Muassasar alhasanain (a.s)

Waki’ar Ashura

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Jawabin Sheikh Zakzaky a wajen rufe muzaharar

Ashura a Zaria [1428].


Waki’ar Ashura yunkuri ne na karakar da gidan Manzon Allah (S)

Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana.


code:100046

 

2008/5/5  23:59

WAKI’AR ASHURA YUNKURI NE NA KAU DA GIDAN MANZON ALLAH (S)

Zan fara da cewa, “A’azamallahu ujurana bi musabina bil Husain Alaihis Salam. Waja’alana wa iyyakum mina dalibina bitharihi ma’a waliyyihi Imam Mahdi min Ali Muhammad alaihimus salam.” Wannan rana ce ta juyayi, rana ce ta bakin ciki, na musiba da ta auka wa wannan al’umma, wanda kuma sakamakon wannan musiba har yanzu al’umma tana fama da shi, tana fama da wannan sakamako, kuma ba za ta gushe ba a cikin wannan hali har ya zuwa lokacin da za a sami ‘Faraj’. Musiba wadda ta auka wa wannnan al’umma a sakamakon yunkuri na ganin cewa an karakar da gidan Manzon Allah (S), domin a tabbatar da cewa addinin wannan Manzo ya kawo karshe. Wannan a sarari yake a bayanan da Yazidu ya yi a yayin da aka kai masa kan Husaini (AS).

Ya ce ba wani wahayin da ya sauka, ba wani Alkur’anin da aka saukar, Banu Hashim sun rudi kansu ne kawai. A iyakar fahimtarsa, kokawa ce ta gidaje, tsakanin Hashimawa da Umayyawa, yau kuma a wurinsa Umayyawa sun yi nasara. Hashimawa, a fahimtarsa sun yi nasara ne ta hanyar jan ra’ayin mutane da sunan cewa wai akwai Annabi a cikinsu wanda yake jin magana daga sama. To yau ya tabbatar da cewa babu wannan, iko ne, mulki ne, kuma yau Banu Umayya sun kwace. Sai dai tilas, tilas, wadda ta tilasta wa Ubansa ya yi amfani da Mususlunci, ya tilasta shi, shi ma ya yi amfani da Musulunci. Don bai isa a ran nan ya ce tunda yana da akidar ba wahayin da ya sauka, a daina salla, a daina azumi, a dai karanta Alkur’ani, a daina kiran salla, a daina addini ba. Bai isa kuma ya dawo da Lata da Uzza da Hubbal ya ce sune iyayengiji ba, wadanda kakanninsa suka gada.

Tilas ya zama don masalahar ikonsa ya ci gaba da amfani da sunan wannan addini kamar yadda Ubansa ya yi. Wanda ya so ya cire kalmar “ashhadu anna Muhammadur Rasulullah” daga kiran salla, a yayin da wani na kusa da shi ya ce da shi, lokaci ya yi da ya kamata ka sa da zumunci da Banu Hashim, domin yau ba ka wani tsoro daga wajensu, mulki ya tabbata a hannunka, kuma su yanzu sun zama talakawa, mabiya, saboda haka kamata ya yi ka san da zumuncin da ke tsakaninku.”

Ya ce da shi “Ashe kai ba ka tunani. Wane daukaka ya wuce wannan, ya zama kullu yaumin sai an ce ‘Ashhadu anna Muhammadur Rasulullah’?” Har ya ce, a kalmarsa, “abaitu illa dafanan, dafanan!” Ma’ana “Na ki, sai na bizne, na bizne.” Wato sai ya bizne “Muhammadur Rasulullah” din nan.

Na’am ya kawo sauye-sauye a kiran salla, kamar yadda ya kawo sauye-sauye a ita sallar kanta. Kuma na’am an kawo ’yan canje-canje a wadansu abubuwa cikin addinin, amma dai Allah ya ki a canza kalmar ‘la’ilaha illallah Muhammadur Rasulullah.’

Ya zama tun daga wannan lokaci, wannan musiba ta dubi wannan al’umma ana ta jarabtar ta daga makiyayi, ‘habis’ zuwa ‘ahbas.’ Yazidu ne ko wadanda suka biyo bayan Yazidu. Kullu yaumin, makiyayi bayan makiyayi, wanda abin da ya dame shi shi ne sarauta, ba addinin Musulunci ba.

Har ta kai ma wannan al’umma, kafirai wadanda ba su ko amfani da sunan addinin suka yi galaba a kanta, suka tsaga ta yadda ransu ya ga dama ya zuwa kasa-kasa. Har ta kai ma sun soka akidar ’yan kasanci a wannan al’umma. Yanzu al’ummar ta kasu kashi-kashi. Mutane kuma suna ganin sunansu a matsayin ’yan kasashe daban-daban, kowa yana alfahari da kasarsa. Ya kasance kuma wadannnan kasashe takensu ra’ayin shi ne na ra’ayin ’yan kasanci da tunkaho da tarihi da asalin kakanni.

YANZU BA A KIRAN MUSLMI MUSULMI, SAI DAI A KIRA SU DA WASU SUNANNAKI

Har ta kai ma kafircin duniya, duk da shi akidarsa ce ’yan kasancin, amma shi ya iya hada kai a ’yan kasance. Kasashensu na haduwa a kan yarjejeniyoyi daban-daban wanda yake hada su. Alal misali, duk da bambance-bambancen da ke tsakanin kasashen kafiran duniya, sun yi ittifaki a kan ba za su taba lamuncewa addinin Muslunci ya dawo ya sake iko da duniya ba. Domin kuwa komai lalacewar al’ummar musulmi, ikonsu a kansu, su a wurinsu kaskanci ne.

Kuma yanzu ma sun yi ittifaki cewa shi wannan addini abin a kawar da shi ne. Yanzu kafircin duniya ya tashi haikan ya tunkari wannan al’umma da fada da ita ta kowane janibi. Abin takaici, wannan al’umma ta rasa makiyayi, ta zame tamkar yadda makiyi ke son ya gan ta. Yanzu makiyi ya daina kiran ta musulma ya sa mata sunannaki. Kuma ga dukkan alamu tana son wadannan sunannakin da yake kiranta. Yanzu makiyi ya rarraba kawunan musulmi har ma ba ya kiran su musulmi.

Kamar jiya ina sauraron wata lacca da wani tsohon Gwamnan Newyork yake yi dangane da al’amarin Irak. Sam a cikin al’amarin nasa bai ma ce musulmi ba. Sai yana cewa ‘extremist Shi’a da extremist Sunna.’ Har ya gama maganarsa, sunan ’yan Iraki, Shi’a da Sunna da Kurdawa, bai kira su musulmi ba.

Abin takaici, irin wadannan sunannaki da makiya suke kiran al’umma da ita, su kuma al’ummar suna kiran kanta da irin wadannan sunannakin. Yanzu kadan ne za ka sami musulmi ka ce masa wanene kai? Ya ce maka shi musulmi ne. Sai dai ya ce maka shi dan kaza ne. Har dai mu nan, wanda ’yan kazanci ya yi mana katutu, har mun fara kallon kawunanmu a matsayin yadda makiyanmu ke bukatar su ganmu, kowanne sunansa dan kaza. Har masallatanmu sun sami ‘signbord,’ ko da ba a zana ba dara-dara. Masallaci wanda ake salla.

Na’am na yarda cewa musulmi suna da bambance-bambance, tabbas haka ne. Saboda ana iya samun bambance-bambancen fahimta, amma akwai wani abu guda, Musulunci sako ne na Allah (T) ta hanyar Manzonsa ya zuwa dukkanin mutane. Kuma shi wannan addinin na Musulunci shi ne muka amsa duk cikarmu, sai dai kowa yana aikata da daidai gwargwadon abin da ya zo masa ne. Ban ce babu bambanci ba. Saboda haka akwai makarantu daban-daban. Galiba, in ana magana sai a ce wannan shi ne ra’ayin makaranta kaza, wannan shi ne ra’ayin makaranta kaza, wannan shi ne ra’ayin makaranta kaza. Amma ba a taba ganin mutane a matsayin su ’yan kaza da ’yan kaza da ’yan kaza bane sai a wannan lokaci. Wanda yake hattaa amawa suna ganin su ma ’yan kaza ne. Da kuwa ana ganin wannan ra’ayi ne na karatu kawai. Ra’ayi ne da akan same shi a littattafai, ko a tsakanin tattaunawa tsakanin masu ilimi, wanda yake wannan yana da ra’ayi iri kaza, wannan yana da ra’ayi irin kaza. Amma yanzu an wayi gari, da Malamai da Amawan gari duk cikansu suna ganin su kungiyoyi ne. Wannan tabbas kamar haka makiyanmu suke so su gan mu, kamar haka kuma muka mai da kawunanmu.

Wannan kuwa ba wani abu bane illa ita wannan musiba da ta auku tun waki’ar Ashura, wadda ta nemi ta ga mutane a matsayin ’yan gida-gida. Ta ga wanan al’amari a matsayin gidan sarauta. Ta gan shi da mahangar kabila ba mahangar addinin Musuluci ba. Wanda kuma ya yi daidai da akidar kafiran duniya, wanda su mahangarsu ba addini bane. Mahangarsu maslahar rayuwarsu ta duniya kawai. Saboda haka za su iya fitowa da fuska ta kabila ko ta jinsi, amma ba ka ji shi da fuska ta addini ba, hatta walau ko suna da’awar wani addini.

Wannan muna iya cewa asasin wannan abin da muka fada a ciki a wannan lokaci namu, ya yi wo asali ne tun daga lokacin wannan waki’a. Na’am wani yana iya cewa wakia’r a lokacin ne aka fare ta? Sai mu ce lallai kam ba a lokacin bane. Ita ma kafin waki’a din akwai abin da ya fara farowa, ya dinga ruruwa, ya dinga ruruwa, ya dinga ruruwa ya kai ga waki’ar Ashura. Bayan waki’ar Ashura kuma, sakamakonsa ya dinga biyo bayan har ya zuwa yau din nan.

Har yaushe ne za mu ci gaba a wannan hali? Ba za mu gane da cewa Musulunci sako ne na Allah (T) ba ya zuwa dukkannin mutane. Kuma mu gane da cewa duk wanda ya shaida da cewa ‘la’ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah,’ aikinsa ne ya isar da wannan sakon ya zuwa ga sauran al’umma, wanda Allah (T) ya dauki wannan al’umma ya ba ta matsayi ya ce mata ‘khairu ummatin ukhrijat linnas.’ Mafificiyar al’ummar da aka fitar a cikin mutane.

Na’am ba sai an gaya maka ba, ta fi kafiran duniya? Sai mu ce maka ai wannan ba shi ne ma ake nufi ba, ya wuce nan. Abin da ake nufi, shi ne ta fi dukkannnin al’ummun Annabawan da suka gabata. Wato al’umma ce wadda take ta fi al’ummar Nuhu da Ibraheemu da Musa da Isah da sauran Annabawan da Allah ya aiko kafin wannan Manzo (S). Ita ce ‘hairu ummatan ukhrijat linnasi.’ Wadda aka dora mata aikin ‘amru bil ma’aruf’ da ‘nahyi anil munkar’ da imani da Allah. Saboda su wannan al’umma yana cewa ‘kuntum khaira ummatin ukhrijat linnasi,’ sai ya ce ‘ta’amiruna bil ma’arufi watanhauna anil munkari wa tu’uminuna billah.’ Sabanin sauran al’ummu.

Sannan kuma ita wannan al’umma da Allah ya ce ita ce ‘ummatan wasada,’ al’umma zababba, madaidaiciya, mafificiya. ‘Wa kazalika ja’alnakum ummatan wasadan li takunu shuhada’a alannasi.’ Haka nan muka sanya ta ta zama al’umma mafificiya. Ana ce mata ‘wasadan’ da cewa ana nufin zababba ce. Zababbiyar al’umma don ku zama kune shaidu a kan sauran al’ummu, a kan mutane duk gaba daya. Ma’ana za ku zama shaida gare su gobe kiyama kan kun isar masu da sako amma ba su bi ba. Wannan kuma yana nufin kenan za ku zama shaida gare su in sun bi sakon. In kun sanar da su wannan sako na wannan Manzo sun karba. ‘Wa yakunu shahidan alaikum.’ Shi kuma Manzo ya kasance shaida a kanku in ba ku yi wannan aikin ba. Cewa ya isar maku da sako, sako ya zo gare ku, kune ba ku isar da sakon ya zuwa sauran al’ummu ba.

Wannan al’umma wadda ya kamata ta zama ita ce ke haskaka sauran duniya, take jagorancin duniya, sai ta koma yanzu ita ce ake ganin wallenta, ita ake tattakawa, ita ake kai mata hare-hare, ita ake mutsuttsukawa, ita ake debe dukiyarta, ita ake talauta mutanenta, ita ake zuba ma mutanenta cututtuka. Kafiran duniya su suke kyasawa, suke abin da ransu ya ga dama ba su jin tsoron wani abu daga wannan al’umma, ba su ganin wani alheri daga wannan al’umma ballantana su yi tunanin cewa wannan al’umma ita ce za ta shiryar da su. Saboda menene muka fada wannan hali? Saboda al’amari ba yana hannun ma’abotansa bane.

DA A CE WANNAN AL’UMMA TA SAMI MAKIYAYI KAMAR IMAM HUSAINI (AS)

Mu kaddara da a ce tun farkon al’amarin nan, al’amura na hannun ma’abotansa ne, da ba a jarabci wannan al’umma da makiyayi kamar Yazidu ba. Fasiki, Fajiri, mashayin giya, mai wasa da karnuka, girman dangin nono na kiristoci, wanda bai san komai ba daga ilimomin addini ko dabi’u na addini. Shi ne aka ce masa wai Sarkin musulmi.

Mu kaddara misali da a ce a wannan lokacin wannan al’umma ta sami makiyayi kamar Imam Husaini (AS), ba ta gushe ba kuma tana samun makiyaya, Imami bayan Imami ya zuwa wakilan A’imma. Da a yau mutanen China da ba su yi addinin Buda ba, da yau ba addinin Hindu. Da yau ‘Kara’ din Amerika da Turai da duk musulmi ne. Ko da za a sami rikici, sai dai a sami rikicin cikin gida tsakanin musulmi ya-su-ya-su, amma dai ba kafirci ya yi izza a kan addinin Musulunci ba.

Amma kasantuwar al’amari ba yana hannun ma’abotansa bane, sai ya zama duk inda Musulunci ya kafu, al’ummar musulmi suka kafu, sai shimfida mulki da shan shagali. Tana iya yiwuwa wani lokaci idan aka kira al’umma gaba daya, daidai gwargwadon fahimtar mutum da ita al’ummar gaba daya, yake iya ganewa. Amma na san idan na tsuke lamarin ya zuwa nan inda muke, kila mutane su gane nan da nan. Kila mutane za su fi gane in na tsuke al’amarin na dawo da shi inda muke nan yanzu.

Sanin kowa ne, babu wai, cewa yanzu mun sami kanmu a cikin wata kasa, kodayake ba mu muka yi kasar ba, ba mu muka shata kan iyakarta ba, ba mu muka sa mata suna ba, wadda ake ce mata wai Nijeriya. Baturen mulkin-mallaka ne ya zo ya ya yi dala da gawarwakin kakanninmu kafin ya ima kasar. Ya yi mana hadaka, ya tsaga mu yadda ya ga dama, ya yi kan iyaka yadda ya ga dama. Ya raba mu da ’yan uwanmu na Arewacin kasar nan ya ce masu wai Nijar, su kuma su nan karkashin mulkin Faransa suke.

Ya raba mu da ’yan uwanmu na Gabashin kasar nan ya ce sunansu wai Kamaru. Ya raba mu da ’yan uwanmu na Yammacin kasar nan ya ce sunansu wai Dahomey (Benin) da su Burkina Fasso. Ya tsattsaga yadda ransa ya ga dama, ya yi kan iyaka. Ya hada mu da ’yan kudancin kasar nan wadanda suka yi iyaka da ruwa ya ce sunanmu wai Nijeriya. Ya ba mu harshenmu na kasa, wai Ingilishi, wai mu nan Ingilishi ne harshenmu.

Ya ba mu ilimi na rubutu na ‘as’habul shimali,’ wanda ake yi daga hagu zuwa dama. Kodayake rubutu ne, ana iya rubutu ko sama ko kasa in an ga dama. Amma dai akalla dai ba gadon ubanmu bane, alhali muna da namu gadon. Muna da rubutu gadon iyayenmu da kakanninmu, wanda yake shi ya dace da mu, shi ne kuma ya yi daidai da addininmu.

Ya ba mu akida na ’yan kasanci, ya ba mu wata gona da ake noma a yi girbi a kai masa kayan. Mune noman gyada, mune noman auduga, mune na koko, mune na kwaran mai, shi kuwa yake cin gajiya. A kwashi gyadarmu a kai masa ya tatse man, ya yi kulikuli da tunkuza din, ya turo mana mu saya, biskit kenan. Mu ci yana rakas-rakas mu ce mun ci gaba.

Ya kuma gano kwasar arzikinmu, wanda Allah (T) ya halitta a karkashin kafafunmu, ya tone zinariya kakakaf ya kwashe. Ya tone kuza. Yanzu ga shi yana tonon mai. Mu kuwa ya bar mu da tinkahon mu ’yan kasa ne, ya bar mu da rigimar bangaranci, Arewa da Kudu. Domin wannan maslaharsa ne. Matukar za mu yi ja-in-ja, tsakanin wannan dan Arewa ne, wannan dan kudu ne, to ya yi masa daidai. A yi ta rigimar Kudu da Arewa, shi kuwa ya yi ta dibar arziki. Da zai ga rijiyoyin mai sun shiga hadari, da zai zo da kansa saboda wannan ne ba ya bukata.

AN DAUKI ADDININ MUSULUNCI A MATSAYIN ABU MAI HADARI

To, sanin kowa ne a wannan wuri da aka shata aka ce mata wai Nijeriya, ko nawa ne ma mutanen kasar, don ba a san mutanen kasar ko su nawa bane. Ko ba komai yawansu ba ma yana da muhimmanci bane, saboda yawansu yawan kawai ne. Ana cewa yawansu mai yiwuwa ya kai miliyan 150, mai yiwuwa ma ya wuce haka nan. Wasu su ce 120. Duk dai yadda suka yanka. Amma dai wani abu sananne shi ne, ko ma miliyan nawa ne yawan mujtanen Nijeriya, in ka kasa su kashi 100, to kashi 66 zuwa 70 musulmi ne, ka ki ko ka so! Saboda haka in ma miliyan 100 ne ake batu, akwai mutum miliyan 66 zuwa 70 kenan musulmi. In mutum miliyan 140 ne, ka ga ana batun wajen miliyan 100 musulmi ne. In ana batun miliyan 150 ne zuwa sama, ana batun sama da miliyan 100 kenan, ka ga duk musulmi ne.

Amma a yau an wayi gari shi Muslunci sam ba a san da zamansa ba a nizamin kasar. Kai ma ba a san da zaman musulmi ba. Ba a san da zaman addininsa ba, ba a san da zamansa ba shi ma. Abin da aka sani kawai shi ne nizami wanda ba ruwansa da addini, ko kuma da ruwansa da addinin, amma ba ruwansa da addinin Musulunci. Yana iya zama kowane addini, amma banda Musulunci.

Kuma har yanzu an dauka duk wani abin da ya shafi addinin Musulunci hadari ne ga kasa. Babban aikin jami’an tsaro na kasa, SSS, shi ne su tabbatar da cewa wani abu na addinin Musulunci bai taso ba. Domin shi addinin shi ne hadari. Addinin Musulunci shi ne hadari. Amma in wani abu ne lallai ana iya yi, ba komai.

Hatta a al’amarin soja ne ko ’yan sanda ko menene, addinin Musulunci shi ne hadari gare su, amma kowane addni yana iya zama daidai, ko da na gargajiya ne. Abu daya ne ake ganin cewa shi wannan kada a yarda ya dago, domin shi hadari ne ga kasantuwar kasar nan, shi ne addinin Musulunci.

Wannan fadi kara, duk wanda yake Gwamna ya riga ya san wannan. Yana zaune ne a matsayin Gwamna ya tabbatar da cewa addinin Musulunci bai dago ba, aikinsa kenan. Ya gada ne dama tun daga gadon Lugard, har yanzu kuma a kansa yake, ko da kuwa shi Alhaji waye. Kuma kullum za a kawo masa ‘Report na Security’ game da ga Musulunci nan yana yunkuri.

Kuma a kan shi ake nada Sarakunan Gargajiya. Hatta ma takardar nadin, an ce aikinsu ne su kawo rahoton duk wani wanda ke neman ya tayar da hankali, tun a lokacin Turawa na mulki. Ma’ana duk wani wanda yake wa’azin a koma ma ga addinin Musulunci. Har ma tun ’yan mulkin-mallaka suna tashensu, gabar sun kama kasa, an sami wani Malami mai wa’azi, wanda aka ce ma Sarkin musulmi ya tsine masa yana neman ya kawo tashin hankali.

Don rahoto ya je Ingila, ga wani can, yana neman ya kawo tashin hankali, yana cewa kar a yarda da mulkin bature, a koma ga addinin Musulunci. To sai da Sarkin Musulmi ma ta kai ma ya tsine masa. Ya ma tsine ma ’yan garin gaba daya. Aka je aka fatattake su. Kuma Sarkin musulmi ya tsine wa duk wanda ya zauna a garin, ko ya noma kasar garin. A kan shi har yanzu duk Sarakunan nan masu kahon tsumma, suke aiki. Kada a yarda addinin Musulunci ya daukaka. Wai yanzu a wannan kasa, addinin Musulunci shi ne ake kokarin a tabbatar lallai kar ya sake dawowa.

MUSULMI SUN LALACE A KASAR NAN

Mun ma fahimci wannan a yayin da muke hankoron yin fim dangane da tarihin Shehu Usmanu Dan Fodio, nan da nan magana ta kai Amerika cewa, akwai babban hadari na dagowa. Wadannan mutanen in suka yi wannan fim din za su dawo da tarihin Dan Fodio kamar yadda yake, alhali sun yi aiki iya iyawarsu sun mantar da mutane Shehu, an nuna shi a matsayin Sarki ne Bafillatani. Su kuwa wadannan za su yi kokarin su nuna shi a matsayin addini ne. Saboda haka kar a yarda a yi wannan.

Ka ga wato kenan yanzu an kafa kasa a kan cewa ba za a taba yarda a ce addinin Musulunci shi ne ya dawo ya yi iko ba. Saboda haka ka ga ga musulmi sama da miliyan 70, ko ma sama da miliyan 100, wallahu a’alam, amma ga su nan kara zube kawai, sai kada su ake yi. Zilla ta kai masu har ba sa ganin wani ya cancanci ya jagorance su sai wanda yake ba musulmi ba. Sun kasa ko da dandamali ma su yi su ce masa wannan dandamalin musulmi ne. Ko sun yi sun kira shi na musulmi, suna jiran sai sun nemi shugabanninsu na gaba da su, wadanda suke ba musulmi ba sun ba da amincewarsu.

Don haka ne ma aka yi Kwamitin tara kudi don a gyara masallacin Abuja, aka sa kirista ne Shugaban Kwamiti din. Aka yi wani dandamali na dattawan Arewa, aka ce kirista ne Shugaba. Ya gama ‘term’ dinsa shekara 10 aka sake zabe, aka sake saben kirista. Zilla ta kai masu ba su ganin tana iya yiwuwa a ce musulmi yana da wani izza. Wannan ba kaskanci ne da wulakanci ba?

To da menene kuke tinkaho yanzu? In dai kuna tinkaho da cewa ku Hausawa ne, Fulani, sai mu ce maku lallai a matsayinku na Hausawa da Fulani ba ku da bambaanci da Igbo da Yoruba da Tiv da Idoma da Etsekiri da sauransu, don duk wadannan mutane ne. Amma kun fi su a matsayin ku musulmi ne. Saboda a matsayinku ku musulmi kun zama ‘khairi ummatin ukhrijat linnas.’ Kun zama ‘ummatan wasadan.’ Kune shaidu a kan sauran wajen isar masu da sako, kuma suna da hakki a kanku.

AN MAISHE MU KARA ZUBE

Abin da nake kokarin in nuna a nan, shin ne ku lura, in ba ku iya gane na duniya da fadi gaba daya in na debo ta, na nuna yadda Amerika ke barnarta yadda ta ga dama a Iraki ne, a Afghanistan ne, barazanonin da take yi wa kasar Iran da Siriya ne, tursasa Palasdinawan da ake yi ne, ko Rasha yadda take mutsuttsuka Shishanawa (Ceceniyawa) yadda ranta ya ga dama, ko kuma yadda Indiya take mutsuttsuka Kashmirawa musulmi da sauransu da sauransu, in wannan ya yi maku nisa, dubi nan inda ake zaman kara zube, a wulakance. Yadda ake zaman talauci. Ni ban ga abin da ake nema ba a rayuwar. In kana so ka ji dadin rayuwa ne, ba jin dadin rayuwar.

Akwai wani lokaci za mu je Kano muka tsaya kan hanya, wasu mutane suka wuce, suka ce, “sannunku, sannunku.” Na kidaya su, sun kai su goma sha, za su je farautaa ne. Me ake samu afarauta? Gafiya da zomo! Har nake tunani, wadannan mutane wajen goma sha, in an sami gafiya, ya za a raba?

Yanzu ga samari nan majiya karfi sai tura baro na ruwa ko sayar da kati na salula, har da wadanda suka gama jami’a suna guje-guje ka sayi katinsu. Duk ana zaune kara zube. Sai acaba sai shan shalusho, shi ne akwai. An maishe mu kara zube kawai, ga mu nan rututu kawai ba mu da wani amfanin komai.

ALLAH YA DAUKAKA MU NE DA DARAJAR WANNAN ADDINI

A wannan lokaci kuma sai aka zo mana da wasu fitinoni iri-iri na rarraba, na cewa mu ’yan kaza ne da ’yan kaza ne. Za ka ga mutum da hankicinsa ya yi bakik saboda zukar shalushon shi, ni ba ina raina masa bane kan zukar shalushon, ina ganin cewa ba laifinsa bane, laifin al’umma ce don ita ta jefa shi a kan shan shalushon din. Don da yana da aikin yi yana samun rayuwa lafiya lau, ba yadda za a yi ya ce shi ba zai yi ba, shalusho zai sha. Tilas ta sa shi shan shalushon, ko ba komai ya dan huta. Tunda in ya manta da matsalarsa shi kenan.

Na ji ma ana hira da wani dan shalusho, ya ce wahala ce da yunwa. Yunwa ta dame su ba su da aikin yi. Ya ce to shi kenan in ya sami dan shalushonsa ya dan zuka ya je ya dan sami wani kango labe, sai ya gan shi a gida mai ‘Air conditioner,’ ya shiga zungureriyar mota kuma. Ya ce, to su nasu jin dadin kenan. Saboda an haramta masu su ji dadi.

Kuma ko ’yan farautar nan da ka gani, ko ’yan tauri, ba wanda yake so ya yi wannan, tilas ta sa shi. Ko dan wiwi, in da da abin kirki ba zai ce shi ba zai yi wannan ba, za shi ya je ya yi farauta ne ya kama gafiya. Ta kai ma duk gafiyoyin gari an kame su. Suka shiga cin kyanwa. Har ma ana ce mata zomo mai dogon bindi. Duk sun kwashe kyanwan gari. Har karnuka. In fata wannan jawabin da nake yi ba za a ji a kasashen waje ba, wannan na ’yan kasa ne.

Don ta kai ma ’yan uwa akwai wani lokaci da aka kai su kurkuku suka zauna tare da dan Limamin wani gari. Shi dan Liman din an kawo shi ne shi ma kurkukun saboda ana tuhumar sa da ya sace kare. Saboda akan mangare karen ma a cinye.

Dubi irn yadda aka talauta mutane aka maishe su ga su nan kawai kamar wasu dabbobi. Mutanen da ya kamata ya zama sune taurari da suke haskaka al’umma. Wanda su ya kamata su jagoranci al’umma, an maishe su ga su jahilai, matalauta. Kuma ko ma ka yi karatu an maishe ka zauna gari banza.

A lokaci guda aka kawo fitinar kai dan kaza ne, kai dan kaza ne, in dai za ka sami abin tabawa, ba shi kenan ba. Wannan me ya kawo wannan?

Ba mu sami daukaka a sanadiyyar mu ’yan bangare kaza ne ba, ko mun ’yan kaza ne ba. Allah ya daukake mu ne da darajar wannan addini. Kuma mu gane komawa ga wannan addini shi ne abin da yake mafita gare mu.

DA ZAMA KARKASHIN ZILLA GARA MUTUWA DA KARAMA

Fakam da yawa in mun hadu a daidai wannan lokaci muna magana ne dangane da abin da ya faru a Ashura da darussan da za mu iya koya a ciki. Darasin da Imam Husaini ya koyar da mu a Ashura, shi ne, da zama karkashin zilla,gara mutuwa da karama. Da zama karkashin wannan wulakanci da kaskanci da talauci da rashin daraja da rashin mutunci, wallahi gara mutuwada karama!

Kuma abin da ya sa muka fada wanna hali, kuma muke zama a ciki sai dada karuwa kuma yake yi, saboda kowannenmu ya tsaya kyam a kan cewa wannan kan da ke birbishin wuyarsa sai ya zauna a wuyar. Da kowa zai ce ga shi a sare, ko a yi addini ko a sare kan, wallahi da addini ya tabbata! Kuma da duk za a kawo kawunan nan a tsaya kyam, sai dai addini ko a mutu, to illa iyaka a sare ’yan dubbai; ko miliyan daya ba za a sare ba cikin sama da miliyan saba’in din nan. Da duk cikarmu za mu ce ga kawunanmu a sare, ko a yi addini ko a sare kan, wallahi kar ku dauka duk za a sare kan ne. Illa iyaka in an sare ’yan dubbai, to addinin zai tabbata. Amma da yake kowannenmu yana son kansa a birbishin wuya, ya shafa ya ji yana nan ba a sare masa ba, sai ya dauki kaskanci da wulakanci ya zauna a ciki.

Kuma kan nan da ke birbishin wuya ba ya dinga zama kenan ba. Ko ya hau jirgin sama ya fado, ko ya yi hadarin mota, da ma ba tayoyi, ko ya sha gurbataccen mai, ko ya fada rami. Domin duk duniya ba inda ake samu kwalta da rami sai Nijeriya. Ko ya yi rashin lafiya a kai shi asibiti a ce ana neman sai an kawo Naira dubu hamsin a yi masa ‘Operation,’ ya mutu don ba shi da dubu hamsin din. Akwai wadanda suka mutu saboda Naira dubu uku. Za a yi masu ‘operation’ ba su da dubu uku, suka mutu. Kullum ka ji sanarwa a rediyo, wani ba shi da lafiya ana neman dubu biyar a yi masa aiki. Wanda yake wadannan da yake lazim, dole ne a yi masa kyauta, ballantana mace-macen yara, ga su nan, mafi yawa kuma rashin abinci ne.

To ko da ma ka ki ka ba d a kanka din, kar ka dauka kan zai zauna yana nan a wuya, mutuwa kam dole. Kuma mutuwar zubargada. Ga shi nan ana ta ta yi, mace-mace iri-iri, masifu kala-kala. In ciwo ne ya same ka, ba magani. Hadari kuwa, dama hanyoyinmu tarko ne na mutuwa. Motocin da muke shiga galibansu duk tarkunan mutuwa ne. daga mai sudadden taya, wanda yake kodawane lokaci tayar na iya fashewa. A haka muke tafiya. (Kaset din namu ya dan sami matsala a nan.)

Da fashi muna jin labarinsa ne ana yi a Amerika. Ana nan aka ce ya zo Legas muna ta mamaki, Legos?! Aka ce sai a nuna maka bindiga. Ana nan yanzu ya bazu ko’ina. Yanzu ko a kauyukanmu ana yin fashi, kuma fashi mummuna. Tunda za su ga mutum yana zuwa ne da babur su labe, in ya zo a sara masa adda. Har ma ya ga wanda yake kashe shi. Ya ce wane kai ne kake sara na? Ya ce ai ba za ka ba da labari ba. Ya kashe shi ya dauke babur din.

                                                                   

                                                                           GARA A MUTU DA IZZA

 

                                             

Saboda haka in dai kai ne na birbishin wuya kake so ya zauna daram, to ka tabbatar da wani abu guda, ba fa zai zaunan ba. In ma ka yarda ka zauna bisa kaskanci da wulakanci, to za ka mutu da kaskanci da wulakancin.

To, in haka nan ne mutuwa ta zama dole, ba gara a mutu da izza ba. Wannan shi ne darasin Ashura. Mu tsaya kyam a tafarkin Allah ko da za a kashe mu ne. Da wannan Imam Husaini ya yi juyi, juyin-juya-hali, wanda ya koyar da al’umma har ya zuwa ranar karshe cewa haka ake yi. Akan tsaya kyam ne a kan gaskiya tare da ma’abotansa. Haka kuma su mutanen da suka yadda suka yi shahada tare da Imam Husaini, abin da suka nuna kenan. Ana kasancewa tare da ma’abota gaskiya ne a duk inda suke.

Wannan umurni ne na Allah “Ya ayyuhallazina amanu takullaha wa kunu ma’assadikin.” Ana kasancewa da ma’abota gaskiya ne. Da gaskiya da ma’abotanta a duk inda suke ko da za a rasa menene.

Abin da ke gabanmu yanzu, yadda za mu fita daga wannan zilla da muke a ciki. Na ce bari in tsuke magana din ya zuwa Nijeriya. Al’ummar musulmin Nijeriya, abin da yake gabanmu wanda zai fisshe mu daga wannan zilla da muka fada, shi ne mu ce addinmu namu shi zai iko da mu ko uban kafiri ya ki!! In ya so ba yana da bindiga ba, to ya harba don ubansa!!! Ya wuce haka nan ne? Mu mutu da karama.

Abu daya da muka tabbatar, tabbaci hakikan shi ne, in ma an kashe mu, to jinainanmu za su zama ruwan ban ruwan itaciyar Mususlunci, wadda kuma za ta kafu daram, an ki ko an so!

Da fatan Allah (T) ya nuna mana lokacin da tutar ‘la’ilaha illallah Muhammadur Rasulullah’ za ta filfila a wanna kasa da dukkanin duniya baki daya. Ya nuna mana lokacin da wannan al’umma za ta dawo da izzarta da karamarta, ta koma yadda Mahaliccinta ya so ta kasance, ‘khaira umma.’ Ta zama mai shaida ga sauran al’ummu ta hanyar nuna mata wannan hanya, ta zama ita ce jagora ba ana jan ta ba, jan wulakanci. Da fatan Allah (T) ya nuna mana wannan ba da nisa ba, kuma ya gaggauta bayyanar wanda da bayyanarsa ne za a sami mafita gaba daya ga wannan al’umma.

Wassalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuh.  

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

 
 

 

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)