Muassasar alhasanain (a.s)

ka san kanka

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Da sunan Allah mai Rahma mai jin Kai.

ka san kanka

 

Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzanSa Muhammad da Iyalan gidansa tsarkaka.

Za mu fara gabatar da wannan bahasi akan mutum, wato sanin hakikanin mutum, amma da yake bahasin da alamun zai tsawaita kuma sakamakon rashin wadatar lokaci, da kuma kada yawan Shi a lokaci daya ya gunduri mai karatu; to zamu karkasa shi zai rika fitowa daki-daki. Kamar haka, wannan ne kashi na farko:

Mutum ta fuskoki daban-daban, ya kasance abin la'akari ko bahasi wato maudhu'in ilmomi kala-kala da kowannensu yake bahasin mutum ta fuska daya, kamar: Ilmin sanin dabi'ar Dan Adam (psychology), ilmin zamantakewar Dan Adam (sociology), Tarihi, Akhlak, Likitanci, Ilmin rayuwar Dan Adam (biology) ds... wadanda kowanne daga cikinsu ya dauki wani bangare ne na samuwar mutum yana yin bahasi a kai.

To mu a wannan bahasin za mu yi magana a kan mutum ne ta fuskancin cewa Shi mutum halitta ce ko samuwa wacce take karbar Kamala; kuma za mu yi magana ne dangane da kamala ta kololuwa da kuma hanyar isa gare ta (kamalar), kuma za mu yi kokari ta hanyar zurfafa tunani a cikin halittar tashi da kuma gano abubuwan da suke a fitirarmu (Dabi'ar da take bangaren asalin halittar mu ce) wadanda aka sanya mana su domin wucewa da isa ga hadafi na asali, da kuma sanin abubuwan da suke tattare da mutum da suka bunkasa shi yake da wannan matsayi babba a cikin halittu.

Sannan kuma mu san abin da yake sa dangantaka tsakanin su da halittarmu kuma suke ba mu damar yin amfani da kansu, da kuma kokari wajen salladuwa da karfafa su yana dada mayar damu masu karfi da kasantuwa cikin shiri na musamman, domin kara kammaluwa, saboda kowanne lokaci gwargwadon sanin karfinmu na ciki wato karfin ruhinmu da kuma sanin kayan aiki na wajen ruhinmu; to gwargwadon yiyu war isar mu ga kamala da sa'ada ta hakika zai kasance. Wadda da taimakon Allah madaukakin Sarki hakan zai kasance taku zuwa ga kammalar kanmu da wasunmu.

Dan haka, Maudhu'in bahasinmu zai kasance kamar haka, 'MUTUM A MATSAYINSHI NA SAMUWA MAI KARBAR KAMALA'. Kuma hadafi da fa'idar bahasin zai kasance kamar haka, 'SANIN KAMALA TA HAKIKA DA KUMA HANYAR ISA GA ITA'. Kuma hanyar gabatar da wannan bahasi ita ce, BINCIKEN MAHANGOGI NA CIKIN MUTUM (INTERNAL) DOMIN KARIN SANIN BUKATU DA SINADARAN DA SUKE A CIKINMU DA AKA SANYA MANA DOMIN ISA GA KAMALA, DA KUMA ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKA MANA WAJEN KAIWA GA ITA, DA KUMA BINCIKEN SHARUDAN DA ZA MU IYA AMFANUWA DA SU DOMIN WANNAN NUFI NAMU (isa ga kamala).

Kuma za mu yi kokari wajen gabatar da wannan bahasi da kuma tabbatar da abin da muke bukata, za mu yi amfani da hujjoji da misalai saukaka da kuma amfani da mafi saukin fahimta na daga bayanai domin fito da abubuwan da suka shige mana duhu wadanda suma sun shafi wannan bahasi. Idan kuma da bukatuwa ko kuma gurin da ya zama wajibi za mu yi ishara ga dalilai na hankali da ruwayoyi masu Dan zurfi.

 

LARURAR (WAJIBCIN) SANIN KAI:

Dangane da Samuwar da a fitirar shi yana da son zatin kanshi; to hakika dabi'a ne cewa ya dubi kanshi kuma ya fantsama zuwa ga sanin kamalolin kai da kuma hanyar isa gare su. Dan haka fahimtar lalurar sanin kai abu ne a fili wadda ba ya bukatar wasu dalilai na kwakwalwa masu sarkakiya ko na ruwaya. Ta wannan fuskar, gafala daga wannan hakikar da ruduwa da abubuwan da ta kowacce fuska ba su da wani tasiri a kamala da sa'adar mutum, al'amarine mai ban al’ajabi kuma karkacewa ce mai zurfi, kuma ya zama wajibi a binciki wannan al'amari tare da nemo illarshi (sababinshi) da kuma sanin hanyar magancewa da kubuta daga gare shi.

Dukkan yunkurorin mutum, hada da na ilmi da na aiki, yana yin su ne domin tanada ko samar da jin dadi ko alfanoni da kuma masalih na Dan Adam. To dan haka sanin Shi kanshi mutum da faruwarshi kai da ma kamalolin da mai yiwuwa ya karkata ga su, dole su gabaci dukkan masa'il, kai in yawaita ma, ba tare da sanin hakikar mutum da kimarshi ta hakika ba; to dukkan wasu bahasosi da yunkurori za su kasance ba su da wata alfanu.

Dagewa da kuka ga saukakkun addinai da shuwagabanninsu da malaman Akhlak suke yi akan sanin kai da mayar da hankali ga shi, dukkan wannan shiryarwa ne zuwa ga wannan hakika ta Fitra da kuma hankali.

Alkur'ani mai tsarki, ya danganta ko ya kwatanta Mantuwa ko gafala da kai (self) a matsayin mantawa da Allah kuma Ya sanar da kwatankwacin ukubar wannan sabo, inda yace:

و لا تكونوا كالذين نسوا الله فانساهم انفسهم (حشر : 19)
Ka da ku kasance kamar wadanda su ka manta Allah; sai Shi ma Ya mantar da su kawukansu. (Hashr, aya ta 19)

Sannan kuma a wani gurin dai Allah (SWT) ya kuma cewa:

عليكم انفسكم لا يضركم من ضل اذا اهتديتم

"Ya ku wadanda suka yi imani! Ku lizimci rayukanku (kawukanku), Wanda ya bace ba zai cuce ku ba idan kun shiryu..." (Surar Ma'ida aya ta 105).

Hakazalika manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Alihi) shima dangane da sanin kai ya ba da muhimmanci kwarai da gaske, a yayin da ya danganta hakan da hanyar sanin Allah, inda yake cewa:

من عرف نفسه عرف ربه

"Wanda ya San kan shi; to ya san Ubangijinshi"

Hakazalika a cikin 'yan gajerun kalmomi Imam Ali (alaihissalam) ya yi ishara da makamantan wadannan a cikin gurarul hikam, inda yake cewa:

معرفة النفس انفع المعارف

Wato,sanin kai mafi anfanin ilmomi.

عجبت لمن ينشد ضالته و قد اضل نفسه فلا يطلبها

Wato, na yi mamakin wanda ya ke neman bataccen abinshi alhali ya batar da kanshi kuma ba ya nemanshi .
Sannan a wani gurin ya ce:

عجبت لمن يجهل نفسه كيف يعرف ربه

Ina mamakin wanda ya jahilci kanshi ya za ayi ya san Ubangijinshi.

غاية المعرفة ان يعرف المرء نفسه

Kololuwar sani shine mutum ya san kanshi.

Shi yasa masanan ilmomi na yammaci suke cewa: "Human being is the most complex creature" wato, mafi cukurkudaddiyar halitta da ta kunshi abubuwa masu yawa da sarkakiyar gaske.

To wannan kenan!

Da yake a wannan bahasi akwai wasu ibarori (kalmomi) wadanda da yiwuwar amfani da su da wasu ma'anoni daban a wasu gurare, to dan haka akwai bukatuwar mu dan yi bayanin wasu daga ciki, domin gujewa wata fahimta ta daban dangane da bahasin. Dan haka zamu yi bayanin su kamar haka:

(1) Abin da muke nufi da 'SANIN KAI' -kamar yadda aka yi ishara a baya- shine Sanin Mutum ta mahangar cewa shi samuwa ce wadda ya ke da wasu Kuwwa ko Isti'idad wato wani Karfi ko Baiwa (power, strength, faculties or potentials) domin samun kai wa ga kamala ta mutuntaka. Saboda haka a wannan bahasi namu ba za mu wadatu da kawai Ilmin da yake halartacce ba -wato Ilmin da ake kira 'al-'ilm al-hudhuri (Immediate knowledge or knowledge by presence)- wadda kowa yana da shi. Hakazalika a nan ba muna nufin kammalallen Ilmin hudhurin da a yayin da masana Allah (A'rifai) suke tafiya ta ma'anawiy ake yaye musu labule suke ganin hakikanin su ba; saboda Shi wannan sakamakon Gina kai ne mutum ya ke kai wa ga shi ba wai daga mukaddimominshi ba.

Hakazalika 'SANIN KAI' a nan ba muna nufin sanin Gabobin jikin mutum ba, da kuma yadda su ke yin aiki kamar yadda a Physiology ake bahasin hakan, a'a wannan ma ba shi da alaka da wannan bahasin namu.

Kai hatta sanin dabi'a da kuwwat (internal powers) na mutum wadanda ake bahasin su a Ilmin dabi'a (psychology), a nan ba su muke nufi ba; saidai za mu iya amfani da wani yanki na Ilmin dabi'a domin ya zame mana wata matakala ta bahasinmu.

(2) Shi kuma 'GINA KAI' a dunkule shine Duben kai, tsarawa da bai wa ayyuka na rayuwa fuska mai kyau, ba wai kange su da yi musu iyaka ba. Da wata ma'anar za mu iya cewa manufar wannan bahasin shine, domin mu san ya za mu tsara ilmi da aikinmu kuma mu san zuwa ina za mu karkata akalarsu domin mu isa ga kamala ta HAKIKA, saboda haka lazima wato hadafin da yake tattare da wannan bahasi shine Inkari ko Kalubatantar HAKIKOKI na wajen Kwakwalwa ko kuma inkarin kimomin da saninsu ko yaya karkata ne ga idealists (wadanda suka tafi akan yiyuwar neman kamala a komai), wadda hakan yana da fuska ta nakasu. Hakazalika inkarin fahimtar Pragmatists (wadanda suka tafi akan cewa hakika itace yin Aiki mai amfani domin kawai rayuwar wannan duniya), to duk wadannan ba za su kasance masu nuna hakikar wannan bahasi namu ba, face ma za mu ga cewa kishiyan su ne.

(3) abin da mu ke nufi da Duben kai (self-inclination) da duben cikin mutum da kuma binciken kai a wannan bahasi, shine Mutum tare da tunani a Samuwar Shi kanshi da kuma kyautattukan da suke a halittarshi wadda suka hada da dama ta fahimtar abubuwa da aikata abubuwan da za su sanya ya zama ba kamar yadda yake a farko ba, da kuma sanin hadafi na asali da kamala ta kololuwa da kuma samun sa'ada ta hakika. Ba wai muna nufin mutum ya cure komai na daga tunani ba, ga samuwar kanshi shi kadai ba tare da dube ga wanin Shi ba, kuma ba wai ya ce zai yi inkarin dukkan kayayyakin aikin da suke a cikin al'umma domin ci gaba da kamalar mutum ba.

Dan haka ma'anar wadannan istilahohi a nan shine ta fuskancin ma'anarsu abin so (positive meaning), ba wai Ma'anarsu kamar: Son kai, damuwa da kai, son zuciya, fifita kai, bautar kai d.s.. wadda a ilmin dabi'a da Akhlak da wasunsu ake amfani da su ba, wadda a wadancan gurare da ma'anar abin Ki (negative meaning) su ke.

(4) Hakazalika akwai wasu lafuzza wadanda suna da ma'anoni na istilahi da dama, kuma ana yin amfani da su wajen ma'anoni mabambanta a wasu ilmomi, kai mai yiwuwa ne ma a cikin ilmi guda amma a makarantu mabambanta na wannan Ilmin, Ma'anarsu ta bambanta, misalinsu: hankali, rai ko kai, gani ko mahanga, ji, riska ko sawwarawa. d.s.. to ta wannan fuska domin ayyana ma'anar da ake nufi dole ne a jingina da ma'anar kalmomin da suka zo a gefensu da kuma irin maganar ko gundarin batun (topic) da ake yi a gurin, na kawo wannan ne saboda ko da wasu sun San istilahohin a sauran ilmomi na kimiya ko philosophy, to kada su takaita fahimtarsu a iya fagensu, domin kada su yiwa wasu ibarori mummunar fahimta.

To za mu tsaya nan, a bahasi na gaba za mu tashi a ma'anar KAMALA wadda ita ce maksad (destination) din mu a karshen bahasin dukan shi.

 

Wassalamu alaikum.

Littattafan da aka duba:

  1. Al-Kur’ani mai tsarki
  2. Nahjul fasaha
  3. Gurar al-Hikam

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)