Muassasar alhasanain (a.s)

Yin Rantsuwa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Yin Rantsuwa

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Rantsuwa Da Wanin Allah

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
A fasalin da ya gabata mun yi magana ne a kan hada Allah da wasu bayinsa na gari, wato mutum ya nemi wani abu daga Allah ta hanyar hada shi da matsayin wani daga bayin Allah.
Amma a cikin wannan fasali abin da zamu yi magana a kansa shi ne rantsuwa da wanin Allah. Mu musulmai saudayawa yayin da muke magana da abokanimmu mukan yi rantsuwa da Allah da Manzo da ka'aba da makamantansu, cewa ban yi kaza ba. Ko kuma ina rantsuwa da Kur'ani zan yi kaza, amma ta bangaren shari'a menene hukuncin wannan abu shin ya halasta ko kuwa bai halasta ba?
Kafin mu bayar da amsar wannan tambaya zamu yi bayanin wasu abubuwa guda biyu a matsayin gabatarwa kamar haka:

1- Menene Dalilin Rantsuwa Da Wanin Allah A Cikin Kur'ani?
A cikin Kur'ani kusan wurare arba'in ne aka yi rantsuwa kuma Allah yana rantsuwa ne da wasu abubuwa da ba shi ba, misali yakan yi rantsuwa da baure, zaitun, Dotsen Duri sina, Baladil amin, dare da rana, Fajr, Rufi madaukaki, darare guda goma, shafa'i da Wutri, Dur, Kitabul mansur, Baitull ma'amur, Bahrul masjur, da ruhin Manzo:
"Allah yana rantsuwa da itaciyar baure da zaitun, sannan yana rantsuwa da duri sina. kuma yana rantsuwa da garin Makka mai aminci".
"Allah yana rantsuwa da dare yayin da ya yi duhu, kuma yana rantsuwa da rana yayin da ta haskaka duniya" .
"Allah yana rantsuwa da Fajr da darare goma. Sannan yana rantsuwa da shafa'i da wutri. Kuma Allah yana rantsuwa da dare mai duhu yayin da ya koma rana" .
"Allah yana rantsuwa da dutsen duri sina, sannan yana rantsuwa da rubutaccen littafi, wanda aka rubuta a cikin takarda mai fadi, kuma Allah yana rantsuwa da baitil Ma'amur, sannan yana rantsuwa da rufi madaukaki, kuma Allah yana rantsuwa da kogi mai igiyoyin ruwa" .
"Ina rantsuwa da rayuwarka ya Manzo, lallai suna cikin magagin dimuwa" .
Dalilan da suka sanya Allah madaukaki yake rantsuwa da wadannan abubuwa yana iya zama daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu kamar haka:
A- Sanya wa mutum tunanin ya yi bincike a kan sirrinka da suke cikin wadannan abubuwan, ta yadda zai yi tunani a kansu, domin kuwa tunani a kan halitta yana daya daga cikin siffofin masu imani. Sannan Kur'ani yana kira zuwa ga tunani kamar haka:
"Ka ce ku kalla ku gani abin da yake cikin sammai da kassai" . Sannan a wata ayar yana cewa: "Wadanda suke tunani a cikin halittar sammai da kassai, ubangijimmu lallai ba ka halicci wannan ba hakan babu wata manufa, tsarki ya tabbata gareka ka tseratr da mu daga zabar wuta". Haka nan Allah madaukaki yana rantsuwa da rana da wata, sannan yana rantsuwa da dare da rana, ga abin da yake cewa a cikin Kur'ani:
"Allah yana rantsuwa da rana da haskenta, kuma Allah yana rantsuwa da wata yayin da ya biyo rana, kuma Allah yana rantsuwa da yini yayin da ya yi haske, Kuma Allah yana rantsuwa da dare yayin da ya rufe rana. Sannan yana ranstuwa da sama da abin da ya gina ta. Kuma yana rantsuwa da kasa da abin da ya shimfida ta".
Manufar dukkan wannan rantsuwa shi ne janyo hankalin mutum zuwa ga tunani a kan ayoyin Ubangiji, ta yadda sakamakon haka ya kara karfafa imaninsa da kadaita Ubangiji.
B- Dalili na biyu kuwakan yin wannan rantsuwa shi ne, bayyanar da matsayin wadannan abubuwa na halitta wanda Allah yake yin rantsuwa da su, ta yadda suke da matsayi a wajen Allah madaukaki ta sakamakon haka yake rantsuwa da su, a kan haka ne yake rantsuwa da ran Manzo (s.a.w) inda yake cewa: "Ina rantsuwa da ranka lallai sunacikin magagin dimuwa".

2- Kur'ani Abin Koyi Ne
Kur'ani littafi ne mai shiryaswa kuma abin koyi, yin rantsuwa da wani abu wanda ba Allah ba a cikin Kur'ani yana nuna cewa wannan abin ba shirka ba ne sannan kuma ba haramta ba. Sannan idan irin wannan rantsuwa ya kebanta da Allah ne, ta yadda wasu ba su da hakkin yin irin wannan rantsuwa, to da ya kamata a bayyanar da hakan a cikin Kur'ani ko maganganun Manzo (s.a.w)
Kur'ani yana nuna cewa sifffar "takabbur" (nuna isa) siffar Ubangiji ce, amma hankali da ruwayoyi suna nuna cewa wannan siffa ta girman kai, ta takaita ne kawai ga Allah, wanda yake da dukkan siffofi na kammala da jamala daga zatinsa, ba waninsa ba wanda ba shi da wata kammala sai wacce ya samu daga Allah madaukaki.
Kasantuwar rantsuwa da wanin Allah kusan arba'in a cikin Kur'ani yana bayyanar da cewa idan da wannan aiki ba shi daga kyawawan ayyuka, to ba shi daga cikin ayyuka kuma mararsa kyawu. Kuma idan har irin wannan ranstuwa shirka ce, to yana nufin kenan Allah wanda yake hana mu daga yin shirka, shi da kansa ya aikata hakan! Daga wannan ne zamu fahimci cewa rantsuwa da wanin Allah wanda yake nuna girma da daukakar wanda aka yi ranstuwar da shi, ba shi da wata matsala.
Wadansu wadanda suke fito-na-fito da irin wannan al'amari wanda yake da dalilai masu karfi, sun yi kokarin tawilin wadannan ayoyi ne, ta yadda suka sanya kalmar"Rabb" a farkon irin wadannan rantsuwa, misali suna cewa, idan Allah ya ce ina ranstuwa da rana, wato ma'anarsa ina rantsuwa da ubangijin rana, wato "rabbis shams", saboda haka idan muka lura rantsuwa guda daya tak kenan ta zo a cikin Kur'ani, wannan kuwa shi ne ranstuwa da Allah! A nan kuwa akwai sauran magana domin kuwa wannan shi ne ake kira da tafsiri da ra'ayi, domin kuwa mai yin wannan tawilin tun farko yana da wata akida sakamakon zahirin wadannan ayoyi ba su dace da wannan akida ta shi ba sai ya fake da yin tawili kamar yadda muke gani!

Rantsuwa Da Wanin Allah A Cikin Sunnar Manzo (s.a.w)
A cikin sunnar Manzo ma akwai misalai da dama dangane da ranstuwa da wanin Allah, don haka a nan zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:
1-Muslim yana ruwaitowa a cikin sahih dinsa: Wani mutum ya zo wajen manzon Allah sai ya ce: wace sadaka ce ta fi kowace lada?
Sai Manzo ya ce: "Ka yi ranstuwa da babanka, ya fi ka bayar da sadaka kana mai lafiya alhalin kana tunanin talauci da rashi a kan ci gaba da rayuwarka" .
2-Sahih Muslim ya ruwaito a cikin sahih dinsa yana cewa:
"Wani mutum ya zo wajen manzon Allah daga Najad yana tamabaya a kan musulunci? Sai Manzo ya ce masa: Musulunci shi ne salloli guda biyar a cikin dare da rana.
Sai ya ce bayansu akwai wani abu da ya hau kaina? Sai Manzo ya ce masa babu…sai dai ka yi nafila da azumin watan Ramadhan.
Sai ya ce akwai sauran wani abu?
Sai Manzo ya ce babu. Sai dai ka yi nafila. Sai ya ambata masa zakka.
Sai wannan mutum ya ce: "Akwai sauran wani abu? Sai Manzo ya ce babu sai dai ka yi nafila. Sai wannan mutum ya juya yana cewa: wallahi ba ragi ba kari a kan wannan, sai Manzo ya ce masa ka rabauta, ina rantsuwa da babansa idan da gaske yake yi zai rabauta, ko kuma ya ce ina ranstuwa da babansa zai shiga aljanna idan ya zama mai gaskiya a kan a bin da ya fada" .
Wannan kuwa ba kawai Manzo ba ne ya yi rantsuwa da wanin Allah, domin kuwa a hudubobin da wasikun Imam Ali (a.s) a wurare da dama ya yi ranstuwa da wanin Allah.
Imam Ali (a.s) wanda yake misali wajen tarbiyar musulunci, ya yi ranstuwa da ransa a cikin hudubobi da wasikunsa awurare da dama, sannan a wani wurin yana rantsuwa da rayukan iyayen masu saurarensa.
Imam Malik a cikin mu'uda yana cewa: Wani mutum ya shigo Madina yana mai karar gwamanan Yaman a wannan zamani, ya ce: Hakimin Yaman ya yanke mini hannu da kafa da dalilin cewa na yi sata, a wannan daren da ya shigo Madina ya ci gaba da ibada, ibadarsa ta janyo hankalin khalifa ya ce masa: "Ina rantsuwa da babanka darenka ba daren barawo ba ne".

Fatawawoyin Malaman Sunna A Kan Ranstuwa Da Wanin Allah
Ibn Kudama a cikin littafin Mugni wanda aka rubuta shi bisa ga fikhun mazhabar Hambaliyya, yana rubuta cewa: Idan wani ya yi ranstuwa da Manzo, rantsuwarsa ta tabbata, domin kuwa Manzo yana daya daga cikin rukunnan shahadar musulunci, don haka idan ya saba, dole ne ya biya kaffara .
Hanafiyya suna cewa: Rantsuwa da mahaifi da ran mutum makaruhi ne.
Shafi'iyya suna cewa: Rantsuwa da wanin Allah tare da nisantar shirka makaruhi ne.
Daga Malik kuwa an ruwaito maganganu guda biyu ne, wanda daga cikinsu shi ne, rantsuwa da wanin Allah makaruhi ne.
Tare da lura da wadannan ayoyi da hadisai da muka ambata zamu iya gane hukuncin wannan rantsuwa a fili, don haka yanzu zamu yi bincike ne dangane da dalilan masu musun wannan al'amari.

Dalilan Masu Haramtawa
Masu musun rantsuwa da wanin Allah suna kafa dalilai ne da wasu hadisai guda biyu kamar haka:
1-Manzo (s.a.w) ya ji Umar yana cewa na rantse da babana, Sai Manzo ya ce: LAllai Allah ya hane ku da ku yi rantsuwa da iyayenku, wanda yake so ya yi rantsuwa ya yi rantse da Allah ko ya yi shiru" .

Amsa
Wannan hadisi ba sheda ba ne ga masu musun wannan al'amari:
Domin kuwa akwai yiwuwar cewa an hana sahabbai da su yi ranstuwa da iyayensu domin iyayensu sun kasance mushrikai ba mutanen kirki ba, don haka irin wadannan mutanen sam ba su da wani matsayi a wurin Allah wanda suka cancanci a yi ranstuwa da su. Abin da yake karfafa wannan magana kuwa shi ne hadisan da zasu zo kasa kamar haka:
"Kada ku yi rantsuwa da mahaifi ko mahaifiyarku ko wani kishiyar Ubangiji".
"Kada ku yi rantsuwa da iyayenku ko dawagitai".
Tare da kula da ma'anar wadannan hadisai na sama zamu iya fahimtar abin da wancan hadisi yake magana a kansa, wannan kuwa shi ne Manzo ya hani Umar ne da yin ranstuwa da abin da suke bayyanar da shirka da mushrikai ne, domin kuwa a gefen iyaye ya ambaci kishiyoyin Ubangiji da dawagitai wadanda suke nufin gumaka da abin bauta. Saboda haka manufar Manzo shi ne hani a wani wuri na musamman ne ba dukkan rantsuwar ba.
Saboda haka tare da kula da wadannan hadisai da muka kawo ta yaya za a ce Manzo ya yi hani a kan ranstuwa da annabawan Allah da waliyyai masu girma da daukaka?
2-Wani mutum ya zo wa Ibn Umar ya ce da shi ina rantsuwa da ka'aba, sai ya ce da shi a a sai dai ka rantse da ubangijin Ka'aba, domin kuwa Umar ya yi rantsuwa da babansa sai Manzo (s.a.w) ya ce kada ka yi rantsuwa da babanka, domin kuwa duk wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah ya sanya wa Allah abokin tarayya.
A cikin wannan hadisi abubuwa guda uku ne suka zo kamar haka:
A- Wani mutum ya zo wajen Ibn Umar ya yi ranstuwa sai Ibn Umar ya hane shi da yin irin wannan rantsuwa.
B- Umar ya yi rantsuwa a gaban Manzo sai ya hane shi da irin wannan ranstuwa.
C- Maganar Manzo wacce take cewa duk wanda ya yi ranstuwa da wanin Allah ya yi shirka.
Abin da yake muhimmi a wajenmu a nan shi ne kashi na biyu da na uku. Domin kuwa Ijtihadin Ibn Umar da ya yi dangane da wanda ya zo wajensa yana rantsuwa da Ka'aba hujja ne a gare shi ba hujja ne a wurimmu ba. Abin da yake muhimmi shi ne tattaunawar Manzo tare da Umar.
Amma dangane da hanin Manzo (s.a.w) da ya yi wa umar lokacin da ya yi ranstuwa da babansa, wannan ya auku ne sakamaon cewa baban Umar ya kasance mushirki ne, yin ranstuwa da mushiriki kuwa ba shi da wani matsayi, sannan kuma yana nuni ga girmama itakanta shirkai.
Amma menene abin da Manzo ya yi hani a kansa a matsayin wata ka'aida ta baki daya?
Shin yana nufin duk wani nau'i na rantsuwa da wanin Allah ko kuwa ranstuwa da irin "Lata da Uzza" wadanda suka kasance gumanka larabawa na jahiliyya, wanda zuwa wancan lokaci akwai sauran tunanin ire-iren wadannan abubuwa na bautar gumama a cikin kwakwalan musulmai, ta yadda wani lokaci ba tare da sun ankara ba sukan yi rantsuwa da su.
Saboda haka alamomin suna nuna cewa Manzo ba ya yi hani ba ne ga dukkan rantsuwa da wanin Allah, kawai ya yi hani ne da rantsuwa da gumaka da makamantansu, domin kuwa a wani hadisin ga abin da Manzo (s.a.w) yake cewa:
"Duk wanda ya yi ranstuwa sai ya ambaci Lata da Uzza a cikin rantsuwarsa, to ya ce "La'ilaha Illallah".
Wannan hadisi idan aka hada shi da hadisai guda biyu da suka gabata, zai bayyanar mana da cewa zuwa wannan lokaci akwai sauran al'adun jahiliyyana bautar gumaka a cikin zukatan musulmi, ta yadda wani lokaci sukan tuna irin wannan al'adu na jahiliyya, kuma har sukan yi ranstuwa da gumaka. Saboda haka Manzo (s.a.w) domin ya kawar da wannan mummunan aiki ya fadi wannan jumla, shi kuma Ibn Umar ya hada wannan hani da aka yi a kan ranstuwa da mushiriki da yin rantsuwa da abubuwa masu tsarki. Alhalin kuwa manufar Manzo shi ne yin ranstuwa da mushiriki wanda ba shi da wani matsayin da za a yi rantsuwa da shi.
Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa duk da cewa yin ranstuwa da wanin Allah ya halasta, amma ta fuskar alkalanci yin rantsuwa da Allah ne kawai hujja wacce zata sanya a amince da abin da mai rantsuwa yake fada. Don haka ranstuwa da wanin Allah ba ta wadatar wajen raba husuma da jayayya da take tsakanin wasu mutane ba, malaman fikihu kuma sun yi bayani a fili a kan hakan .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)