutu neman ceto daga gare shi ai wani abu ne marar fa'ida.
Amsar wanann kuwa tare da kula da bahsin da muka yi dangane da rayuwar barzahu ya wadatar mu fahimci rashin ingancinsa.
Domin kuwa yayin da ya kasance shahidi a tafarkin Allah yana raye a barzahu, annabin Allah shi ya fi cancanta ya kasance a raye, sakamkon cewa mun yi cikakken bayani dangane da wannan a cikin bahsimmu na rayuwar barzahu, don haka a nan ba zamu mai -mai ta ba.
Mu dauka cewa annabawan Allah matattu ne, ta yadda ba su jin maganarmu, a nan zai zamana neman ceton da muke yi a wajensu ba shi da amfani, ba wai ya haramta ba.
Wanda ya fada a cikin rijiya, idan ya nemi taimako daga masu wucewa, aikinsa ya dace da hankali, amma idan ya nemi tamako daga duwatsun da suke gefen rijiya, to lallai ya yi aikin banza marar amfani, amma bai aikata haram ba, kuma bai shigar da shirka ba a cikin bauta.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)