Muassasar alhasanain (a.s)

Bukin Mauludi

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Bukin Mauludi

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Girmama Ranakun Haihuwar Waliyyan Allah

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Tarihi yana nuna cewa tun lokaci mai tsawo musulmai sun kasance duk shekara suna bukin ranar haihuwar Manzo (s.a.w) ta yadda suke ambatar kalmomin yabo ga Manzo a wurin wannan buki. Babu tabbas a kan wane lokaci ne a ka fara wannan buki, amma dai wannan bukin an dauki daruruwan shekaru ana yinsa kuma ya yadu a duk garuruwan musulmai.
Ahmad Bn Muhammad wanda aka fi sani da Kusdalani, (ya rasu a shekara ta 923) Dangane da bukukuwan da mashahuran malaman karni na tara suk kasance suna yi, yana ruwaito cewa: Musulmai sun kasance a kowane lokaci suna yi bukukuwan ranar haihuwar Manzo (s.a.w) suna ciyarwa a wannan rana, sannan suna raba sadaka a dararen wannan ranaku, suna bayyana farin cikinsu a wannan rana, sannan suna ninka kyautatawa a wannan rana, kuma suna yin wakokin yabon Manzo a wannan rana. Sannan albarkar Manzo tana bayyana a kowace shekara, rahamar Allah ta tabbata ga wadanda suka yi bukin daren ranar haihuwar Manzo (s.a.w) sannan ya kara ciwo ga zuciyar makiyansa masu cutar zuci.
Hasan Bn Muhammad Bn Hasan wanda aka fi sani da Dayyar Bukari (ya rasu shekara ta 960) kuma ya kasance daya daga cikin alkalan Makka, a cikin littafinsa na tarihi yana rubuta cewa: Musulmai sun kasance a kowane lokaci suna bukin ranar haihuwar Manzo, suna ciyarwa a wannan rana kuma suna bayar da sadaka a dararen wannan rana, kuma suna bayyanar da farin cikinsu a wannan rana, sannan suna tabbatuwa wajen kyautata wa mabukata, suna karanta tarihin Manzo a wannan rana, sannan karamar Manzo ta kasance tana bayyana a kowane lokaci.
Wannan nassi guda biyu na tarihi wanda dukkansu daga karni na goma suke suna, yana nuna cewa bukin ranar haihuwar manyan bayin Allah wani abu ne wanda yake da tsawon tarihi a tsakanin musulmai, ta yadda manyan masana da malaman musullunci sun kasance suna yin wannan buki na ranar haihuwar Manzo (s.a.w) sannan yin wannan buki na ranar haihuwar Manzo ba ya nuna wani abu sai nuna kauna da soyayya ga Manzo (s.a.w) Dukkammu mun san cewa daya daga cikin ginshikan musulunci shi ne nuna soyayya ga Manzo Allah kamar yadda Kur'ani yake cewa: "Idan har ya kasance iyayenku da 'ya'yanku da danginku da matayenku da kabilarku, da dukiyarku wacce kuke tara ta, da kasuwancin da kuke jin tsoron faduwa a cikinsa, da gidajen da kuke kauna, sun fi soyuwa gareku a kan Allah da manzonsa, da yin jihadi a tafarkin Allah, sai ku saurara, har sai al'amarin Allah ya zo muku, Kuma lallai Allah ba ya shiryar da mutane fasikai" .
Soyayya da kaunar Manzo wani abu ne wanda Kur'ani ya yi umarni da shi kuma hadisai sun zo a kan karfafa hakan, Manzo (s.a.w) yana cewa: "Ina rantsuwa da wanda rayuwata take a hannunsa, dayanku bai yi imani ba har sai na fi soyuwa gare shi a kan iyayensa da 'ya'yansa" .
Ruwayoyi da dama sun zo a kan haka, don haka kawo dukkansu a nan zai sanya mu tsawita, don haka zamu wadatu da wannan. Babu shakka wadanda suke yin bukukuwa a ranar haihuwar Manzo ba su da wata manufa wacce ta wuce nuna soyayyarsu ga Manzo, a hakikanin gaskiya suna amfani da wannan bukukuwa ne don su bayyanar da soyayyarsu ga manzon Allah (s.a.w)
Kur'ani yana bayar da umarni a kan cewa musulmai bayan sun yi imani da Manzo wannan bai wadatar ba sai sun nuna girmamawarsu ga Manzo, ga kuma abin da Kur'ani yake cewa: "Wadanda suka yi imani suka kuma girmama shi kuma suka taimake shi, sannan suka bi hasken da aka saukar masa tare da shi, wadannan su ne masu babban rabo"
Wannan aya tana bai wa musulmi umarni guda hudu kamar haka:
1-Su yi imani da Manzo.
2-Su girmama shi.
3-Su taimaki Manzo.
4-Su bi hasken da aka saukar masa tare da shi.
Tare da la'akari da wadannan umarni guda hudu, girmama Manzo a ranar haihuwarsa, yana nuna aiki ne da umarni na biyu, wanda ake magana a kan girmama Manzo. Kur'ani yana bayyanar da cewa daya daga cikin ni'imomin da Allah ya yi Manzo shi ne ta yadda ya daukaka shi kamar yadda ayar Kur'ani take cewa: "Shin a mu ne muka yaye maka kirjinka ba, sannan muka cire nauyin da yake kanka, nauyin da yake gab da ya karya maka kashin baya, sannan muka daukaka ambatonka" .
Tare da la'akari da abin da Manzo Allah yake cewa dangane da Manzo (s.a.w) ta fuskar daukaka sunansa da ambatonsa a duniya, kuma yana kidaya wannan daya daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa manzonsa, don haka bukukuwa da musulmai suke yi ranar haihuwarsa suna daya daga cikin aiki da abin da wannan aya take umarni da shi.
Saboda haka tare da kula da ayoyin da hadisan da aka ambata a sama, idan har muslmai ba su hada wadannan bukukuwa ba ayyukan haram kamar abin da ya shafi kide-kide na haram da wakokin da ba su dace ba, to menene hukuncin wannan? Shin girmama Manzo ne ko kaskantar da shi? Nuna soyayya gare shi ne ko nuna kiyayya? Shin yana daya daga cikin daga sunan Manzo da tunawa da shi ko kuwa ba ya daga ciki?
Amsar wannan a fili yake, domin kuwa kowa ya san cewa wannan yana daya daga cikin girmama Manzo da nuna soyayya a gare shi, sannan yana taimaka wa wajen daga sunan Manzo (s.a.w), don haka shin zai yiwu a haramta wadannan bukukuwa?
Dalilan Masu Haramta Bukin Ranar Haihuwar Manzo
Masu sabani a kan yin bukin ranar haihuwar bayin Allah na kwarai, suna labewa da wasu dubaru guda biyu domin ba ma zamu kira su da dalilai ba domin kuwa sam ba dalilai ba ne, abubuwan da suke kawowa kuwa guda biyu su ne kamar haka:
1-Bukin ranar haihuwa ba bai zo ba a cikn addini!
Bukin ranar haihuwar Manzo bai zo ba a cikin Kur'ani da Sunna, don haka wannan buki bidi'a ne!
Amsar wannan kuwa a fili take, tare da kula da bahsin da muka yi a baya dangane da "bidi'a", domin kuwa bidi'a ita ce yin wani abu a cikin addini wanda bai zo ba daga Kur'ani ko kuma ba shi da asali daga Kur'ani ko Sunna, alhalin cewa nuna soyayya ga manzon Allah da girmama shi yana da tushe daga Kur'ani.
Amma a cikin ruwayoyin musulunci dangane da musamman maulidin Manzo ruwaya ba ta zo ba a kan haka, sannan babu wani musulmi da yake da'awar cewa akwai wani dalili wanda yake magana musamman a kan bukin ranar haihuwar Manzo. Sai dai musulmai suna cewa ne Allah madaukaki ya umurce su da su girmama Manzo a duk tsawon shekara a ko'ina ne, wanda daya daga cikin wadannan wurare shi ne bukin ranar haihuwar Manzo, wato yana daga cikin aikata wannan umarni na Allah madaukaki.
Daga karshe yana da kayau mu yi nuni da wannan abu daga Kur'ani mai girma inda yake maganar cewa: Annabi Isa (a.s) ya nema wa sahabbansa abinci daga sama, sakamakon haka ne sai sahabbansa suka ce, zamu rika yin bukin ranar da wannan abinci ya sauka daga sama muka cika cukkunanmu da shi ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka:
"Ya Ubangiji ka saukar mana da abinci daga sama, ta yadda zai zama idi gare mu ga kuma na farko da karshemmu, sannan aya ce daga gare ka, ka azurta mu, kuma kai ne fiyayyen mai azirtawa".
Babu shakka idan har ranar da a ka saukar da abinci daga sama, wanda yake wata ni'ima mai wucewa, ya cancanci a yi bukin shekara saboda shi, me zai hana ayi bukin ranar haihuwar Manzo da murna a kowace shekara kasantuwar wata ni'ima ce daga Allah kuma madawwamiya wacce ya yi ga dukkan 'yan Adam?
2- Girmama ranar haihuwa wani nau'i ne na bauta
Abin da ya fi komai abin mamaki a nan shi ne wai yin rin wadannan bukukuwa na ranar haihuwar Manzo wai sun dauke shi a matsayin bauta ga shi Manzo (s.a.w) a kan haka ne suke cewa: Bukukuwan da suka cika garuruwan musulmai da sunan waliyyai, nau'i ne na bautarsu da girmama su.
Kuskurensu a nan shi ne duk wani nau'i na girmamawa sun dauke shi a matsayin bauta, alhalin cewa bauta bayan girmamawa tana bukatar wani abu daban kafin ta zama bauta, wannan kuwa shi ne mutum ya yi imani da cewa wannan abin da yake girmamawa Allah ne kuma ya cancanci a bauta masa. Amma idan ya zamana kawai girmamawa ce zai mai da shi bauta, to tabbas ba za a samu wani mai kadaita Allah ba a duniya!
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)