Muassasar alhasanain (a.s)

Sayyida Fadima Masuma Qom (A.S)

5 Ra'ayoyi 02.0 / 5

Da sunana Allah mai rahama mai jin kai
Sayyida fatima ma’asuma.
السيدة فا طمة المعصومة
Mai karamcin alayen  Muhammad (SAWW)

 
An dade ana ruwa kasa tana shanye wa!!!
Na dade ina mamakin yadda duniyar musulimai take mantawa da tushe tana rikar reshe.
Ina mamakin yanda 'ya'yan gidan Manzo (SAW) suka wayi gari ba’a maganar su sai a wasu lokuta, kari a kan cewa da yawansu ba'a san su ba, alhali sanin su da son su wajibi ne bisa gwargwadon matsayin da Allah Ta'ala ya basu. Hakika a cikin halitta baki daya ba wanda ya kamo matsayinsu a ilimni da aiki da imani da kyakykyawar rayuwa kanar yadda tarihi ya tabbatar. Ballantana ma hadisai masu dimmbin yawa daga manzo (SAW) sun zo a kan matsayiin su da wajabcin bin su dama yin koyi dasu.
Allah Ta'ala yana cewa: {ان الله اصطفی ادم و نوحا و ابرا هیم و آل امران علی آلمین *زرية بعضها من بعض .....} {lalle Allah ya zabi Adam da alayen Ibrahim da alayen Imran bisa birbishin talikai. Zuriya bayan zuruyi}. Babu wanda bai san cewa Manzonmu ya fito daga tsatson Ibrahimu (AS) ba, ballantana ma ya zo ahadisi ingantacce cewa: {ان مثل اهل بيتي فيكم كمثل سفينه نوح ..................} {Musalin yan gida na a cikin ku kamar jirgin Annabi nuhu ne wanda ya shiga ya tsara wanda kuma ya ki ya halaka}   

Wacece Sayyida Fadima Ma’asuma?
An haifi wanna babbar baiwar Allah a ranar farko ga watan Zulka’ada shekara ta 13 bayan hijira kuma ta bar duniya a ranar 10 ga Rabius Sani shekara ta 201 bayan hijira. Baban ta shi ne Imam  Musa Dan Ja’afar kuma babar ta ita ce Najma khatun yar’uwa ce ga Imam Ali Arridha uwa daya uba daya, kuma ana yi mata lakabi da Ma’asuma da kuma (Fatimatul kubra)

Matsayin ta da darajojin ta
Hadisai da dama sun zo a kan matsayin wannan baiwar allar kai ka ce bayan  BABAR TA FATIMATU ZARARA `YAR MANZO ba’abar mana babbar misali a mata ba kamar ta, an karbo daga Imam Ja’afar (AS) yana ce wa: ku saurara lalle garin kum haramina ce kuma haramin `ya`yana a bayana …wata mace zata gangaro zuwa gare ta daga cikin yaya na sunanta Fadima `yar Musa, baki dayan Shi'ar ta zasu shiga aljanna da ceton ta.
An kardo daga Imam Ridha yana cewa lalle: ya Sa’ada hakika muna da harami a wajen ku, sai na ce nafanshe ka da raina Fadima yar Musa sai ya ce: na’am wanda ya ziyarce ta yana mai sanin hakkin ta (matsayin ta)aljanna tatabbata a gare shi.
Imam Jawad yana cewa: wanda ya ziyarci amma (gwaggo) ta  a garin kum allajanna ta wajaba gare shi.
Tabbas babu mamaki wadda rayuwar ta kaco kaf ta kasance ba ta da banbanci da rayuwar kakarta sayyida FADIMA AZZAHARA yan Manzo ta sami matsayi irin wannan! wanda matsayin ta na boye Allah kadai ne ya sa ni sai kuma wadanda ya yardarwa.

WAFATINTA
Tuni mun riga mun san cewa alayen Manzo (SAW) bayan wafatinsa duniya ta yi musu kunce, al’amarin da ya yi ta ci gaba har ya kai ga karbala kai har zuwa lokacin mu wannan.
Ashekara ta 200 bayan hijira sarkin wannan lokacin Abdullahil Ma’amun Dan Harunar Rashid ya turo a tafi da Imam rida zuwa marwu, bayan shekara daya sai ta tafi ta ziyarci dan'uwanta a can Marwu, sai rashin lafiya  ya kamata a wani gari kusa da kum daga nan ta nemi a karasa da ita cen kum, a inda ta rasu bayan rashin lafiyar kwana sha shida, sai aka bunne ta a nan.
Aminci ya tabbata a gare ta ranar haihuwar ta da ranar da ta rasu da ranar da za,a tashe ta.

Munir Muhammad Said Akanawi

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)