Muassasar alhasanain (a.s)

Neman Tabarruki

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Neman Tabarruki

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Neman Tabarruki Da Manzo Da Abin Da Ya Bari

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Kadaita Allah a cikin halitta yana daya daga cikin matakan tauhidi, abin da kuwa yake nufi shi ne a wannan duniya babu wani mai halitta in ba Allah ba wanda yake shi kadai yake. Sannan dukkan abin da yake a cikin duniya na halitta a wannan duniyar ne ko kuwa a wata duniyar da ba mu gani ne Allah ne ya halicce shi, Sannan duk wani abu na halitta ba shi da samuwa ko wata kammala daga kashin kansa, idan har yana da wata kammala a zahiri to ya same ta ne daga Allah madaukaki. Dangane da wannan asali kuwa Mumini da mushiriki duk daya suke, domin kuwa a tambayoyin da Kur'ani yake kaddarawa, cewa, da za a tambayi dukkan wadannan gungu guda biyu, wato masu kadaita Allah da mushrukai a kan cewa wane ne wanda yake yin halitta, a nan amsar duka guda biyu daya take shi ne Allah ne. Ga abin da kur'anin yake cewa dangane da haka: "Da zaka tambaye su wane ne ya halicci sammai da kassai sannan ya hore rana da wata, da zasu amsa da cewa lallai Allah ne" .
Gurin da aka samu sabani tsakanin masu imani da mushrikai a zamanin manzanci shi ne wajen kadaita Allah a wajen tafiyar da duniya da al'amurran dan Adam, yayin da masu imani suka tafi a kan cewa Allah ne kawai yake tafiyar da duniya da abin da yake a cikinta, amma mushrikai suka tafi a kan cewa: allolin karyarsu na gumaka suma suna da hannu wajen tafiyar da duniya.
Tare da yin imani dacewa mai tafiyar da duniya da duk abin da yake a cikinta shi ne kadai Allah madaukaki, amma a lokaci guda dole ne musan cewa ba yana kore kuma tasirin wasu abubuwa ba ne a cikin wadansu abubuwan halitta. Domin kuwa bisa ga dalilai daga Kur'ani da na ilimin kimiyya da na hankali mun ga cewa duniya an halicce ta bisa wani tsari na musamman ta yadda wasu daga cikin halittu suke da tasiri a cikin wadansu, kuma wadansu abubuwa su ne dalilin samuwar wasu, don haka wasu abubuwa wadanda zasu faru sakamakon faruwar wasu abubuwa ne kafinsu. Amma dukkan wannan abin da yake a cikin duniya da tasirin da yake a tsakanin halittu yana faruwa tare da kudra da yardar Allah madaukaki. Misali hasken rana da wata, kunar wuta, da rayuwar tsirrai ta hanayar ruwa, da komai da komai, yana faruwa ne karkashin ikon Ubangiji, idan da daidai da runtsewar ido Allah zai cire ikonsa babu wani abu da zai yi saura a duniya.
Domin Karin bayani muna tunatarwa a kan cewa, a cikin wannan duniya abu guda ne kawai wanda yake shi ne sanadi na hakika, wannan kuwa shi ne Allah madaukaki, amma duk da haka a cikin wannan duniya akwai wadansu halittu wadanda suke da tasiri a cikin wasu, kuma wasu su ne sanadin faruwar wasu, amma dukkkan wannan da karfin ikon Ubangiji ne, wanda yake shi kadai ne mahaliccin duniya kuma mai tafiyar da ita. Misali girman itaciya da rayuwar mutum duk suna bisa wasu sharudda ne na duniyar dabi'a, wanda idan babu wadannan abubuwa, wadanda suka hada da ruwa, iska da haske, rayuwar dan Adam zata shiga cikin hadari. A daidai wannan lokacin wanda babu wani mai yin wani abu sai Allah, su kuwa wadannan abubuwan baki daya suna matsayin masu tafiyar da umarnin Allah ne a cikin wannan duniyar ta halitta.
Kur'ani a cikin surar bakara aya ta 22 yana bayyanar da wannan tasiri wanda yake karkashin ikon Allah (s.w.t) (Ta bakin masu falsafa tasiri zilli) inda yake cewa: "Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya sanya muku sama a gine, kuma ya saukar muku ruwa daga sama, sannan ya fitar da tsirrai daga gare shi wadanda suke arziki ne gare ku". Wannan aya tana bayyanar da yadda tasirin da ruwa yake da shi wajen fitowar tsirrai da yadda itatuwa suke yin 'ya'ya sakamakon saukar ruwan sama.
Sannan kuma aikin ilimin kimiyya baki daya shi ne gano yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu ne, ta yadda ta wannan hanyar za a san yadda alakar da take tsakanin abubuwan halitta domin yin amfani da su kamar yadda ya dace.
Kuskuren wannan duniyar da muke ciki shi ne, ta yadda take bayyanar da fuskarta ta zahiri wanda sakamakon haka ne saia dauka cewa ai abubuwan da suke da tasiri ga sauran halittu kamar ma su ne sanadi na asali babu wani abu bayan hakan, alhali kuwa bayan wannan duniya akwai wanda shi ne mai tasiri na hakika kuma shi ne ma yake tafiyar da komai da komai, sannan tasirin sauran halittu abin da ya kama daga kasa har zuwa sauran taurari suna tafiya karkashin iko da nufinsa kuma kamar yadda ya tsara ne suke tafiya.

Allah Shi Yake Bayar Da Iko Ya Kuma Amshe Idan Ya So
Kamar yadda ya kasance Allah shi yake bai wa wasu daga cikin halittu ta yadda zasu iya yin tasiri a sauran halittu, haka nan idan ya ga dama yakan amshe wannan ikon ta yadda ba zasu iya yin tasirin ba a cikin wasu. Misali Allah yana bai wa wuta umarni da cewa kada ta kona Ibarahim (a.s) kamar yadda shi ne ya sanya wuta tana iya kone wani abu, haka nan kuma shi ne ya amshe wannan tasiri da take da shi kuna. Haka nan yake bai wa teku umarni da kada ta nutsar da annabi Musa da mutanensa, saboda da haka kamar yadda Allah yake bai wa wasu daga cikin bayi ikon yin wani abu haka nan idan ya so sai ya amshe wannan karfi da ikon da suke da shi.
Wata Fuskar Daban Da Allah Yake Bayyanar Da Ikonsa
Iko da kudirar Ubangiji ta ginu a kan cewa kowane abu zai faru ta hanyar wani na musamman, amma sakamakon wasu dalilai sai Allah madaukaki ya sanya wasu abubuwa su auku ba bisa yadda suka saba faruwa a al'ada ba. Wannan kuwa yakan faru ne yayin da annabawa suke so su tabbatarwa mutane cewa suna da alaka da Allah (s.w.t) Irin wannan aiki shi ne ake kira da "Mu'ujiza".
Mu'ujizar annabawa baki daya tana faruwa ne ta wannan hanyar, babu shakka kasantuwar sanda busasshiya ta koma macijiya, ko kuma janyewar ruwan kogi ta hanyar sandar Musa (a.s) ko kuma sanya makaho wanda ba ya gani ya koma yana gani, da warkar da sauran cututtuka masu wuyar magani, dukkan wadannan abubuwan suna faruwa ta hanyar da ba su saba faruwa ba (amma ana ba muna Bahasi ne a kan hakikanin mu'ujiza ba ne).
Da wannan ne zamu fahimci cewa, mafi yawa, baiwar Ubangiji tana isowa zuwa garemu ne ta hanyar da aka saba da ita, amma wani lokaci takan iso wajenmu ne ta wata hanyar daban wacce ba a saba da ita ba, wannan kuwa ita ake kira da mu'ujiza, wannan kuwa tana faruwa ne yayin da mutumin da ya zo da ita yana ikirarin annabta ne kuma ya zo da ita ne domin ya tabbatar da alakarsa da Ubangiji. Amma duk lokacin da irin wannan ya faru, amma wanda ya zo da shi bai yi da'awar annabta ba, ana ce ma shi da karama.
Karamomi Biyu Da Suka Bayyana Ga Maryam (a.s)
Kur'ani yana ambatar karamomi guda biyu da suka bayyana daga maryam su ne kamar haka:
1-Ta kasance tana ganin abinci a wurin da ta kasance tana bautar Ubangiji, sakamakon haka ne duk lokacin Zakariya (a.s) ya shigo wajenta sai ya tarar da abinci a wajenta, sai ya tambaye ta daga ina take samun wannan abincin, sai ta ce masa: "Wannan yana zuwa ne daga Allah, Lallai Allah yana azirta wanda ya so ba tare da hisabi ba".
2-Maryam yayin da zata haihu ta kama wata itaciyar dabino sakamakon ciwon nakudar haihuwa, sai kwatsam ta ji wata murya tana cewa: Ki kama wannan reshen busasshe na dabino ki girgiza shi domin 'ya'yan dabino su zubo miki".
A wadannan wurare guda biyu da muka ambata na karamomin sayyida maryam (a.s) na kawo mata abinci da ake yi da kuma yadda busasshyar itaciyar dabino ta yi 'ya'ya, duk suna nuna mana tsarkin ruhin Maryam ne, ta yadda wadannan abubuwa suka faru sabanin yadda suka saba faruwa saboda girmanta. Zuwa yanzu mun fahimci ma'anar mu'ujiza, a nan ya dace mu yi bayani a kan neman tabarruki.
Menene Neman Tabarruki
Tabarruki ya samo asali ne daga kalmar 'baraka' wacce take bayar da ma'anar Karin ni'ma, a nan kuwa abin da ake nufi da haka shi ne mutum mai imani kuma mai kadaita Allah yanemi wani abu ta hanyar wani abu wanda ya zo daga annabawa ko manyan bayin Allah. Wannan kuwa ba yana nufin cewa ba mutum ya kulle kofar faruwar abubuwa kamar yadda suka saba faruwa, a lokaci guda mutum yana bin hanyar da aka saba da ita kuma ya nemi kari ta hanyar neman tabarruki daga bayin Allah ta yadda kofofin ni'ima zasu bude a gare shi.
Babu shakka babu wata alaka ta duniya tsakanin abubuwan da suka ragu daga bayin Allah da abin da mutum yake samu na daga ni'immomi ta hayar wadannan abubuwan. Amma kamar yadda muka yi bayani cewa wani lokaci lokaci ni'imar Ubangiji takan kwararo wa dan Adam ta wata hanyar da ta saba wa wacce aka saba. Haka nufin Allah ya rigaya a kan cewa ta hanyar neman tabarruki da manyan bayin Allah da abubuwan da suka ba ri mutum yana iya samun abin da yake nema, wannan kuwa wta hakika ce wacce ayoyin Kur'ani suke tabbatar da ita. Sannan ruwayoyi mutawatirai sun zo a kan hakan, sana babu wani dalilin hankali wanda yake kin yiwuwar tasirin abubuwan da ake jingina su zuwa ga bayin Allah.
A nan zamu kawo wasu daga cikin ayoyin da suke bayani a kan haka:
1-Neman Tabarruki Da Matsayin Annabi Ibrahim (a.s)
Allah madaukkakin sarki ya sanya wani bangare na kasa ya zama wurin ibada sakamakon kasantuwar wasu bayin Allah masu kira zuwa ga tauhidi a wurin, kamar idan Allah yake ba da umarni da a tsayar da salla inda annabo Ibrahim ya kasance (Makamu Ibrahim). Inda Allah yake cewa: "Yayin da muka sanya Ka'aba wurin da mutane zasu rika taruwa kuma wuri na aminci, to ku riki wurin da Ibrahim ya tsaya wurin salla" .
Yin salla a wannan wurin kasantuwar ba shi da bambanci da sauran wuraren da suke a msallacin, ya samo asali ne daga tsayuwar da Ibrahim ya yi a wajen sakamakon haka ya samu albarka ta musamman, don haka ne masu salla suke so su yi salla a wajen, domin neman tabarruki. Haka nan zamu gani yadda Allah ya sanya tsakanin dutsen safa da marwa wurin ibada, wannan kuwa duk saboda al'barkacin kafafuwan wata baiwar Allah ta taka wajen har sau bakwai, don haka ne Allah yake ba da umarni cewa mahajjata su je su dawo a wannan wuri har sau bakwai, duk wannan ana yinsa ne don neman tabarruki da Hajara (a.s) kuma babu wani dalili wanda ya wuce wannan.
2-Rigar Annabi Yusuf Ta Warkar Da Annabi Yakub (a.s)
Annabi Yakub sakamakon rashin Yusuf ya yi kuka tsawon shekaru da shekaru, ta yadda har ya rasa ganinsa, yanzu Allah yana so ya mayar masa da idanunsa, Annabi Yakub (a.s) sakamakon aza rigar Yufus da aka yi a kan fuskarsa ya samu lafiya, kamar yadda Allah yake fada a cikin littafinsa mai tsarki; "Ku tafi da wannan rigar tawa ku jefa a kan fuskar babana ganinsa zai dawo".
Rigar annabi Yusuf ba ta kasance tana da saka ba ce ta musamman wacce ta fita sauran mutane, an yi wannan riga ne da audugar Misra kuma a nan a ka saka ta, amma Allah madaukaki ya so ya isar da ni'imarsa zuwa ga bawansa ta hanyar wannan riga. Sakamakon dora wannan riga a kan fuskar Yakub ya koma yana gani tangaram kamar yadda Allah yake cewa: "Yayin da dan aike ya zo sai ya jefa rigar a kan fuskarsa sai ganinsa ya dawo".
3-Akwatin Alkawari Ya Kasance Dalilin Natsuwa Da Cin Nasara
Annabi Musa (a.s) a karshen rayuwarsa ya kasance ya sanya allunan attaura wadanda aka saukar masa da kuma wasu abubuwa da ya gada masu muhimmanci a cikin wani akwati ya kuma mika shi zuwa ga wanda ya gaje shi wato Yusha'u Bn Nun, sakamakon haka ne Bani Isra'il sun kasance suna bai wa wannan akwati muhimmanci kwarai da gaske, don haka duk lokacin da zasu yi yaki tsakaninsu da wasu al'umma sukan tafi da wannan akwati tare da su, ta wannan hanyar ne suke cin nasara a kan makiyansu, zuwa lokacin da wannan akwati mai matsayi da abin da yake a cikinsa ya kasance a hannunsu sunkasance suna rayuwa madaukakiya, amma abin bakin ciki sakamakon raunin addinin da suka samu ta hanyar makiyansu wannan akwati mai dinbin daraja ya kau daga hannunsu.
Bayan wani lokaci sai Allah madaukaki ya zabi Dalut a matsayin kwamandan yaki ga Bani Isra'il, sannan annabinsu ya bayyana musu cewa alamar wannan kwamandanci da aka bai wa Dalut cewa daga Allah ne, akwatin nan wanda yake kuna natsuwa da shi. Idan kuka halarci wannan yaki za a mai do muku da shi. Ga abin da Allah yake cewa: Sai annabinsu ya ce musu lallai alamar mulkinsa shi ne za a zo muku da akwati wanda akwai natsuwa a cikinsa daga ubangijinku, sannan akwai sauran abin da iyalan Annabi Musa da Harun suka bari, mala'iku suna dauke da shi, a cikin wannan aya ce gareku idan har kun kasance masu imani".
A nan Allah madaukaki ta hanyar annabinsa yana ruwaito batun neman tabarrukin da Bani Isra'il suke da wannan akwati, abu mafi muhimmanci shi ne ta yadda mala'iku suke daukar wannan akwati, idan addinin Allah yana ganin yin haka wani aiki wanda ya saba wa kadaita Allah sam ba zai yiwu annabin Allah ya kawo shi ba a matsayin wani labari mai farantawa.
4-Neman Albarka Da Wurin Da As'habul Kahfi Suka Kasance
Muminai masu kadaita Allah bayan sun gano inda aka rufe As'habul kahfi, dukkansu sun hadu a kan cewa zasu gina masallaci ne a kan kabarinsu ta yadda ta hanyar ibada kusa da kaburburansu zasu nemi tabarruki. Ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka: "Sai wadanda suka ci nasara a kan saura suka ce, zamu gina masallaci a kan kabarinsu" . Masu tafsir suna cewa: Abin da ake nufi da gina masallaci a cikin wannan aya shi ne yin salla awurin da neman albarkaci daga jikunansu.
Dangane da neman tabarruki zamu wadatu da wannan ayoyin guda uku ne. Kula da ma'anar wadannan ayoyi zasu koyar dam u ne wani asali na ilimi daga Kur'ani ai girama, wannan kuwa shi ne nufin Allah madaukaki ya tafi a kan cewa zai kwararo da ni'imominsa na fili da na boye zuwa ga dan Adam ta hanyar wasu daga cikin bayinsa, a nan kuwa tsakanin abubuwan da suka shafi rayuwar duniya da wanda ba su ba babu bambanci, misali Allah madaukaki a kan abin da ya shafi shiryarwa yakan dauki wani abu wanda aka saba da shi ya yi amfani da shi, wato ta yadda yake zabar wani daga cikin bayinsa a matsayin Manzo ya aiko shi zuwa ga mutane domin ya shiryar da su.
Amma wani lokaci nufinsa yakan yi rigaye a kan ya tafiyar da ni'imominsa ta wata hanya wacce ba a saba da ita ba don ya isarda wannan ni'ima zuwa ga bayinsa. Neman tabarruki kuwa bai wuce wannan ba ta yadda mutum zai nemi wani abu daga ni'imar Ubangiji ta hanyar da ba ita ake bi ba wajen neman wannan abin a cikin rayuwar duniya.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)