Sakamakon Ayyuka
Sakamakon Ayyuka
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Ayyuka Da Kyakkyawan Sakamako
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
A sakamakon bincike na ilimi da falsafa an tabbatar da cewa mutuwa ba ita ce karshen rayuwar dan Adam ba, mutuwa kawai cirata ce daga wata duniya zuwa wata domin ci gaba da rayuwa, don haka hakikanin dan Adam ba shi ne jikinsa ba, ta yadda sakamakon lalacewarsa ya zamana mutum ya kau, hakikanin dan Adam shi ne ruhinsa kamar yadda muka tabbatr a baya, wanda sakamakon mutuwa ba zai kau ba, zai ci gaba da rayuwa a wata duniyar ta daban da wani jikin da ya dace da shi, wanda malamai suka ambata da "barzakh".
Sakamakon mun yi cikakken bayani a kan wannan magana a nan ba sai mun sake Maimaitawa ba, yanzu abin da muke magana a kansa shi ne, shin wai wadanda suka rigamu gidan gaskiya suna iya amfana da wasu ayyukammu ko kuwa ba zasu amfana ba.
Da wata ma'nar shin idan muka yi wani aiki mai kyau a matsayin kyauta ga ruhin iyayemmu wadanda ba su raye a wannan duniyar, shin zai yi amfani a gare su kokuwa?
Dangane da wannan magana dole ne mu koma zuwa ga Kur'ani da hadisi domin mu samu amsar wadannan tamabayoyi da muka ambata daga tushen addini wato Kur'ani da sunnar ma'aiki (s.a.w).
A baya mun yi tunatarwa da cewa imani ba tare da aiki ba, ba zai amfanarba, sakamakon haka ne ya zamana ayoyi suna bayanin imani tare da aiki da wannan jumla kamar haka: "Wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki kyakkyawa". Wannan jumla ta zo a wurare daban-daban a cikin Kur'ani. Don haka mutum ba zai iya dogara da imaninsa ba kawai ba tare da aiki ba, ko kuma da dogaro da cewa idan na rasu dana zai yi mini aiki mai kyau a bayana, don haka tsirar mutum tana tare da imaninsa da aiki mai kyau.
A karshen karni na farko da farkon karni na biyu aka samu wasu gungu masu suna "Murji'a" wadanda kawai suke dogara da yin imani, ba tare da dogaro ba a kan yin aiki, shugabannimu sun soki wannan ra'ayi sannan iyayemmu da kakannimmu suna horan mu da cewa mu yi wa 'ya'yanmu tarbiyya kafin su fada tarkon "murji'a".
Tunanin ceto wanda ake jingina shi zuwa ga iyalan gidan Manzo wanda ba tare da kokari wajen yin aiki ba, wani tunani ne wanda ba da shi tushe. Wannan tunani ya samo asali ne daga yahudawa, wadan suka dauki kansu a matsayin al'umma mafificiya, sannan suka dauki kansu cewa su 'ya'yan Allah ne, sakamakon haka ne suke kore duk wani nau'i na zunubi daga kawunansu, sannan tunaninsu shi ne cewa: "mu 'ya'yan Allah ne kuma wadanda suke sonsa"
Daga wannan bayanin zamu fahimci cewa tsirar mutum kawai ta rataya ne ga ayyukansa kyawawa, don haka dogara da ayyukan wani ko jingina kai ga wasu abubuwa mararsa tushe tunani ne wanda ba shi da inganci kuma sam bai kamata a dogara a kansa ba.
Amirul mumininn Ali (a.s) dangane da aiki yana da wasu jumloli masu kawatarwa a kan karfafa batun aikin, wanda a nan zamu kawo guda biyu kawai daga cikinsu kama haka:
1-"Ku sani yau rana ce ta aiki babu hisabi, gobe kuwa rana ce ta hisabi babu aiki" .
2-Ku sani yau rana ce ta koyo, gobe kuwa rana ce ta gasa, wanda layin karshe na wannan gasa shi ne aljanna, wanda ya kasa kaiwa kuwa makomar shi ita ce jahannama, shin akwai wani daga cikinku wanda zai tuba daga laifukansa kafin mutuwa ta riske shi, shin akwai wanda zai yi aiki kafin ranar kaico ta riske shi".
Tare da imani da wannan asali shin akwai sauran Bahasi kuma a kan cewa, shin wadanda suka riga mu zasu iya amfana daga ayyuka kyawawa da muke yi, misali kamar idan muka yi wani aiki a mai makonsu zasu iya amfana da wannan aiki namu?
Muna bukatar amsar wannan tambaya daga Kur'ani da sunnar Manzo wanda zamu ga cewa tabbas amsar wannan tambaya shi ne tabbas zasu iya amfana.
Kafin mu ci gaba da bayani kan wannan al'amari zamu yi tunatarwa a kan cewa ayyukan mutum a mai makon wani sun kasu zuwa gida biyu:
1-Wani lokaci mutumin da ya rasu yana da hannu wajen ayyukan wanda yake raye.
2-Wani lokaci kuwa ba shi da wani hannu sai dai kawai shi mumini ne.
Dangane da kashi na farko kuwa wanda ya kasance mamaci yana da hannu a cikin ayyukan wanda yake raye babu wata magana a cikin wannan. Ya wadatar dangane da wannan mu saurari hadisin Manzo wanda duka bangarori guda biyu suka ruwaito shi.
Abu hurera yana cewa Manzo (s.a.w) ya ce: "Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke sai guda uku kawai; sadaka wacce take gudana, ko ilimi wanda ake amfana da shi, ko kuwa dan kwarai wanda zai yi masa addu'a".
1-Sadaka mai gudana ita ce kamar gina masallaci, asibiti makaranta da dai sauransu, wadanda mutane suke amfani da su.
2-Ilimin da mutane suke amfana da shi.
3-Dan kwarai wanda zai rika yi wa mutum addu'a.
Idan mutum ya rasu zai ci gaba da amfana da wadannan abubuwa guda uku da muka ambata a sama, domin kuwa yayin da yake da rai yana da hannu wajen samar da wadannan abubuwa, kamar masallaci da ya gina lokacin da yake raye sannan yanzu mutane suna ci gaba da amfani da shi, ko kuwa littafi ya rubuta har yanzu mutane suna ci gaba da amfana da shi, ko kuwa ya haifi da sannan ya yi masa tarbiyya ta gari yana yi masa addu'a.
Jarir Bn Abdullah yana cewa: Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi wata Sunna mai kyau a cikin addini sannan mutane suka yi aiki da ita bayansa, za a rubuta masa ladar wanda ya yi aiki da ita ba tare da an tauye ta wanda ya yi aikin ba. Haka nan duk wanda ya yi wata Sunna mummuna (wato ya yada wani abu da bai dace ba) a cikin addini sannan wasu suka yi aiki da ita, to yana da zunubin duk wanda ya aikata ba tare da an tauye zunubin wanda ya aikata hakan ba .
Saboda haka amfana da lada ko zunubin da wadanda suka riga mu zasu yi ta wannan fuskar ce, wannan kuwa saboda hannun da mamaci yake da shi wajen aiwatar da hakan yayin da yake raye, wato lokacin da yake raye ya bayar da gudummuwa wajen yada aikin assha ko kuma ya taimaka wajen yada aikin kwarai, domin idan da bai yi hakan ba mutane ba zasu samu damar aikita hakan ba.
Tambaya zata kasance dangane da bangare na biyu ne wanda idan ya kasance mutum ba shi da hannu wajen ayyukan da wani mutum yake yi bayan rasuwarsa, shin wannan mamaci zai iya samu ladar aikin wannan rayayyen, amsar da Kur'ani da hadisi kuwa suka bayar dangane da wannan ita ce zai ya samu. Wannan amsa kuwa a takaice ita ce, idan mutum wanda yake da tsarkin zuciya ya nema wa wani mamaci gafara ga Ubangiji, ko kuma ya yi wani aiki a mai makon mamaci ko kuma ba da wannan niyyar ba, sai ya bayar da wannan lada ga mamaci a mastayin kauta, wannan ladar zata isa zuwa ga wannan mamacin. Kur'ani mai girma a wurare da yawa yana bayyanar da yadda mamata zasu iya amfana daga neman gafarar da wadanda suke raye suke musu kamar haka:
A-Neman Gafarar Mala'iku Ga Muminai
Kur'ani mai girma a fili yake ya bayyanar da cewa mala'iku suna nema wa masu imani gafara a wajen Allah madaukaki. Idan har ladar hakan ba ta isa ga mamaci wannan neman gafarar da mala'ik suke zai zama marara ma'ana. Ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka:
1-Wadanda suke daukar al-arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, kuma suna neman gafar ga wadanda suka yi imani suna cewa ya ubangijimmu ka yalwatar da rahama da ilimi ga komai, kuma ka gafarta wa wadanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, katseratar da su azabar jahannam .
2-"Ya rage saura kadan sama ta tsage daga bisanta, kuma mala'iku suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, sanann suna neman gafara ga wadanda suke a bayan kasa, Ku sani Allah shi ne mai gafara mai jin kai" .
Dangane da wadannan ayoyi guda biyu da suka gabata suna magana ne a kan neman gafarar da mala'iku suke yi wa muminai, amma aya ta uku zamu ga yadda muminai ne suke nema wa junansu gafara kamar haka:
3-"Wadanda suka zo bayansu, suna cewa, ya Allah a gafarta mana da 'yan'uwammu wadanda suka riga mu da imani, kada sanya wani jin zafi cikin zuyarmu dangane da wadanda suka yi imani, ubangijimmu lallai kai mai tausayi ne kuma mai jin kai" .
Wadannan ayoyi guda uku suna nuna mana yadda wadan suka riga mu suke amfana da neman gafarar wadanda suke raye suke yi musu. Sannan wannan amfanar da suke yi bai takaita ba da neman gafara kawai, ya hada da abubuwan daban-daban banda wannan, kamar yadda ruwayoyi suka bayyanar da hakan:
Kyakkyawan Aiki Da Bayar Da Ladar Ga Wadanda Suka Rasu
Dangane da kyautata wa wadanda suka rasu ruwayoyi da dama sun zo domin su bayyanar da hakan a cikin Littattafan hadisi, kuma dukkansu suna bayyanar da cewa idan mutum ya yi wani aikin lada a mai mai kon iyayensa, ko wani daga cikin dangi ko abokai to ladar zata je wa wanda aka yi saboda shi. Don haka a nan ya dace mu kawo wasu kadan daga cikin wadannan ruwayoyin.
1-Amfanar mamaci daga ladar azumi da hajji da aka yi a mai mai konsa
A-Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya rasu kuma ana binsa azumi, sai babban dansa ya rama masa a madadinsa.
B-Ibn Abbas yana cewa: wata mata ta zo wajen Manzo (s.a.w) sai ta ce mahaifiyata ta rasu kuma akwai azumi a kanta.
Sai Manzo ya ce: Idan akwai bashi a kanta ke ce zaki biya? Sai wannan mata ta ce ni zan biya! Sai Manzo (s.a.w) ya ce: To biyan bashin Ubangiji shi ya fi muhimmanci.
C-Wata mata ta zo wajen Manzo sai ta ce: Na 'yantar da baiwa a madadin mahaifiyata. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ladar hakan zata isa zuwa gareta. Sai wanann mata ta kara da cewa, sannan kuma azumin wata daya yana kanta, shin zan iya yin wannann azumin a madadinta? Sai Manzo ya amsa mata da cewa; kina iya yin azumin. Sannan sai ta kara da cewa mahaifiyata ba ta yi aikin hajji ba, ina iya yin hajji a madadinta? Sai Manzo ya amsa mata da cewa kina iya yi.
2-Amfanar mamaci daga sadaka
Kamar yadda muka ambata cewa ruwayoyin da suka zo dangane da wannan suna da yawan da ba zai yiwu mu kawo dukkansu ba, amma a nan zamu kawo hadisi guda biyu kawai wadan zasu iya warware mana dukkan wannan matsalar.
A-A'isha tana cewa: Wani mutum ya zo wajen manzon Allah sai ya ce: Mahaifiyata ta rasu sannan kuma ba ta yi wasiyya ba, sannan ina tunanin cewa idan da har ta iya yin magana zata bayar da sadaka ne, yanzu idan na bayar da sadaka a madadin mahafiyata ladar zata je mata?
Sai Manzo (s.a.w) ya amsa da cewa me zai hana!
B-Sa'ad Bn Ubada ya kasance daya daga cikin sahabban Manzo, lokacin da mahaifiyarsa ta rasu, sai ya zo wajen manzon ya ce: wace sadaka ce tafi kowace daraja? Sai Manzo (s.a.w) ya amsa masa da cewa ta ruwa.
Sa'ad Bn Ubada sai ya gina rijiya ya ce wannan rijiya saboda maharfiyar Sa'ad.
A nan ya kamata mu yi bayani a kan wadannan ruwayoyi kamar haka. Wani lokaci wasu mutane ba tare da sun yi alkawari ba zasu yi wasu ayyuka na kwarai, sannan su bayar da ladar wadannan ayyukan zuwa ga wadanda suka riga mu. Babu shakka duk lokacin da mutum ya yi wani aiki na kwarar kuma saboda Allah, tabbas zai samu ladar wannan aikin daga Ubangiji a matsayin baiwa ta Allah madaukaki ba wai don ya cancanci hakan ba ne, amma Allah madaukaki ta hanyar wannan baiwar yake bayar da ladar ayyuka. Sannan ta hanyar wadannan ruwayoyin mun fahimci cewa Allah madaukaki ya bayar da damar cewa ana iya yin ayyukan lada a madadin wadanda suka riga mu sannan a yi kyautar ladar zuwa garesu.
Bakance Da Waliyyan Allah
Musulmai sakamakon soyayya ta musamman da suke da ita ga Manzo da iyalansa tsarkaka, wani lokacin domin samun kusanci zuwa ga Ubangiji sukan yi alkawarin wani abu zuwa ga waliyyan Allah, ta yadda yayin da zasu yi wannan bakance zasu ce na yi wa Allah alkawarin kaza, amma wannan ba zai hana ladar ta je wa Manzo da waliyyan Allah ba.
Tare da la'akari da wannan zamu gane ma'anar wannan jumla "Na yi Alkawari zuwa ga Allah zan yanka rago ga annabi ko wanda ya yi mini wasiyya". A nan dole a lura da kalmar Allah ba tana bayar da ma'anar kalmar Annabi ba ce.
A cikin wadannan kalmomi guda biyu duk da cewa akwai wadansu abubuwa masu kama da juna amma ba daya suke ba, domin kuwa ga yadda abin ya zo a cikin harshen larabci "Lillahi alayya an azbahu shatan linnabiy" lamun din da ya zo a cikin kalmar "Lillahi" yana nuna neman kusanci ga Allah ne, amma lamun da ya zo a cikin kalmar "linnabiy" yana nuna wanda aka yi aikin don shi ne, sannan cikin sa'a duka wadannan lafuzan guda biyu sun zo a cikin Kur'ani mai girma kamar haka:
Dangane da wannan ga abin da Allah yake cewa: "Ka ce ni ina yi muku wa'azi ne da abu guda daya shi ne ku tsayar da salla domin Allah (Lillah).
A cikin wata ayar kuwa yana cewa: Lallai sadaka saboda mabukata ce (lilfukara).
Saboda haka bai kamata ba a dauki wannan wani abu na hada Allah da waninsa wato shirka, don mutum ya ce na yi niyyar yanka wannan domin Manzo, wato ma'anarsa shi ne na yi wannan ne saboda Allah kuma ladar zuwa ga Manzo. Saboda haka ma'anar jumlar "Lillahi, linnabiy" shi ne na yi wannan aiki ne ladarsa zuwa ga Manzo don neman kusanci zuwa ga Allah. Sannan irin wannan ya zo a cikin hadisin Ubada da ya gabata inda yake cewa na gina wannan rijiya ne (li'ummi) wato dan mahaifiyata. Ma'aunin shi ne niyyar da aka yi aikin ba zahirin aikin ba.
Masu hadisi sun ruwaito daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Lallai ayyuka suna tare da niyyar da aka yi su tare da ita. Tare da la'akari da ma'anar wannan hadisi dole ne mu bambance wani aiki da mai kadaita Allah zai yi, kamar ya yanka wata dabba domin Manzo (s.a.w) a matsayin bakance, da wanda wani mushiriki zai yanka wata dabba ga gumakansu, duk da cewa wadannan abubuwa guda biyu sun yi kama da juna amma akwai gayar bambanci idan muka lura da badininsu, kuma ba za a taba daidaita su ba.
Mutumin da yake kadaita Allah ya yi alkawari ne ya yanka wani abu zuwa ga Allah, kuma ya yi wannan yanka ne domin ya samu lada daga Allah. Amma mushrikai suna yanka wadannan abin yanka nasu ne da sunan gumakansu, kuma suna neman lada ne daga gumakan nasu. Saboda haka ta yaya za a iya daidaita wadannan ayyuka guda biyu? Idan har ya zamana zahirin aiki shi ne ma'auni wanda zai yi hukunci a kansa, to zai zama aikin hajji ya yi kama da aikin mushrikai, domin kuwa suna zagaya gumakansu ne suna bautarsu, muma kuma muna zagaya dakin ka'aba muna yin dawafi kuma muna sumbatar Hajrul aswad. Sannan suna yanka ragunansu a mina da sunan gumakansu, muma muna yanka ragunammu na hadaya a wannan rana, amma shin wadannan ayyukan guda biyu zasu zama daya?
Abin da yake sanyawa masu bautar gumaka suna bauta musu shi ne, neman yardarm gumakan, amma abin da yake sanyawa mumini yake bauta shi ne neman yardar Allah. Mai kadaita Allah yana bayar da kyautar ladar yankansa zuwa ga annabi da waliyyan Allah, sannan ruwayoyin suna nuni ga ingancin hakan.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012