Muassasar alhasanain (a.s)

Sayyida Zainab'Yar Imam Ali

23 Ra'ayoyi 02.1 / 5

Sayyida Zainab al-Kubra 'Yar Imam Ali (a.s):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com
________________________


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Shakka babu nazari bincike cikin tarihin Ahlulbaiti (a.s) da samun masaniya kan koyarwarsu ta tunani da siyasa lamari ne da ke da muhimmancin gaske wajen fahimtar koyarwa da tafarkin Manzon Allah (sawa) da addinin da ya zo da shi (Musulunci)…don haka ne ma makiya suka ba da lokacinsu ba dare ba rana wajen ganin sun toshe wannan haske da hana al'umma fahimtar irin matsayi da gudummawar da Ahlulbaitin suka bayar wajen ci gaban wannan addini da kuma 'yantar da al'umma daga duhun zalunci zuwa ga hasken Musulunci. Ahlulbaiti (a.s) dai sun ba da gagarumar gudummawa ta hanyar koyarwarsu, dabi'unsu, jihadinsu na fada da zalunci da kaucewa tafarki da dai sauransu wajen kyautata rayuwar al'umma duniya da lahira.

Ko ba a fadi ba waki'ar Karbala mai dacin gaske da ta faru na daga cikin lamurran da suka faru a tarihin Musulunci sannan wanda tafi tasiri wajen ayyana tafarkin Musulunci da kare shi. A wannan waki'a ta Karbala akwai wata madaukakiyar mace daga cikin Ahlulbaitin Manzo (s) da ta ba da gagarumar gudummawa wajen isar da sakon Karbala da kuma ci gaba da kare shi bayan shahadar dan'uwanta Husaini bn Ali (a.s) har zuwa karshen rayuwarta. Wannan madaukakiyar mace kuwa ita ce Zainab al-Kubra 'yar Aliyu bn Abi Talib da Fatima 'yar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su da alayensu). Don haka wannan dan abin da muka rubuta dai zai yi magana ne kan rayuwar wannan baiwar Allah da kuma irin gudummawar da ta bayar, don ta kasance mana abin koyi musamman ma ga matayenmu na wannan zamani, saboda kasantuwansu (Ahlulbaiti) abin koyi gare mu bayan kakansu Ma'aiki mai tsira da aminci, sannan kuma don su kasance mana abin so da kauna saboda fadin kakansu cewa: "Ku sani duk wanda ya mutu a kan son Zuriyar Muhammadu, ya mutu shahidi"

An haifi Sayyida Zainab al-Kubra ne a gidan Ali da Fatima karkashin kulawar gidan Annabci a ranar biyar ga watan Jimada Awwal shekara ta biyar bayan hijira. Babu shakka wannan rana ta haihuwar Zainab ta kasance rana ce ta farin ciki a bangare guda, a bangare guda kuma ta bakin ciki ga juyayi da iyayenta da kakanta Manzo (s). Ranar farin ciki saboda karuwar da Zuriyar Manzo ta samu da kuma irin kariyar da Musulunci ya sake samu, ranar bakin ciki kuma saboda irin abin da zai faru da ita nan gaba daga wajen makiya. Bayan haihuwar Zainab, mahaifiyarta Fatima al-Zahra (a.s) ta dauko ta ta kawo ta wajen mahaifinta Ali (a.s) don ya sanya mata suna…sai dai kamar yadda al'adarsa (Ali) ta ke bai taba wuce Manzon Allah ba wajen dukkan abin da zai gudanar don haka sai ya ce wa Fatima:"Lalle ba zan gabaci Manzon Allah wajen sanya mata suna ba, don haka bari mu jira Manzo ya dawo", don a daidai lokacin da aka haifi Zainab, Annabi (s.a.w.a) ya kasance ya yi wata 'yar karamar tafiya wajen Madina. Don haka lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya dawo, kamar yadda kuma al'adarsa take, idan har ya dawo daga tafiya baya shiga wani gida har sai ya je ya ga Fatima. Don haka ko da ya shiga gidan Fatima, sai Ali (a.s) ya masa bushara da wannan karuwa da aka yi ya kuma kawo masa abar haihuwar yana mai bukatarsa da ya sanya mata suna, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya amsa masa da cewa: "Lalle ba zan gabaci Ubangijina ba wajen sanya mata suna". A daidai wannan lokaci sai ga Mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauko da sakon Ubangiji yana mai ce wa Manzo (s.a.w.a) cewa: "Mai Girma da Daukaka yana isar maka da gaisuwa Yana mai umartanka da ka sanya mata suna Zainab", Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Hakan kuwa aka yi, nan take Manzo ya sanya mata suna Zainab. Wasu ruwayoyi sun ce bayan haka kuma sai Jibrilu (a.s) ya sanar da Manzon Allah (s.a.w.a) irin abubuwan da zai faru da ita na wahalhalu da kuma yadda za ta kasance ita kadai a Karbala wajen kare wannan addini da kuma fuskantar makiya Allah wadanda suke son ganin bayan wannan addini bayan shahadar dan'uwanta Husain (a.s).

Haka dai Zainab (a.s) ta ci gaba da rayuwa karkashin kulawar kakanta Manzon Allah (s.a.w.a) da mahaifinta Ali (a.s), wanda shi ma ya tashi ne karkashin kulawar Manzon Allah tun yana karami, da kuma mahaifiyarta Fatima al-Zahra (a.s), wacce 'ya take wa Manzo din sannan kuma ta tashi karkashin kulawa da shiryarwarsa tare da madaukakiyar uwargidansa Khadijah al-Kubra (a.s), wanda ko ba a fadi ba hakan yana nuni ne da irin tashin da Zainab za ta yi ne cikin kulawa ta musamman da ba kowani mutum ne yake samun irinta ba in ba wadanda Allah Ya zaba ba don wani aiki na musamman.

Zainab ta ci gaba da zama karkashin wannan kulawa ta Manzon Allah (s.a.w.a) har na tsawon shekaru biyar lokacin da Allah Ya yi wa ManzonSa (s.a.w.a) rasuwa, don haka sai kulawarta ta koma karkashin mahaifanta Ali da Fatima kai tsaye a karo na farko, a bangare guda kuma ga madaukakan yayuntan nan guda biyu Hasan da Husaini a gidan da duk fadin wannan duniya babu gida kamarsa, gidan da ke cike da hasken Annabci da Wilayah, gidan da Alkur'ani mai girma ya kira mutanen da suke cikinsa da sunan 'Mutanen Gidan Annabcin da Allah Ya tafiyar da kazamta daga gare su ya kuma tsarkake su tsarkakewa cikin fadin Allah cewa:  "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)

Wannan rasuwa ta Manzon Allah ta kasance lamari mai tsanani ga Zainab al-Kubra (a.s) saboda da farko dai ga rabuwa da kakanta wanda yake nuna mata tsananin soyayya, a bangare guda ga irin tsananin da iyalan nasa suka shiga sakamakon kwace musu hakkinsu da aka yi na halifancin Manzon Allah da kuma barazanar da aka ci gaba da yi wa rayuwarsu har ta kai ma ana barazanar za a kona wannan gida mai tsarki da suke ciki. Irin wannan yanayi dai ya sanya rayuwar Zainab din cikin kunci. Ana nan kuma sai ga rasuwar mahaifiyarta Fatima al-Zahra (a.s) 'yan watanni bayan rasuwar Manzo (s.a.w.a) ita ma cikin wani irin mawuyacin hali da har ta yi alkawarin sai ta isar da kukanta ga Mahaifinta idan suka sadu kan irin abin da wasu na kurkusa da shi suka yi mata (mai son karin bayani yana iya komawa ga Al-Imama wa al-Siyasa na Ibn Kutaiba juzu'i na 1 yayin da yake batu kan abubuwan da suka faru bayan rasuwar Manzo). A daidai wannan lokaci dai Zainab ta rasa wannan kulawa ta mahaifiya, babu wanda ya saura mata sai mahaifinta Ali, sai kuma yayunta Hasan da Husain da kuma kanwarta Zainab al-Sughra wacce aka fi sani da Ummu Kulthum, sai dai lamurra sun dan yi mata sauki bayan da mahaifinta ya auri Umama, jikar Manzo ta wajen 'yarsa Zainab bint Muhammad, bisa wasiccin da Fatima al-Zahra (a.s) ta yi wa mijinta Ali (a.s) yayin da take ce masa: "Ya dan baffa! Ina maka wasicci da farko da ka auri 'yar 'yar'uwata Umama a bayana, don kuwa za ta kasance ga 'ya'yana tamkar ni..... ". Ta haka ne Umama ta maye gurbin Fatima wajen bayar da kulawa irinta mahaifiya ga Zainab har lokacin da ta yi aure, wato lokacin da ta auri dan baffanta Abdullah bn Ja'afar.

Auren Zainab dai ya yi kama da na mahaifiyarta Fatima al-Zahra (a.s), saboda ita ma Zainab, kamar mahaifiyarta, mutane da dama sun zo wajen mahaifinta (Ali) neman aurenta, kamar yadda manyan gari a lokacin Manzon Allah suka zo neman auren Fatima, amma Ali ya ki yarda ya ba su, kamar yadda Manzon Allah ya ki yarda ya ba wa wadancan manyan auren Fatima, yana mai tunawa da isharar da Manzon Allah ya taba masa yayin da yake kallon 'ya'yansa (Ali) da 'ya'yan Ja'afar inda ya ce:"'ya'yanmu mata na 'ya'yanmu maza ne, 'ya'yanmu maza kuwa na 'ya'yanmu mata ne". Don haka lokacin da Ali (a.s) ya ga jama'a suna ci gaba da zuwa sai ya kira Abdullah ya ba shi auren Zainab, sannan shi da kansa ya biya kudin sadakinta daga cikin dan abin da ya mallaka. Shi dai Abdullah dan Ja'afar bn Abi Talib ne, sannan mahaifiyarsa kuma ita ce Asma'u bint Umais. An haife shi ne a Habasha (Ethiopia) lokacin da mahaifansa suke gudun hijira a wajen a bisa umarnin Manzon lokacin da al'amurra suka tsananta wa musulmi. Bayan shahadar Ja'afar a yakin Mu'uta, Manzon Allah (s.a.w.a) ya dauki nauyin kulawa da 'ya'yan Ja'afar wato Abdullahi da sauran 'yan'uwansa, inda suka sami tarbiyya irin tasa.

Zainab ta ci gaba da rayuwa karkashin kulawar mahaifinta har lokacin da ya yi shahada. A tsakanin wannan lokaci, Zainab ta kasance tare da shi da taimaka masa musamman ma dai lokacin halifancinsa da kuma fitinun da suka auku a wancan lokacin na tawaye da yakukuwan da suka faru tun daga Yakin Jamal, karkashin jagorancin Ummul Muminina A'isha, da yakin Siffin da 'yan tawaye karkashin jagorancin Mu'awiyya bn Abi Sufyan suka tilasta masa da kuma Yakin Nahrawan da Khawarijawa, duk wadannan lokuta dai Zainab ta kasance tare da mahaifinta wajen taimakon Musulunci da hana shi fadawa karkatattun hannaye, har lokacin da ya yi shahada bayan sarar da Ibn Muljam al-Muradi ya yi masa a daren 19 ga watan Ramalana shekara ta arba'in da hijira. Bayan nan kuma Zainab ta ci gaba da kasance tare da wanta Imam Hasan bn Ali (a.s) lokacin da ya zamanto halifan Manzo kana kuma shugaban muminai. A nan ma ta ci gaba da taimaka masa har lokacin da shi ma ya yi shahada.

Bayan shahadar Imam Hasan a nan ne fa asalin gudummawar da daman aka tanadi Zainab don ita za ta faru. Don kuwa bayan shahadar Imam Hasan kulawa da al'ummar musulmi da shiryar da su ya koma hannun Imam Husaini (a.s) wanda Zainab din ta fi kasance kusa da shi tun suna kanana saboda irin taimakon da zata masa a nan gaba.

Ruwayoyin sun bayyana cewa irin kauna da son da Zainab take nuna wa Husaini (a.s) yana da yawan gaske, har ta kai ma wata rana Fatima (a.s) ta tafi wajen Manzon Allah (s.a.w.a) tana ce masa: "'Ya Baba lalle ina mamakin irin tsananin so da kaunar da ke tsakanin Zainab da Husaini. Zainab ba ta taba gajiya da kasancewa tare da Husaini ba". Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce mata: "Ya 'yata! Ai a nan gaba ita ce za ta kasance tare da shi cikin wahalhalun da za su same shi". Allahu Akbar! Wannan yana nuna mana irin matsayin da Manzon Allah (s.a.w.a) yake da shi ne na sanin abin da zai faru nan gaba, don kuwa ya san irin abin da wadannan 'ya'yaye nasa za su fuskanta nan gaba daga wajen Umayyawa, wadanda su ne itaciyar da aka la'anta cikin fadin Allah Madaukakin Sarki cewa cikin Suratul Isra'; sura ta 17 aya ta 60: "….kuma ba Mu sanya gani (mafarkin) wanda Muka nuna maka ba, face domin jarraba ga mutane, da itaciya wadda aka la'anta a cikin Alkur'ani. Kuma Muna tsoratar da su, sa'an nan (tsoratarwar) ba ta kara musu ba face kangara mai girma". Malamai dai sun tafi kan cewa abin da Manzo ya gani su ne Banu Umayya, itaciyar kuwa ita ce itaciyarsu. An ruwaito A'isha tana gaya wa Marwan bn Hakam cewa: Na ji Manzon Allah yana gaya wa babanka da kakanka cewa: Ku ne la'ananniyar bishiyar da aka fadi cikin Alkur'ani'. Mai son karin bayani sai ya duba Tafsir al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, cikin mujalladi na 12 da 13 na wannan littafi yayin da yake magana kan wannan aya, sannan sai kuma Durrul Mansur na Suyuti da Tafsir al-Kurdabi duk dai yayin da suke magana kan wannan aya.

Zainab dai ta kasance tare da Imam Husaini (a.s) a wannan kokari nasa na tabbatar da Musulunci da tseratar da shi daga kokarin da ake yi na kawar da shi da karfin gaske musamman ma lokacin mulkin Yazid bn Mu'awiyya. A wancan lokacin dai abin da ake da muhimmanci ga Zainab da dan'uwanta Husaini (a.s) shi ne kiyaye wannan addini na Musulunci. Sanannen abu ne cewa, a wancan lokacin makiya karkashin jagorancin Umayyawa sun tashi da dukkan karfinsu wajen wasa da wannan addini da mai she shi ba a bakin komai ba, kamar yadda kakanninsu suka so yi, don haka babu wani abin da zai iya ceto Musuluncin in ba irin yunkurin Ashura ba, sannan kuma babu wani wanda zai iya jagorantar wannan gagarumin yunkuri in ba Imam Husaini ba, kamar yadda kuma babu wani da zai iya taimakawa Husaini (a.s) wajen cimma wannan buri in ba kanwarsa Zainab ba.

Don haka Zainab ta ba da gagarumar gudummawarta wajen karfafa mujahidai wajen ci gaba da wannan yunkuri nasu tun kafin a zo Karbala da kuma ma lokacin da aka iso aka fuskanci makiya Allah. A wannan lokaci Zainab ta ba da gagarumar gudummawa da suka hada da karfafa zukatan mataye da kananan yaran da suke Karbala, kamar yadda kuma ta taimaka wajen ba da magani da kula ga wadanda suka sami raunuka. Bisa irin wannan kokari ne ma ya sa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba wa ranar da aka haifi Zainab sunan Ranar Masu Kula da Majinyata don tunawa da kuma girmama irin rawar da ta taka wajen jinyan wadanda suka sami raunuka a Karbala.

Gudummawar Zainab dai ba ta tsaya kawai a filin Karbala ba don har bayan waki'ar Karbala, ta ci gaba da tsayawa kyam wajen kare Musulunci da wannan yunkuri na dan'uwanta Husaini (a.s) musamman ma a garuruwan Kufa, a gaban Ubaidullah bn Ziyad da kuma Damaskus a gaban Yazid lokacin da aka kawo su a matsayin fursunonin yaki.

Umayyawa dai sun fahimci irin munin aika-aikan da suka yi a Karbala, sannan kuma sun san irin matsayin da Iyalan gidan Manzo (a.s) suke da shi a idanuwan al'umma, don haka sai suka fara yada farfagandoji na karya dangane da Ahlulbaiti (a.s) da nuna cewa 'yan tawaye ne kawai da suka yi tawaye wa sarki don haka sun cancanci kisa. A daidai wannan lokaci dai wasu daga cikin mutanen Kufan sun yarda da wannan farfaganda, wasu saboda rashin masaniyyar da suke da ita wasu kuma saboda tsoro. A wannan lokaci ma dai Zainab ta nuna jaruntakarta da gudummawarta wajen bayyanar da gaskiya da kuma umarni da abu mai kyau da hani da mummuna musamman ma lokacin da ta ga mutanen Kufa sun gane su su wane ne sannan kuma sun fara nadama kan irin rashin cika alkawarin da suka yi, inda da dama daga cikinsu suka fashe da kuka cikin nadama. Ganin haka, sai Zainab ta umarce su da su yi shiru don cika wannan sako na Husaini (a.s), inda take cewa:

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Babana Muhammad da iyalansa tsarkaka zababbu. Bayan haka, Ya ku Mutanen Kufa, Ya ku ha'inai maciya amana; shin kuna kuka ne? To kada Allah Ya sa hawayenku ya bushe, sannan kuma kada wannan juyayi naku ya kare. Ku dai tamkar macen da ta kuncen igiyar da ta riga da ta kitsa ta ne, imaninku bai kasance ba face ha'inci da yaudara. Shin a cikinku akwai wani mutum in ban da mai da'awar karya na girman kai, wulakantacce, abin kyama, dan koran sarakuna, abin harin abokan gaba, tsiron da ke cikin bola, ko kuma kamar azurfar da ke cikin kabari? Ya munana abin da zukatanku suka kitsa muku, Allah Yana fushi da ku, kuma lalle za ku tabbata cikin azaba. Shin kuna kuka da nuna juyayi ne? To wallahi ku yi kuka da yawa kana ku yi dariya kadan, don kuwa ayyukanku sun munana ta yadda ba za ku iya wanke su ba. Shin ya ya za ku iya goge laifin kashe silsilar Cikamakin Annabawa, ma'adinin sakon (Musulunci), shugaban matasan Aljanna, makomar zababbunku, makomar da kuke komawa yayin musiba, hasken hujjojinku kana kuma mai kare sunnoninku. Lalle laifin da kuka aikata ya munana, kuma ya koma gare ku, babu tuba gare ku. Hakika kokarinku ya gaza kamar yadda hannayenku ma suka gaza, kun yi asara, ba abin da kuka sa kawukanku a ciki face fushin Allah, kamar yadda wulakanci da kaskanci suka fada muku. Kaiconku Mutanen garin Kufa! Shin kun san yadda kuka keta hantar Manzon Allah? Kuma wace 'yarsa ce kuka keta huruminta? Kuma wani jininsa ne kuka zubar kana kuma wani haraminsa ne kuka keta? Hakika ayyukanku sun munana kwarai da gaske, wanda munin nasu ya cika sama da kasa. Shin za ku yi mamaki idan sama ta yi ruwan jini? Lallai azabar ranar lahira ya fi zafi kuma ba ku da mataimaki. Kada jinkirin da aka yi muku wajen azaba ya rude ku lallai Ubangijinku Yana nan a madakata".

Wannan dangane da jama'a kenan da suka karya alkawarin da suka yi na kare Husaini (a.s). Cika sakon Zainab dai bai kare a nan ba don kuwa lokacin da aka shiga da su wajen Ubandullah bn Ziyad (sarkin Kufa) ma a nan ma ta nuna rashin amincewarta ga zalunci da kuma fadin gaskiya a gaban ja'irin Sarki. Hakan kuwa ya faru ne lokacin da Ibn Ziyad ya dubi Zainab da Imam Zainul Abidin (a.s) ya ce musu: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya wulakanta ku, Ya kashe ku da kuma bayyanar da ikirarinku na karya". Nan take sai Zainab ta mayar masa da kakkausar martani, ta ce masa: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya karrama mu da Annabinsa Muhammadu (s.a.w.a), Ya kuma tsarkake mu tsarkakewa, sannan kuma ya wulakanta fasiki, fajiri wanda ba shi daga cikinmu". Sai Ibn Ziyad ya ci gaba da cewa:"Ya ya kika ga yadda Allah Ya yi da iyalanki", sai ta ce masa: "Allah Ya rubuta musu mutuwa, don haka suka gaggauta zuwa makomarsu, kuma da sannu Allah Zai tada kai da su, kuma za ka amsa tambayoyi a gabanSa". Irin wadannan zafafan amsoshi na Zainab sun tona asirin azzalumi Ibn Ziyad sannan kuma ya sanya shi cikin kunya bai samu ya cimma burin da yake son cimmawa ba na wulakanta Iyalan Gidan Manzo (s.a.w.a).

A garin Damaskus a gaban Yazid Zainab ta nuna jarunta da nuna rashin amincewarta da ayyukan da yake aikatawa da kuma rashin mika masa wuya, inda take ce masa:

"Ya Yazid, duk wani abin da ka aikata yana nuni ne da tawayenka ga Mahalicci da kuma rashin imaninka da Manzo (s.a.w.a), Littafin Allah da kuna Sunnar da Annabi ya zo da ita. Lalle ayyukanka ba za su kasance abin mamaki ba, don kuwa duk mutumin da kakanninsa suka ci hantar tsarkakakkun bayi, wanda namansa ya ginu daga jinin shahidai, wadanda suka yaki shugaban dukkan Annabawa, ba abin mamaki ba ne in ya wuce dukkan larabawa wajen kafirci, aikata sabo da kuma kiyayya da Allah da ManzonSa (s.a.w.a). Ka tuna fa wadannan munanan ayyuka da ka aikata sun samo asali ne daga kafirci da kuma kullin da kake da shi saboda kakanninka da aka kashe a Badar. Hakika duk mutumin da ya sanya idanuwan kiyayya da gabansa a kanmu ba zai yi kasa a gwuiwa wajen aiwatar da wannan kiyayya a kanmu ba. Lalle ya tabbatar da rashin imaninsa da kuma bayyanar da shi da harshensa lokacin da ya ce cikin farin ciki: "Na kashe 'ya'yan Manzon Allah da kuma mayar da iyalansa fursunoni" da kuma fatan da kakanninsa sun rayu su ga wannan nasara da ya cimma don su ce 'Ya Yazid, kada hannayenka su rasa wannan karfi, lalle ka dau mana fansa a madadinmu'". Mai son ganin cikakkiyar wannan huduba yana iya matsa nan:

Irin wannan matsaya da jarunta da Zainab da sauran Ahlulbaiti musamman Imam Zainul Abidin (a.s) sun tilasta wa Yazid gaggauta sake fursunonin gidan Manzo da mai da su zuwa garin Madina don idan ba hakan ba to akwai yiyuwar al'umma su fuskanci hukumar tasa. Don haka Yazid ya shirya aka mai da Zainab da sauran iyalanta zuwa Madina. A Madinan ma dai Zainab ba ta yi shiru ba, don ta ci gaba da wayar da kan mutane kan irin munin hukumar Umayyawa da bayyana musu hakikanin abubuwan da suka faru a Karbala. Wannan lamari ma dai ya tada hankalin Umayyawa, don haka suka yi kokarin tura ta gudun hijira zuwa wani gari na daban da ba Madina ba, da farko dai ta ki amincewa amma bayan sa bakin wasu mata ta amince ta fita daga Madina, inda ta kama hanyar Masar tare da wasu mata na Bani Hashim ciki kuwa har da 'ya'yan Imam Husaini, Fatima da Sukaina.

Zainab dai ta ci gaba da rayuwa har lokacin da Allah Ya yi mata rasuwa a ranar 15 ga watan Rajab shekara ta 62 bayan hijira wato kimanin shekara da rabi kenan bayan waki'ar Karbala. Malamai dai sun sami sabani dangane da inda Zainab din ta rasu da kuma inda aka rufe ta. Wasu cewa su ke ta yi hijira zuwa Sham tare da mijinta Abdullah bn Ja'afar kuma ta ci gaba da zama a can, wasu kuma cewa suke lalle ta yi hijira zuwa Sham sai dai ta ki shiga garin tana mai cewa ba za ta shiga garin da ta shige shi a matsayin fursunan yaki ba, don haka sai ta zauna a wani kauye da ke kusa da Sham din inda ta rasu a can kuma aka bisne ta wannan guri kuwa shi ne inda kabarinta yake kuma mutane suke ziyara a halin yanzu. Wasu kuma cewa ta ke yi ta yi hijira ne zuwa Masar kuma a can ne ta rasu aka kuma bisne ta. Wadannan dai su ne mashahuran maganganu kan inda Zainab ta rasu da kuma inda aka bisne ta, sai dai da dama sun fi fifita cewa kabarin nata yana Sham din ne a garin Damaskus. Allahu A'alam.

Ko ba a fadi ba dai, saboda irin tarbiyyar da Zainab ta samu tun daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya zuwa ga mahaifanta Ali da Fatima (a.s) da kuma yayunta Hasan da Husaini (a.s), Zainab ta kasance ta mallaki wasu kyawawan siffofi da da wuya ka samu wani da irinsu in ba irin wanda ya sami irin wannan kyakkyawar tarbiyya ba. Wadannan siffofi dai sun hada da yarda da mika wuya ga umarnin Ubangiji, hakuri, jarunta, fasaha, hikima wajen magana, rashin sassauci a gaban azzalumai, taimakawa marasa shi, gudun duniya (shi ya sa ma ake mata lakabi da Zahida) mai yawan ibada (shi ya sa ma ake mata lakabi da Abida) da dai sauransu.

Zainab dai ta rasu ta bar 'ya'ya biyar, hudu maza, wato Ali, Aun, Muhammad da Abbas, mace kuma guda ita ce Umm Kulthum.

Amincin Allah Ya tabbata a gare ki Ya Zainab, ranar da aka haife ki, ranar da kika yi wafati da kuma ranar da za a tashe ki alhali kina mai ba da shaida kan abin da aka yi wa dan'uwanki Husaini (a.s) da sauran iyalai da sahabbansa.

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)