Muassasar alhasanain (a.s)

‎Sirrin Slatin Annabi

20 Ra'ayoyi 02.1 / 5

SALATI GA MANZON ALLAH DA IYALAN GIDANSA(AS). Manzon Allah(s w w) ya ce, "Wanda ya yi salati a gare ni bai yi salati ga iyalan gidanaba, za a samu jijjabai guda saba'in tsakanin salatin da sama, kuma Allah Ta'ala zai ce, "Ban karba maka ba, kuma ba ka rabauta ba. Ya mala'ikuna! kar ku haura da addu'ar tasa har sai ya hada Annabi da zurirsa. (Thawabul A'amal: 190).

Imam Aliyu (as) ya ce, "Ba wata addu'a da za ta keta sama, face sai anyi salati ga (Manzon Allah) Muhammadu da Iyalansa". (Thawabul A'amal: 187). Abu Abdullah(as) ya ce, "Duk wanda yace, "Rabbi salli ala Muhammad wa A'ali Baitihi, sau dari,100 Allah zai biya masa bukatu dari 100 , talatin a duniya, saba'in a lahira. (Thawabul A'amal: 191).

 

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)