Muassasar alhasanain (a.s)

Siffar Imam

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Siffofin Jagoran Duniya


Muna son Karin bayani game da muhimman siffofin da Imam Mahadi kuma Halifan Annabi na goma sha biyu yake da su?
Halifan Annabi (s.a.w) wanda yake lamunce cigaban rayuwar addini kuma mai amsa duk wata bukata ta dan Adam shi mutum ne mai daukaka wacce ta dace da matsayi madaukaki na jagoranci wanda yake da siffofi na musamman da suka hada da:
1- Tsoron Allah da nisantar duk abin ki, kuma siffa ta isma ta zama masa jiki ta yadda ba zai iya aikata mafi karancin sabo ba.
2- Ilimi wanda ya karba daga Annabi (s.a.w) wanda kuma yake saduwa zuwa ga ilimin Allah, domin ya amsa duk wata bukata ta mutane a kowane janibi da fagen da ya shafi Duniya da lahira.
3- Siffantuwa da kyawawan siffofi da dabi'u kyawawa a mafi daukakar daraja.
4- Iya tafiyar da al'amuran al'umma da kyakkyawan shugabanci bisa asasin koyarwar addini.
Bisa la'akari da wadannan siffofi da muka kawo ga Imami, a fili yake cewa zabar irin wannan mutum ya fi karfin ilimin dan Adam kuma Ubangiji ne kawai saboda ilimi maras iyaka da yake da shi, zai iya zabar halifofin Annabi (s.a.w), don haka mafi muhimmancin siffofin Imami shi ne Allah ne zai zabe shi.
Don haka ne ma sakamakon muhimmancin wadannan siffofin ne ya sanya zamu kawo su a takaice, kuma mu yi bayanin kowanne daga cikinsu.
Ya zama dole ne ga wanda jagorancin al'umma ya san addini a dukkan kusurwowinsa, kuma ya zama masani da dokoki da cikakkiyar masaniyar tafsirin ayoyin Kur'ani da kewayewa cikakkiya ga sanin sunnar Annabi, da bayanin addini, da amsa tambayoyn mutane a kowani fage, da kuma kyakkyawan jagoranci.
Irin wannan mutumin shi ne zai iya zama madoraga kuma makomar mutane kuma irin wannan ilimin ba a iya samunsa sai da wasidar saduwa da ilimin Allah (s.w.t), saboda haka ne ma Shi'a suke imani da cewa ilimin Imami kuma halifan Manzon Allah (s.a.w) dole ne ya zama ya karbe shi ne daga ilimin Allah maras iyaka.
Game da alamomin jagora kuwa, Imam Ali (a.s) yana cewa: Jagora shi ne mafi ilimin mutane, mafi saninsu da halal da haram din Allah, da kuma hakunce-hukunce daban-daban, da umarni da hani, da kuma duk abin da mutane suke bukata .

Daga cikin siffofi mafi muhimmanci na Jagora kuma sharadi na asasi akwai isma, kuma ita ana samunta ne daga ilimi da hakikanin abubuwa da kuma irada mai karfi. Saboda Imami yana da wadannan abubuwa guda biyu ya zama yana kare kansa daga aikata sabo, haka nan Imami ma'asumi ne wajan bayanin addinin da kuma aiki da shi, da kuma bayyanar da abin da yake maslaha ko cutuwa ga al'umma. Kuma akwai dalilai na hankali da na karbowa daga Kur'ani da ruwayoyi game da ismar Imami (a.s) wanda mafi muhimmancin dalilai na hankali su ne:
A- Kariya ga addini ta doru a kan ismar jagora ne; domin jagora yana da nauyin kare addini daga karkata a wuyansa kuma da shiryar da mutane, to zancensa dole ya zama abin karfafa daga ayyukansa don karfafawa ga ayyukan wasu a cikin al'amarin zamantakewar al'umma da kuma tasiri a kan haka. Don haka dole ne ya zama an kare shi a fahimtar addini da aiki domin ya iya shiryar da mutane shiriya ta gari.
B- Bukatar mutane zuwa ga jagora; mutane ba ma'asumai ba ne game da sanin addini da kuma aikata shi, don haka idan jagora shi ma haka yake to yaya za a yi mutane su dogara da shi idan ba shi da kariya daga kuskure. Kuma dole ne mutane su yi shakku game da biyayya garesu da kuma aiwatar da sakonsu da umarninsu idan ba su da isma.
Sannan akwai wasu ayoyi daga Kur'ani da suka karfafa game da wajabcin ismar jagora wacce daya daga cikinsu ta zo a surar bakara, wacce wannan aya ta zo ne bayan bayanin matsayin annabta, kuma Ubangiji ya bayar da wannan matsayi na jagoranci ga Ibrahim (a.s) bayan yana Annabi ne. A nan ne Ibrahim (a.s) ya nema daga Allah da ya bayar da wannan matsayi ga zuriyarsa. Sai Ubangiji ya ce:
"Alkawarina ba ya samun azzaluamai" Kuma Kur'ani mai girma ya dauki shirka a matsayin zalunci mafi girma kuma duk wani sabawa umarnin Allah yana ganinsa a matsayin sabo ne, to duk wanda ya taba yin sabo a rayuwarsa yana daya daga ckin wadannan azzalumai, kuma bai cancanci matsayin jagoranci ba. Don haka babu makawa Ibrahim (a.s) bai roki jagoranci ga mutanen da tun farko suke sabo ba sannan suka tuba suka koma mutanen da suke aikata aikin alheri sannan sai suka kuma aikata sabo, don haka muna iya cewa mutane sun kasu biyu:

1. Masu sabo tun farkon rayuwarsu sannan sai suka tuba suka koma na gari.
2. Marasa sabo atafau ba su taba yin sabo ba.
Kuma a fili yake cewa ; Ubangiji madaukaki ya toge kashi na farko ne a maganarsa, don haka wadanda suka rage su ne kashi na biyu.

Mutum yana rayuwa ne a cikin al'umma kuma al'umma tana da tasiri mai yawa a kan halayensa da dabi'unsa, don haka dole ya zama akwai zamantakewa ta al'umma mai dacewa domin gyara wannan tarbiyya tasa ingantacciya da kuma shiryar da shi zuwa ga Allah, kuma wannan ba zai yiwu ba sai karkashin hukumar Ubangiji. Saboda haka ne dole ne Imami ya zama yana iya tafiyar da al'umma, kuma ya yi amfani daga koyarwar Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) domin kafa hukumar musulunci.

Jagora shi ne shugaba a cikin al'umma don haka dole ne ya zama ya nisanci dukkan munanan dabi'u, kuma ya zama ya siffantu da dukkan kamala ta kyawawan dabi'u a mafi kamalar cika, domin ana ganinsa a matsayin mafi kamalar mutum ne. Imam Ridha (a.s) yana cewa: Jagora yana da alamomi da yawa: shi ne mafi ilimin… mafi tsoron Allah, mafi juriya, mafi jarumtaka, mafi kyauta, mafi ibadar mutane .
Sannan a matsayinsa na halifan Manzo kuma mai koyarwa da tarbiyyantar da mutane don haka ya zama dole ya riga kowa siffantuwa da umarnin Allah da kyawawan dabi'u. Imam Ali (a.s) yana cewa: Duk wanda ya tsaya matsayin jagoran mutane, dole ne ya fara da koyar da kansa kafin ya koyar da mutane, kuma ya tarbiyyatar da mutane ta hanyar dabi'unsa kafin tarbiyyatar da su da zancensa .

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)