Muassasar alhasanain (a.s)

Karamar Waliyyai

1 Ra'ayoyi 01.0 / 5

Karamar Waliyyai

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Matsayi Da Karamomin Waliyyan Allah

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Samun Karfi Mai Wuce Misali
Babu shakka an halicci mutum ne tare da iko wanda yake mai iyaka, da wannan karfi na shi ne yake rayuwa a cikin wannan duniya kuma yake neman taimako daga sauran wasu abubuwan halitta domin ya tafiyar da rayuwarsa. Wannan shi ne iko da karfin da Allah ya bai wa kowane mutum.
A kan haka akwai wasu gungu daga cikin bayin Allah wadanda suke da wani karfi da iko wanda ya dara wa na sauran mutane, ta yadda suke iya aiwatar da wani aiki wanda sauran mutane ba su iya aikata shi.
Domin samun wannan karfi da iko wanda ya wuce na al'ada akwai hanyoyi guda biyu:
1-Ta Hanayar Tsananin Tarbiyya
Rashin kula da jin dadi na jiki yana sanya wa mutum ya samu wani karfi na musamman da bangaren ruhinsa. Wato kai ka ce akwai kishiyanta tsakanin jiki da ruhi. Domin kuwa duk lokacin da mutum ya bai wa jikinsa kula ta musamman ta yadda ya nutse a cikin jin dadi da sha'awar abin duniya, wannan kulawa da nutsewa cikin tarbiyar jiki yakan sanya mutum ya gafala da bangaren ruhinsa, ta yadda ba zai kula da abin da ya shafi tarbiyar ruhin ba. Haka nan duk lokacin da mutum ya kawar da kansa daga sha'awar abin duniya da jin dadi, sannan ya kula da abin da ya shafi a bangaren ruhinsa, sakamakon haka zai iya samun wani karfi da iko da bangaren ruhinsa, ta yadda zai kara karfin bisa ga wanda yake da shi na al'ada.
Masu tarbiyyar ruhi mai nauyi wacce ma ta saba wa ka'idojin addinin musulunci kuma musulunci yake ganinta a matsayin haram, sun kawar da kansu daga duk wani nau'i na kula da jiki. Wannan nau'in tarbiyya kasantuwarta mai tsananin wahala da azabtarwa ya sanya ba kowane mutum ne ba yake iya jure ma ta. Har suma wadanda suka bi wannan hanya ba kai tsaye suke shiga a ciki ba, sukan bi a hankali ne har su saba, ta yadda sakamakon bi daki-daki a hankali suna kara matsawa gaba.
Babbar manufarsu a kan wannan aiki kuwa shi ne ta yadda mutum zai samu damar da zai iya kaucewa duk wani soyace-soyacen abin duniya da tasirinsa a kansa, sakamakon rashin kula da abin duniya, zai samu karfin ruhi. Babu shakka wannan nau'i na tarbiyya ya sabawa halittar dan Adam da shari'ar musulunci. Domin kuwa wani nau'i ne na isar da cuta ga jiki da rayuwar dan Adam. Sannan kuma wani nau'i na koyi da abin kiristoci suke yi a kaurace wa dukkan rayuwa wacce shari'ar musulunci ta yi hani a kansa.
2-Ta Hanyar Ibada
Hanya ta biyu kuwa kuma ingantatta da ake bi domin samun wannan karfi da iko na musamman ta hanyar ruhi, ita ce bin hanya mikakka ta bin Allah da bautarsa. Ta yadda mutum zai sanya hukunce-hukuncen addinin musulunci shi ne ma'auni a wurinsa, wato mutum ya tarbiyyantar da ruhinsa ta hanyar bin abin da Allah madaukaki ya umurci bayinsa da su aikata. Domin ayyukan ibada na zahiri ba shi ne ba Allah yake bukata, idan har musulunci ya yi umarni da aikata su ba don komai ba sai domin fa'idar da suke da shi ga mutum. Wato saboda kusancin da take sanya wa tsakanin mutum da Ubangiji da kuma kamalar da yake samu ta hanyar hakan. Masu imani da farkon lokacin da suke aiwatar da ayyukansu na ibada, ba tare da zabinsu ba sun fara hawa hanyar samun kammala, sannan suna tanajin wani karfi na musamman ne ta hanyar ruhinsu. Babu shakka ta wannan hanyar kamar da mutane zasu samu ta bambanta da ta juna, haka nan matsayin da kowane zai samu ya bambanta da na wani, wannan kuwa yana faruwa ne domin yawan biyayya ga Allah da bautar da kowane mutum yake yi ba iri guda ba ne.
Manzo (s.a.w) a wani hadisi ya bayyana matsayi da martabar da wadanda suka hau hanyar Allah suke da shi, ga kuma abin da ya ruwaito daga Allah madaukaki: kamar haka: "Babu wani aiki da bawa zai kusance ni da shi kuma na fi soyuwa gare shi kamar ayyukan da na wajabta ga bawa, kuma bawa bai gushe yana kusantata da nafiloli ba sai na so shi, idan kuwa na so shi zan zama jinsa wanda yake ji da shi, in zama ganinsa wanda yake gani da shi, sannan in zama hannunsa wanda yake kai hari da shi, kuma in zama kafafunsa da yake tafiya da su, idan ya roke ni tabbas zan ba shi abin da yake bukata, idan kuma ya nemi tsarina zan rsare shi" .
Tare da kula da abin da wannan hadisi yake koyar da mu zamu gane irin matsayin da zamu iya samu sakamakon yin bautar da aka wajabta mana da sauran nafiloli, sannan kuma ta wannan hanyar ne mutum za samu wani karfi a musamman ta yadda zai iya jin wani sauti daga Allah wanda ba kowane yake iya jinsa ba, sannan zai rika ganin wasu abubuwa wadanda ba iya ganinsu da idanuwan da kowa yake da su. Sannan kuma sakamakon wadannan ayyuka da matsayi da ya samu a wajen Allah duk abin da yake za a biya masa bukatarsa. A cikin kalama guda daya zai zama masoyin Allah, sannan ayyukansa zasu zama ayyukan Allah.
Babu shakka abin da ake nufi da cewa Allah zai zama ji da ganin mutum shi ne, zai kasance idanuwansa sakamakon kudura da ikon Allah suna ganin da ba kowane yake yin irinsa ba, haka nan kunnuwansa suna ji fiye da na sauaran al'umma, sannan zai samu karfi mai yawa.
Manzo (s.a.w) dangane da cancantar dan Adam ya isa ya zama abin mamaki inda yake cewa, hanyar ibada ita ce hanya kawai ingantacciya kuma marar hadari da mutum zai iya bi domin ya samu gani da ji na musamman da sauran martabobi a wajen Allah (s.w.t).
A yanzu zamu yi nuni ne da wasu abubuwan mamaki dangane da sakamakon bin hanyar bautar Allah da bin hanyar Allah wacce take mikakka babu karkace. Ta hanyar kafa hujja musamman da ayoyin Kur'ani zamu tabbatar da yadda mutum zai iya samu iko a kan zuciyarsa da ruhinsa, har ma ya iya samun iko a kan duniyar halitta. Sakamakon biyayyarsa ga Allah (s.w.t), amma dukkan wannan yana samunsa ta hanyar izinin Ubangiji. Wadannan abubuwa kuwa da zamu yi nuni da su, su ne kamar haka:

1-Fin Karfin Zuciya
Abu na farko da mutum zai samu sakamakon ibadarsa zuwa ga Allah shi ne, fin karfin zuciyarsa a kan wasu abubuwa da suke aibu ne gare ta. Sakamakon haka ne "Nafsul insani" zata samu daukaka a kan "nafsul ammara" wacce take umurtar mutum da aikata abin da zai tauye shi daga zuwa samun kammala. Mutum ta hanyar ibada da kamalar da yake samu zai kai wani wuri da zai samu karfi a kan wannan "nafsul ammara" ta yadda wannan mutumin yake iya fin karfin abin da zuciyarsa take so na barna. Idan mutum ya kai wannan matsayi na kammala ana cewa ya samu wilaya a kan nafs dinsa, ga abin da wadannan ayoyi suke fada dangane da hakan:
1-"Lallai salla tana hani daga alfasha da abin ki" . Wato mutum sakamakon sallar da yake yi zata samar masa da wani yanayi wanda zai hana shi yin sabo da zunubi.

2-Gani Na Musamman
Yana daga cikin fa'idar ibada zata sanya mutum ya zama yana ganin wasu abubuwa na musamman ta yadda yana iya gane gaskiya da bata, saboda haka ba zai taba bace hanya ba. "Yaku wadanda kuka yi imani idan kuka ji tsoron Allah zai sanya muku rarrabewa", wato zai ba su wata baiwa wacce zasu iya gane gaskiya da karya .
Sannan a wata aya yana cewa: "Wadanda suka yi kokari a cikin bimmu zamu shiryar da su hanyoyinmu"
A cikin aya ta uku kuwa yana cewa: "Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah ku yi imani da manzonsa, zai ba ku nau'i biyu na daga rahamarsa, sannan ya sanya muku haske wanda zaku rika tafiya tare da shi" .
Abin da kuwa wannan ayar take karantarwa shi ne sakamakon imani da tsoron Allah suna sanyawa su rika jagorantar mutum a duk tsawon rayuwarsa a wannan duniya a kan hanyar da ta dace.
3-Kiyayewa Daga Tunane-tunane Marasa Amfani
Daya daga cikin abubuwan da mutum yake guri shi ne yayin dayake ibada ya zamana ya bar duk wani tunani sai na Allah madaukaki. Wadanda suke tunane-tunane yayin da suke yin ibada, wannan ya samu ne sakamakon kasantunwarsu sunacikin tunani marar kaidi na rayuwa, sakamakon hakane suka kasa mallakar tunaninsu yayin da suke bautar Ubangiji. Don haka ne suke gabatar da salla mai raka'a hudu cikin tunane-tunane mararsa iyaka, wato suna gabatar da wannan ibada ba tare da ruhi ba.
4-Fitar Ruhi Daga Jiki
A cikin wannan rayuwar jiki da ruhi kowane yana da bukatar juna, kamar yadda ya kasance ruhi yana so ya juya jiki, yana kokari ne ya kare jiki daga baci da lalacewa. Ta bangare guda ruhi yana bukatar jiki, ta hanyar wasu gabobi na jiki ne yake iya ji kuma yake gani. Amma wani lokaci ruhi sakamakon karfi da kamalar da yake samu, yana wadatuwa daga amfani da jiki, don haka yana iya fita daga jikin.
Dangane da sauran mutane wadanda suke kallon duniya a matsayin kawai wannan duniyar da muke iya gani ta dabi'a yana yi musu wahala su fahimci wannan al'amari. Amma dangane da wadanda suke bisa hanyar Allah suna ganin wannan wani abu ne mai sauki kuma duk lokacin da suke so ruhinsu ya rabu da jikinsu zasu yi hakan. A cikin rayuwa mun san wasu daga cikin mutane yin hakan wani abu ne wanda ya zame musu jiki sam bashi da wata wahala a gurinsu.
5-Ganin Jikunkuna Masu Taushi
Daya daga cikin alamun kusanci zuwa ga Allah shi ne ta yadda mutum zai rika ganin jikuna masu taushi, (ajsamul latifa) a cikin halittar da Allah ya yi akwai wasu halittu wadanda ba a iya ganinsu da idanuwa na zahiri, amma ta wata hanyar mutum yana iya ganin mala'iku suna cikin ta shi a sama. Kur'ani yana cewa:
"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasai, wanda kuma ya sanya mala'iku a matsayin ma'aika wadanda suke da fikafikai biyu, uku, ko hudu .
Don haka a nan zamu iya fahimtar cewa mala'iku jiki ne da su kuma suna da fika-fikai amma ga shi mu ba ma iya ganin wadannan jikuna. Amma bayin Allah na gari wadanda suka kusanci Allah ta hanyar tsarkin ruhi suna iya ganin mala'iku a matsayin jiki. Kamar yada ya zamana Sayyida maryam (a.s) ta ga jibril a cikin siffa ta musamman. kamar yadda Kur'ani yake cewa: "Jibril ya bayyanar mata a cikin siffa ta cikakken mutum".
Allah madaukaki ba kawai yana ganin mala'iku ba, har ma yana sauraren sautinsu. Imam Ali (a.s) yana bayyana rayuwarsa tare da Manzo a farkon manzanci, ga abin da yake cewa:
"Na kasance ina ganin hasken wahayi, sannan ina jin kanshin annabta, sannan na ji karar shaidan yayin da wahayi ya saukar wa Manzo. Sai na tambayi Manzo cewa: Wannan kara ta wacece? Sai ya amsa mini da cewa, wannan kara ta shaidan ce, ya yi wannan kara ne sakamakon yanke kauna da ya yi a kan cewa wani zai bauta masa. Ali! duk abin da nake gani kai ma kana ganinsa, sannan abin da nake ji kai ma kana jinsa! kawai sai dai kai ba Manzo ba ne, amma kai ne wazirina, kuma zaka kasance a cikin hanya mikakkiya" .
Karfin da zai sanya mutum ya iya ganin mala'iku yana kuma jin wata murya da ba a saba ji ba, wannan yana nuna karfin ruhin mutum ne, wanda yake samuwa ta hanyar bautar Allah. Manzo (s.a.w) Kur'ani ya bayar da shedar cewa, yana ganin mala'iku da jibril. Ganin Jibril yana bukatar karfin ruhi da kammala ta musamman, ta yadda zai ba mutum damar ya iya ganin wannan abin halitta.
A cikin matayen Bani Isra'il maryam ce kawai Allah ya bai wa wannan damar ta ganin mala'ika, lokacin da wannan mala'ika yake yi mata albishir da cewa ba tare da dadewa ba zata samu da, duk wannan ya faru ne sakamakon kamalar ruhi da maryam (a.s) ta kasance tana da shi.
6-Samun Ikon Yin Wani Abu A Cikin Duniya
Sakamakon bautar Allah ba kawai jiki ne zai kasance karkashin ikon mutum ba, duniya ma zata kasance tana bin umurninsa, ta yadda ta hanyar izinin Ubangiji sakamakon karfin ruhin da ya samu ta hanayar kusancinsa ga Allah, yana iya sarrafa duniya ba tare da yin amfani da wani abu da aka saba yin amfani da shi ba, ta yadda zai kasance ya mallaki mu'ujiza da karamomi.
A nan domin kafa hujja a kan bin da muke magana a kansa, ya kamata mu kawo wasu ayoyi da suke tabbatar da hakan cewa waliyyan Allah bisa wasu dalilai na musamman suna tare kuma da izinin Allah suna iya yin wani abu a cikin duniyar halitta ba tare da amfani da wani abu da aka saba amfani da shi wajen yin wannan abin.
Kur'ani wajen bayyanar da karfi da mu'ujizar da annabawa suke da ita wacce take da tushe daga kudrar Ubangiji marar iyaka, ya kawo kissoshi daban-daban, amma a nan zamu kawo wasu daga cikinsu kamar abin da ya shafi labarin annabi Yusuf, Sulaiman, Da Isa (a.s) zamu yi magana a kansu a takaice kamar haka:
A-Mu'ujizar Annabi Yusuf Da Warkar Da Babansa
Kur'ani yana cewa: Annabi Yusuf (a.s) ya aika wa babansa da riga ta hanyar wani wanda Kur'ani yake ambata da "Bashir" ya ce masa ka jefa wannan rigar bisa fuskar babana Yakub (a.s) zai samu ganinsa kamar yadda ya kasance a da, wannan dan aike bayan ya share hanyar da ke akwai tsakanin Misra dakan'an ya jefa wannan riga ga fuskar annabi Yakub sakamakon haka ne ya samu lafiya ya koma yana gani. Kur'ani mai girma yana bayyanar da wannan al'amari cikin ayoyi guda biyu kamar haka:
1-"Ku tafi wannan rigan tawa ku jefa ta a kan fuskar babana zai koma yana gani. "
2-Yayin da wannan dan aike ya zo sai ya jefa ta a bisa fuskarsa sai ya koma yana gani" .
A nan babu shakka a kan cewa wanda ya warkar da annabi Yakub shi ne Allah madaukin sarki, amma kamar yadda muka yi bayani a baya, baiwar Allah da ni'imarsa suna gangarowa ne ta hanyar wasu abubuwa, ta wannan hanya ne zata isa zuwa ga sauran halittu. A nan karfin ruhin Yusuf yana da tasiri wanda ya samu ta hanyar karfin ikon Ubangiji, ta yadda ya warkar da babansa. Amma me ya sanya Yusuf ya yi amfani da wannan hanya mai sauki, amsar wannan kuwa shi ne annabawa wajen yin mu'ujiza ko sauran waliyyan Allah wajen yin karama suna amfani da hanyoyi masu sauki ne kamar haka. ta yadda kowa zai iya gane yadda suke da alaka da duniyar gaibu. Domin idan suka yi amfani da abubuwa masu wahala, mutane zasu ce ai sun yi hakan ne sakamakon wani ilimi da suke da shi.
B- Karamar Mataimaka Annabi Sulaiman
Dukkammu muna da labarin kiran sarauniyar Saba da annabi sulaiman ya yi, amma kafin ta iso wajen Sulamin (a.s) sai Sulaiman ya ce wa wadanda suke tare da shi: Ya ku taron Mutane, wa zai iya zo mini da gadon Bulkisu kafin ita da mutanenta su zo mini suna masu mika wuya" .
"Ni zan zo maka da shi kafin ka ta shi daga nan, kuma ina da karfin aiwatar da wannan aiki kuma ni amintacce ne a kan hakan" .
Ana cikin haka sai wani daga cikin mutanensa wanda yake kuma dan 'yar uwar annabi Sulaiman ne kuma wazirinsa mai suna (Asif barkhaya) ya ce ni kafin ka rufe idonka ka bude zan zo maka da shi. Kamar yadda Allah yake cewa: "Wanda ilimin littafin yake wajensa ya ce: Zan zo maka da shi kafin ka bude idonka, lokacin da ya ganshi a tabbace a gabansa, sai ya ce wannan daga falalar ubangijina ne" .
A cikin fahimtar wannan aya dole ne mu kula da kyau cewa wane abu ne ya sanya wannan al'amari ya yiwu, ta yadda aka kawo wannan gadon mulki daga uwa duniya, a zahirin wannan aya ana fahimatar cewa wadannan mutane su ne suka kawo wannan gadon, amma wannan ya faru ne tare da izinin Allah (s.w.t) kuma muna iya fahimtar hakan tare da amfani da dalilan da zasu zo a nan kasa kamar haka:
Na farko: Annabi Sulaiman ya neme su da su gabatar da wannan aiki kuma yana ganin cewa suna iya yin hakan.
Na biyu: Mutumin da ya ce zai iya zuwa da wannan gado kafin Annabi Sulaiman ya mike tsaye, yana siffanta kansa kamar haka: "Ni a kan haka ina da iko kuma na amince da kaina".
Idan har niyya da karfin wannan mutum ba su da hannu a cikin yin wannan aiki babu ma'ana ya ce: "Ni ina iya aikata wannan aiki kuma na amince da kaina".
Na uku: Mutum Na biyu kuwa cewa ya yi: Ni zan zo maka da shi kafin ka bude idonka, kuma wannan aiki da ya sabawa al'ada ya jingina shi zuwa ga kansa; "Zan zo maka da shi".
Idan a nan Kur'ani yana so ya bayyanar da hakikanin wannan al'amari cewa: Ruhin waliyyan Allah da na sauran manyan bayin Allah yana da tasiri wajen aiwatar da mu'ujiza ko karama, ta wace hanya ce zai bayyanar da haka wanda ya fi wannna bayyana, ta yadda masu shakku na wannan zamani kada su yi tawili ko suki yarda da hakan.
Na hudu: Karfin ikon mutum na biyu kuwa wannan aiki babban abin mamaki ne domin kuwa Allah yana bayyanar da cewa sakamakon iliminsa ne da littafi. Ilimin da ya fita daga ikon sauran mutane, wannan ilimi ya kebanci wasu daga cikin manyan bayin Allah. Sannan ana samun irin wannan ilimi ta hanyar kusanci wasu bayin Allah da shi ubangijin, a kan haka ne yake cewa: "Sai wanda yake da ilimi daga littafi ya ce".

C- Ubangiji Dangane Da Annabi Sulaiman A Fili Yana Cewa:
"Duk ta bangaren da yake so haka iskan yake kadawa. Duk da cewa iska yana karkashin tsarin halitta ne amma yakan canza hanya kamar yadda annabi Sulaiman yake so: "Sulaiman yana da iska mai kadawa, wacce take tafiya da umurninsa zuwa kasar da muka yi albarka gareta, kuma mun kasance muna da masaniya a kan komai" . Abin lura a nan shi ne, a fili ayoyin da muka ambata a sama suna bayyanar da cewa wannan iska yana tafiya ne da umurnin Sulaiman.
A wata aya kuwa ana bayyanar da cewa wannan iska wanda Sulaiman yake amfani da shi a matsayin na'urata yadda daga safiya zuwa Zuhr yana tafiyar da sai an dauki tsawon wata guda za a yi ta, sannan daga Zuhr zuwa dare zai iya yin wata tafiyar wata guda ta hanyar sika, wanda a wannan lokacin abubuwan da ake amfani da su wajen tafiye-tafiye, sai an yi wata biyu ana tafiya sannan a yi tafiyar da zai yi a cikin yini guda daya tal.
Lallai Allah ne ya hore masa wannan iska wanda yake iya yin wadannan tafiye-tafiye da shi ya kuma sarrafa shi yadda yake so. Amma jumlar da take cewa: "yana tafiya da umurninsa" wannan a fili yana bayyana cewa Sulaiman yana da tasiri wajen tafiyar da wannan halitta da yin amfani da ita ta yadda ya so, ta yadda yake tafiyar da iska zuwa wajen da ya so, sannan ya tsayar da shi idan ya so hakan.
D-Mu'ujizar Annabin Allah Isa (a.s)
Kur'ani mai girma ya jingina wasu ayyukan da suka sabawa al'ada zuwa annabi Isa (a.s) dukkan wadannan ayyuka suna faruwa daga karfinsa na badini ta hanyar ruhinsa, kamar yadda yake cewa: "Lallai ina halitta muku wani abu mai kama da tsuntsu daga yumbu, sai in hura a cikinsa, sai ya zama tsuntsu da izinin Allah, Sannan ina warkar da mai kuturta da makaho wanda aka haifa da makanta, kuma in rayar da matattu duk da izinin Allah".
A cikin wannan aya Annabi Isa (a.s) yana jingina wadannan ayyuka zuwa gare shi kamar haka:
1-Halitta tsuntsun daga yumbu.
2-Hura rai ga tsunsu da rayar da shi.
3-Warkar da makahon da aka haifa da makanta.
4-Warkar da kuturta.
5-Rayar da matattu.
Annanbi Isa duk yana jingina wadannan ayuka zuwa gare shi, ba wai yana rikon ba ne daga Allah da gudanar da hakan. Domin kuwa yana cewa: "Ina yin wadannan abubuwa ne da izinin Allah"amma a nan menene hakikanin izinin Ubangiji? Shin wannan izini ta hanyar lafazi ne? Tabbas ba haka ba ne, wannan izini na boye ne. Wato ta yadda Allah madaukaki yake bai wa bawansa wannan karfi ta yadda zai iya gabatar da wadannan ayyuka.
Sheda kuwa a kan ingancin wanann tafsiri shi ne, bawa ba wai kawai a cikin abubuwa da suka saba wa al'ada yake mabukaci ba, har a cikin abubuwan da suke na al'ada mabukaci ne, domin kuwa babu wani aiki da zai yiwu ba tare da izinin Allah ba, iznin Allah kuwa a cikin komai shi ne, ya bai wa mutum karfi da rahamar da zai iya gabatar da wannan aikin. Don haka ne a cikin wannan aya da muka ambata annabi Isa yake jingina wadannan ayyuka zuwa gare shi. Sannan a wata ayar ma Allah da kansa a fili yake jingina wadannan ayyuka zuwa ga annabi Masih (a.s) wannan kuwa yana tabbatar da wannan al'amari kamar haka:
"Kuma yayin da kake halitta daga yumbu kamar siffar tsuntsu da izinina, sannan ka hura masa rai sai ya zama tsuntsu duk da izinina, sannan kana warkar da makaho da mai ciwon kuturta da izinina, sannan ka rayar da matattu da izinina" .
A cikin wadannan ayoyi dole mu kula da kyau, wane ne mai aiwatar da wannan aiki, domin kuwa ba yana cewa: Ni ne na halicci wannan kaza ba, ko ni ne na warkar da wannan makaho, ko ni ne na tayar da wannan matacce. Yana cewa ne: "Yayin da kake halitta, ko "Kake warkar" Ko "Yayin da kake rayar da". Wane bayani ne ya fi wannan bayyana?
Amma domin ya bayyana cewa babu wani mutum wanda yake iya yin haka ba tare da izinin Allah ba, domin Kur'ani ya nisantar da tunani na shirka ko hada Allah da wani, kuma ya tabbatar da cewa mutum wajen yin halitta yana da bukatuwa zuwa ga Allah, ba wai shi da kansa ba tare da amincewar Allah yake yin ayyukansa ba, Sai ya zamana a cikin dukkan wadannan ayyuka na annabi Isa aka bayyanar da abin cewa duk yana faruwa ne da izinin Allah, wato a cikin kowane abu an kiyaye kadaita Allah a cikin ayyuka wanda yake daya daga cikin matakai na kadaita Allah (s.w.t)
A nan zamu wadatu daga abin da muka yi bayani dangane da mu'ujiza da karamar annabawa da waliyyan Allah a kan cewa duk suna faruwa ne da izinin Allah (s.w.t). Sannan dangane da abubuwan da muka kawo kuwa suna matsayin misali ne daga mu'ujizoji da karamomin Waliyyan Allah wadanda suka zo daga Kur'ani da hadisan Manzo da Nahjul balaga.
Daga karshe zamu yi nuni ne da abin da wasu marubuta suka yi imani da shi cewa yarda da irin wadannan karamomin na waliyyai wani nau'i ne na shirka, amma wannan ya faru ne sakamakon gafalarsu a kan cewa mutum yana iya yin wani abu a cikin duniya ta hanya guda biyu:
1-Ya zamana mutum da kansa ne ya mallaki wannan ikon, wato ya zamana wannan karfin da iko daga gareshi ya samo asali.
2-Karfin da ikonsa ya zamana ya samo asali ne daga Allah madaukaki, Wato sakamakon wasu dalilai yake bai wa wasu daga cikin bayinsa ikon yin hakan.Babu shakka da ma'anar ta farko wani nau'i ne na shiraka da Allah kuma ba ya inganta. Kasantuwar mutum ya zamana yana da iko a kan yin wasu abubuwa wadanda suka sabawa al'ada kuma ya dauka cewa wannan ikon ya same shi daga kansa, to wannan shirka ce kuma hada Allah ne da wani kuma yana kore mutum daga musulunci. Amma fuska biyu kuwa, wannan yana nuna tsantsan kadaita Allah ne, domin kuwa ya samo asali ne daga kudrar Allah wanda yake shi kadai yake.
Idan muka lura kuwa dangane da matsayi da martabobin da Allah ya bai wa wasu daga cikin waliyyansa, bai kamata ba mu yi shakku dangane da abin da muka gani ko muka ji labari na daga karamomi da mu'ujizojinsu suna raye ko kuwa bayan ransu. Domin kuwa karamar Annabi Masih ba ta kebanta ba da rayuwar wannan duniya, domin kuwa ta samo asali ne daga kusanci da yake da shi na ruhi zuwa ga Allah madaukaki, wannan kuwa yananan kiyaye a kowane lokaci, wannan kuwa a wannan duniyar ne ko kuwa a rayuwar duniyar barzahu ce.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)