Muassasar alhasanain (a.s)

Aure Mai Albarka Fatima Da Ali (A.S)

5 Ra'ayoyi 02.4 / 5

Aure Mai Albarka Fatima al-Zahra da Ali (a.s):

Auren Nana Fatima al-Zahra (a.s) ya ma ta so, to a nan yana da kayu ki san cewa Fatima al-Zahra tun tana karama har ma da ta zama matashiya ta kasance mace ce mai cike da annuri, wadda ta tattaro daraja, kyau da daukakar matsayi, wannan kuwa ba abin mamaki ba ne saboda ita 'ya ce ta mafi daukakan halitta kuma ta tashi ne a hannunsa karkashin kulawarsa baya ga kasantuwarta Ma'asumiya wacce kuma dukkanin Imaman shiriya za su fito daga tsatsonta. Don haka duk daga wancan lokacin hankula suka fara komawa gare ta, wasu daga cikin sahabbai sun fara tunanin neman aurenta daga wajen mahaifinta don su samu wannan daukakar da kuma nasaba ta hanyar samun dangantaka da babanta. Wanda dai ya fara zuwa neman auren ta shi ne halifa Abubakar, sannan sai Umar bin Khaddab, wasunsu kuma suka biyo baya. Sai dai Manzo (s.a.w.a) ya ki amincewa da wannan bukata ta su yana cewa: "Hukunci bai sauko ba tukuna"wato wahayi daga wajen Allah bai sauko masa dangane da batun auren Fatiman ba wanda hakan yana nuni da irin girman matsayin da take da shi da kuma irin muhimmancin da auren nata yake da shi. Daga nan sai Ali ya yi tunanin neman auren Fatima, don haka sai ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya kuma yafa mayafinsa ya yi nafila raka'a biyu, ya nufi wajen Annabi (s.a.w.a) a lokacin yana dakin Ummu Salama ne kuwa. Ya yi sallama, Manzo ya amsa masa, sai Imam ya zauna a gaban Manzo ya dukar da kai kasa; ganin haka sai Manzo ya ce masa: "Ya Ali, Ka zo da wata bukata ce?" sai Imam ya ce: "Na'am, na zo neman auren 'yarka Fatima ne; ko za ka aurar min da ita Ya Manzon Allah?" Sai Ummu Salama ta ce: "sai na ga fuskar Manzon Allah ta cika da annuri na farin ciki da murna, sannan ya kalli Ali ya yi masa murmushi. Daga nan sai Manzo (s.a.w.a) ya shiga wajen Fatima ya ce mata: "Ali bin Abi Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa a Musulunci ne, ya zo yana zance a kan al'amarinki (wato yana neman auren ki). Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa kuma wanda Ya fi so daga cikinsu. To me kike gani?" Sai ta yi shiru. Sai Manzo (s.a.w.a) ya fita yana cewa: "Allahu Akbar! Shirunta yardarta ne". Sannan ya cewa Imam Ali (a.s.): "Ya Ali, shin kana da wani abu da zan daura maka aure da shi (sadaki)?". Sai Imam Ali (a.s.) ya ce: "Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin). Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: "Amma takobinka kana da bukatarsa, za ka yi yaki da shi a tafarkin Allah kuma ka kashe makiya Allah da shi. Rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi, kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka. Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka". Sai Imam Ali (a.s.) ya je ya sayarwa Usman bin Affan da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzo. Daga nan Manzon Allah (s.a.w.a) ya sanar da Musulmi zancen auren, ya kuma cewa Ali (a.s.): "Allah Ya hore ni da in aurar maka Fatima a bisa nauyin miskali dari hudu na azurfa in ka yarda da haka". Sai Imam ya amsa da cewa ya yarda, don haka sai Annabi ya yi masu addu'a da cewa: "Allah Ya hada kanku, kuma Ya ba ku sa'a, Ya kuma albarkace ku, Ya fitar da tsarkaka masu yawa daga gare ku". Anas bin Malik Ya kasance yana cewa: "Hakika kuwa Allah Ya fitar da tsarkaka da yawa daga gare ku". To Malama Hajara wannan shi ne takaitaccen bayani kan yadda aure Nana Fatima (a.s) da Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya taso da kuma yadda aka shirya shi
To idan kuma muka koma ga bangare na biyu kan yadda aka gudanar da auren, wato watakila yadda aka yi da sadakin da kuma yadda aka gudanar da buki, to a nan muna iya cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya aurar da Fatima da sadaki madaidaici ne inda ya saya mata kayayyakin da suka yi daidai da wannan sadaki, don zamuna masu zuwa su ga cewa abin duniya fa ba kome ba ne a wajen mutuntaka da daukakar kamala. Manzo (s.a.w.a) ya karbi madaidaicin sadakin daga Ali bin Abi Dalib (a.s.), sai ya dauki nauyin shirya 'yarsa da tanajin kayan gidanta wanda ya kunshi 'yan kayayyaki kadan amma cikin daraja da daukaka. Sai ya aiki wasu Sahabbansa kasuwa don sayo mata (Fatima) abubuwan da sabon gidanta ke bukata, da suka kunshi shinfidu da lullubi da sauran bukatun gida da kayan girki tare da wasu 'yan suturu da turare(4) . Bayan wata daya (da daura aure), sai Manzo (s.a.w.a) ya fahimci bukatar Ali (a.s.) na tarewar Fatima a sabon gidanta, don haka sai ya amsa wannan bukata. Sai himmatuwa da al'amarin Fatima (a.s.) ya karu a wajen Manzo (s.a.w.a), don ya musanya mata fakuwar mahifiyar nan na ta mai tausayi (wato Khadija), a wannan sha'ani da uwa take da matukar muhimmanci, kowa dai ya san irin matsayin da uwa take da shi a wajen bukin 'yarta da kuma rawar da take takawa a lokacin aure. To amma abin bakin cikin shi ne cewa a wancan lokacin Fatima ba ta da mahaifiyarta tare da ita saboda Allah ya yi mata rasuwa. Don haka sai ya sa hannu da kansa a al'amarin sa wa Fatima lalle. Ya nemi matansa da su shirya ta kamar yadda ake shirya 'yan mata a daren tarewa. Bayan nan sai Manzo ya hada walima da sanar da aure, Muhajirai da Ansarawa kuma suka halarci wannan taro na farin ciki da ba shi da tamka cikin tarihin Musulunci. Wannan bai zama wani sabon abu ba, himmatuwar Manzo da al'amarin Fatima bai kasance don kusanci da dangantakarsa da Ali da Fatima ba; a'a baya ga hakan, har ila yau kuma wannan lamarin ya samo asali ne saboda fadadar reshen Annabci da bishiyar Imamanci ta wannan iyali mai albarka. Saboda Allah Ya so aurar da zababbiyar mace kuma tsokar Annabi, Fatima, ga zababben mijinta, Ali (a.s). Don kuwa Ali (a.s.) ne wanda Manzo (s.a.w.a) dangane da shi yake cewa: "Ashe ba ka yarda ka zama a wajena irin yadda Haruna ya kasance a wajen Musa ba, in ban da cewa kawai babu Annabi a bayana ba". Fatima kuwa ita ce wannan da Manzo (s.a.w.a) dangane da ita ya ke cewa: "Ashe ba ki yarda ki zama shugabar matan duniya ba". Don haka su biyun sun kasance wadanda Manzo (s.a.w.a) ya fi so daga mutane kuma wadanda suka fi kusa da shi. An taba tambayar uwar muminai A'isha kan mutumin da Manzon (s.a.w.a) ya fi so, sai ta amsa da cewa: "Fatima". Sai aka ce mata: daga maza fa? Sai ta ce: "mijinta. Haka Allah Ya so zuriyyar ManzonSa (s.a.w.a) ta fadada ta hanyar Ali da Fatima (a.s.), ya zama sun sami Hasan da Husaini, shuwagabannin samarin gidan aljanna, da sauran tsarkakan Imamai masu shiryar da wannan al'umma. Wannan babban sirri ne yasa auren Fatima (a.s.) ya kasance bisa horon Allah Madaukaki, Manzo (s.a.w.a) bai gabatar da shi ba kafin umarnin Ubangijin, bai yi wani abu ba har sai da hukuncin Allah ya sauko, kamar yadda ya tabbatar da haka da kansa. Fatima ta tare a dan karamin gidan mijinta Ali bin Abi Dalib (a.s.) alhali tana mai farin ciki da amincewa da shi. Ta rayu tare da mijinta cikin kwanciyar hankali da farin ciki, ko da yaushe tana cikin sakin fuska. Ita ce matar Ali gwarzon Musulunci, ma'abucin sadaukar da kai kuma mai dauke da tutar jihadi da nasara. Fatima (a.s.) ta kasance ita ma daidai da haka. Ta kasance tare da Ali kamar yadda mahaifiyarta Khadija ta kasance tare da Manzo (s.a.w.a), tana gamayya da shi ciki jihadinsa, tana kuma hakuri da wahalhalun rayuwa, don haka sai ta aiwatar da aikinta daidai da yadda Allah Madaukaki Ya zabe ta don shi. Ali da Fatima (a.s) sun rayu a inuwar Manzo (s.a.w.a) kuma karkashin kulawarsa. Manzo ya ba Fatima abin da bai ba kowa ba bayan aurenta, ta yadda tsananin lurarsa da ta'allakar zuciyarsa da ita har ya kai in zai yi tafiya ko zai je yaki Fatima ce karshen wadda ke sallama da shi. Kuma idan ya dawo daga tafiyarsa ko yakinsa Fatima ce farkon wadda ya ke fara haduwa da ita daga cikin mutane. Fatima (a.s.) ta rayu a gidanta a matsayin uwar-gida; tana lura da al'amuran gidanta kuma tana aiwatar da bukatun gidan bisa dogaro da kokarinta. Bata kasance tana da masu hidima ko bayi ko 'yan aiki ba. Duk rayuwarta ta kasnce jihadi ne da kokari. Kamar yadda kuma ta kasance tana gudanar da dukkanin ayyuka na gida da suka hada da nika da yin burodi da sauran ayyuka na gida. Allah ya albarkaci wannan aure na Fatima da Ali da Hasan da Husaini, da Zainab al-Kubrah, gwarzuwar Karbala, kuma abokiyar tarayyar Husaini (a.s.) a jihadi da gwarzantakarsa, sai kuma Zainab al-Sugrah, wacce aka fi sani da Ummu Kulthum. 

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

sadiya:ummulhassanain
2015-05-31 15:59:24

abin da ya kamata iyaye sudinga sa 'ya'yan agaba suna fadakar dasu rayuwar aure da yanayin xaman dan allah adinga yiwa iyaye nasiha sudena jin kun yar 'ya'ya alokacin aurensu.

*
*

Muassasar alhasanain (a.s)