Haihuwar Annabi Isa Ba Mahaifi
HAIHUWAR ANNABI ISA BA MAHAIFI
Shin halittar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, ba za a kidaya shi a matsayin abu ne mai babbar kima ba, kuma fifiko ne? to idan haka al'amarin yake, me yasa wannan fifikon bai samu ba ga mafi daukakar halittu, wato Manzon mafi girma, Annabi Muhammad sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam. ?
Amsa
Duk da yake Annabin Muslunci, shi ne mafificin Annabawa, kuma ma fi daukakar daraja, sai dai hakan ba ya nufin cewa yana da dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Hususiyyarsu.
Akwai wasu kebance-kebance da siffofi na bai daya, wadanda ba su tsaya kawai a wani zamani daban, ko wani wuri kadai ba, kamar ilimi, da kusanci da Allah, a wadannan hususiyyar (kebauce-kebance) Manzon Allah yana gaban dukkan Annabawa. Sai dai wasu siffofi wadanda sun shafi wani kebantaccen lokaci ne, to su ba dole ne, samuwar su ba, don tabbatar da fifikon Manzon Allah mafi girma.
Irin wadannan Al’amuran ba su zamo wajibi ba, samuwarsu ga Manzon Allah.
A hakika hanya ta dabi'a ta duniyar mu, shi ne cewa shi mutum ana haihuwarsa ne daga uba da uwa, wadanda ake ce musu mahaifa. To amma Allah ta'ala ya sanya wannan al'amarin ya canzu ga Annabawa guda biyu daga cikin Annabawa, ta yanda suka zo duniya ba tare da uba da uwa ba, su ne Annabi Adam, ba Uba da uwa, da Annabi Isa an halicce shi ba tare da uba ba. Allah ta'ala, ya yi Ishara da haka a cikin wata aya daga cikin Ayoyin Kur’ani. Allah ta'ala ya ce "Hakika misalin Isa a wajen Allah, kamar misallin Adamu ne, ya halicce shi daga turbaya sai ya ce masa zamo sai ya zamo". [1]
hakika samuwar wadannan Annabawa guda biyu daga cikin Annabawan Allah dalili ne akan kudurar Allah azaliyya, wacce duk wasu dokoki na dabi'a, wadanda Allah subhanahu ya sanya su, shi ba su wajaba akansa ba, wato Allah wanda ya sanya dokar haihuwar mutum daga uba ne da uwa, wannan dokar shi bata hau kansa ba, kuma hakika wannan al'amarin ya tabbata ta hanyar halittan Annabawa biyu daga cikin Annabawansa.
Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da fifikon halittarsa ta dan adamtaka.
A farkon aiko Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) a wancan lokacin, su Yahudawa, da Nasara Mabiya Almasihu, sun karkata ga shirka, ko wani addini, daga cikin wadannan addinan sun sanya wa Allah da.
Allah ta'ala ya ce: ”Yahudawa sun ce Uzairu dan Allah ne, Nasara sunce Almasihu dan Allah ne”[2] kuma a daidai wancan lokacin, mushirikan Hijaz, sun riki alloli masu yawa, suna ma zaton cewa Mala'iku ‘ya’ya ne mata na Allah. [3]
Hakika wadannan akidu sun yi karfi a wurin mutane, ta tabbata a cikin rayukansu, zuwa ga matsayin da ba su ma zaton wani Manzo, zai zo wanda yake cin abinci, yake shiga kasuwanni, kuma yana zama a kasa yana barci, kamar yanda suke barci, sai dai su manzo a ganinsu, ya wajaba ne, haihuwarsa da dukkan motsinsa, da rahsin motsinsa, da dukkan al'amaransa, su zamo al'amura ne wadanda ba na dabi'a ba.
To, a cikin wancan yanayi wanda ya gurbata da shirka, wanda kuma, gaba daya an fi yarda da imanin cewa su Annabawa, ‘ya’yan Allah ne, ke nan idan aka haifi wani sabon Annabi, kamar haihuwar Annabi Isa (a.s) ba tare da Uba ba, ko kamar Annabi Adam (a. s). ke nan wasu irin hujjoji na barna zasu samu, a cikin kwakwalen mutane? shin wannan al'amarin ba zai sanya munanan akidu su kara samun karfi da tabbatuwa ba?
To, shin zai yiwu ga wani Annabi, wanda yake da irin wadannan siffofin, ya iya kiran mutane zuwa ga tauhidi, da ibadar Allah daya, kuma yaci nasara a cikin da'awarsa?
Hakika Kur’ani ya yaki wadannan akidu, kuma ya bayyana a wurare da yawa, kuma a fili balo-balo, a cikin kunnuwar mutane, wannan babban sabanin, da irin a kidunsu, kuma ya karfafa cewa shi Manzo, dan Adam ne irin halittarsu, a saboda haka ne za mu ga Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam), yana bayyanawa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa shi mutum ne, kamar sauran mutane, kuma Kur’ani ya kasance yana zance da Annabin, yana nemansa akan ya bayyana wannan al'amarin ga mutane, yana kuma karfafawa a kai, irin wannan ne ya zo a cikin fadarsa, madaukakin sarki cewa: "Ka ce iyaka kawai ni mutum ne irin ku, ana yin wahayi gare ni) [4] Natijar wannan magana ita ce, wannan hususiyyar idan ta kasance a zamanin Isa (a. s), za a iya kidaya ta a matsayin wata daraja ce don amfanarwa, da isar da sakon addini, to amma da ace ta faru ga Manzon Musulunci (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da za a dauke ta a matsayin al’amari na raunana Addinin musulunci.
A cikin Kur’ani mai girma ana ambaton Isa Annabi (Alaihis salam) akan cewa shi kalmar Allah ce. [5]Ana yabon sa, ana girmama shi, kamar sauran Annabawa akan hakuri, da turjiya[6] da zamowar sa Siddiki [7] kuma Makusanci[8] kuma mai yawan tuba[9] mai Basira [10] to amma bamu samu wani yabo da kwarzontawa ba, ga Annabi Isa (a. s) a cikin Kur’ani mai girma da ruwayoyin Ahlul bait a fuskar zawowansa an haife shi ne ba tare da uba ba.
A cikin wasu ayoyin, Allah Ubangiji madaukakin Sarki ya kidaya falala da ni'imomin da ya yi su ga Annabi Isa (a. s) da mahaifiyarsa, yana cewa: ”A lokacin da Allah ya ce ya kai isa dan Maryam, ka tuna ni'imata a kanka da mahaifiyarka a lokacin da na karfafa ka da ruhi mai tsarki, kana yin magana da mutane, alhali kana cikin tsumman goyo da lokacin da kake dattijo, da lokacin da na koyarda kai littafi da hikima da attaura da Injila, da lokacin da kake halitta suran tsuntsu daga tabo da izinina sai kayi huri a cikinta sai ta zamo tsuntsu da izini na, kuma kana warkar da makaho da kuturu da izini na da lokacin da kake fitar da matattu da izini na, da lokacin da na kame banu Isra'ila daga barinka, a lokacin da ka zo musu da hujjoji sai wadanda suka kafirta daga cikin su sukace, hakika wannan ba komai ba ne sai dai tsafi a fili. ) [11]
Hakika haihuwar Annabi Isa (Alaihis salam) ta uwa kawai, kuma ba tare da tana da miji ba, wani abu ne da ba a rasa hikima a cikinsa ba, ban da ma tabbatar da kudurar Allah buwayayye, gagara misali, marar iyaka, wacce dama su bani Isra'ila sun yi imani da ita, Ita haihuwar wata aya ce da hujja, a matsayin wata hanya ce ta shiryar da mutane, to amma wasu adadin mutane, sun fadi warwas, a wannan jarabawar.
Allah ya fada a cikin Kur’ani mai girma: (da wacce ta kiyaye farjinta sai muka hura ruhin mu a cikinsa, kuma muka sanya ta da danta a matsayin aya ce ga halittu. ) [12]
Allama tabataba'i a kan ita wannan ayar ya ce: ”Wanann ayar ta kadaita su, wato ita Maryam da Isa (a. s) dukkansu biyu a matsayin aya guda daya ga halittu, don ayar ita ce haihuwar, kuma ita Maryam ita ce farko wajen tsayuwar ayar, a saboda haka ne Allah ta'ala ya ce "mun sanya ta da danta a matsayin aya” amma bai ce: kuma mun sanya danta da ita a matsayin aya ba) [13].
A saboda haka ke nan, wannan al'amari dalili ne akan kudurar Allah, kuma hanya ce ta shiryar da mutane da jarabasu[14] duk da yake zai yiwu a ce mu'ujizar haihuwar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, a wancan lokacin, wanda ilimin magani yake tashe kuma ya baibaye ko ina, ita mu'ujizar dalili ne akan kudurar Allah marar iyaka, kuma wani nau'i ne, na girmamawa da fifitawa ga Annabi Isa (a. s) kuma ya yi amfani da wannan daukakar, wajen isar da shari'arsa da hukunce hukucenta daga Allah.
[1] Suratu ali imran 59
[2] Suratut tauba aya ta 30
[3] Sun sanya wa Allah abokan tarayya a cikin aljannu alhali shi ya halicce su kuma suka kirkiri karyar cewa yana da ‘ya’ya maza da mata ba tare da suna da wani ilimi ba tsarki ya tabbata gareshi ya daukaka ga barin da abin da suke siffantawa, suratul an’ami aya ta 100.
[4] “suka ce mene ne ya samu wannan manzon yana cin abinci kuma yana tafiya a cikin kasuwanni ina ma da an sauko masa da mala’ika ya zamo mai wa’azi a tare da shi”
[5] Suratul kahafi, 11. suratu fussilat, 6
[6] Suratun nisa’i, 171
[7] Suratu maryam 14
[8] Suratu maryam 15
[9] Shafi na 17
[10] Shafi na 45
[11] Suratul ma’idah, aya ta 110.
[12] Suratul anbiya’i, aya ta 91.
[13] Littafin tarjumatul mizan, wallafar Muhammad Husain taba taba’i, juzu’i na 14, shafi na 447, maktab almanshurat al-islamiyya, kum, 1347.
[14] Yazo a cikin wasu ruwayoyi cewa haihuwarsa jarawa ce ga mutane almas’udiy abul hasan a cikin littafinsa mai suna isbatul wasiyya lil imam aliyyu bin abi talib, shafi na 80, intisharat ansariyan, bugu na uku, 51624”an ruwaito cewa iblis ya tafi nemansa (neman annabi isa) a lokacin haihuwarsa day a iso wurinsa sai ya samu mala’iku sun kewaye shi, sai ya matsa zai je wajensa sai mala’iku suka yi masa tsawa, sai ya ce:waye mahaifinsa?sai suka ce masa:kamar misalign annabi Adam yake. sai ya ce :na rantse da Allah sai nabatar da kaso hudu a cikin biyar na dukkan halittu a dalilinsa. ”