Muassasar alhasanain (a.s)

Siyasa Da Addini

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

DA sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 

Tsiran Allah da amincinsa su tabbata ga annabi Muhammad Al-mustafa (s.a.w) da alayensa tsarkaka

 

Wannan shi ne sakon da Imami Sayyidi Ali dan Abu Dalib ya aika zuwa ga Malik Ashtar, da ya tura a matsayin wakilinsa (gwamnansa) a Misra, wanda kafin ya kai zuwa gareta ne Mu'awiya dan Abusufyan ya aika wanda ya sanya masa guba a zuma ya sha ya mutu a hanya.

Wannan sako ne na kundin tsarin aiki ga duk wani jagora ga kansa da al'ummarsa don sanin yadda zai yi jagoranci nagari da mu'amala mai kyau ga jama'arsa.

Mustashrikun (Turawan yammancin duniya kwararru kan ilimin sanin addinin musulunci) sun himmantu da wannan sakon, kuma a kasar Jamus sun tarjama shi zuwa yarensu suka sanya shi "Dokar Asasi" da ake dogaro da shi a matsayin "Makomar Doka".

Kamar yadda a Kenya an tarjama sakon zuwa yaren Suwahili aka aika shi ga shugaban kasar (wanda yake Kirista ne), sai sakon ya kayatar da shi ya yi umarni a raba shi ga dukkan gwamnoni da manyan ma'akatun kasar, ya kuma yi kalamai da suke nuni ga cewa; da sun san wannan sakon tun da wuri, da ba su kasance a yadda suke ba.

Haka nan Majalisar dinkin duniya ta aika sakon ga sarakunan kasashen larabawa tana tunatar da su cewa akwai mamaki cewa suna da irin wannan sakon amma ba sa yin aiki da shi don warware dukkan wata matsala da ta addabi dan Adam!

Sayyidi Ali shi ne na farkon jagororin Ahlul-baiti guda goma sha biyu da manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da riko da su tare da littafin Allah bayan wafatinsa kamar yadda ya zo a manyan littattafan ruwayoyi na hadisai. Sai dai kauce wa wannan wasiyya ta manzon Allah (s.a.w) ya sanya al'umma fadawa cikin rudani da bambance-bambance har zuwa wannan zamanin.

Allah (s.w.t) yana fadi a littafinsa game da alayen manzon Allah (s.a.w) cewa:

"Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku ne Ahlul-baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa" .

Wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa:

"Lallai ni mai bar muku nauyayan (alkawura) biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su" .

Hadisai sun yi nuni da su a littattafai daban-daban, kamar yadda Shehu Usman dan Fodio Allah ya kara masa yarda ya kawo sunansu a cikin Nasihatu Ahlizzaman a yayin da yake kawo salsalar Imam Mahadi (a.s) wanda zai zo a karshen duniya. Da al'umma ta fuskanci koyarwarsu, da ba ta samu kanta cikin wannan faganniya da rudani ba, sai dai abin da ya faru ya riga ya wakana.

Domin tubarraki zamu kawo sunyensu kamar haka: Imam sayyidi Ali (a.s), sai Imam Hasan (a.s), sai Imam Husain (a.s), sai Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s), sai Imam Muhammad al'Bakir (a.s), sai Imam Ja'afar asSadik (a.s), sai Imam Musa alKazim (a.s), sai Imam Ali arRidha (a.s), sai Imam Muhammad al'Jawad (a.s), sai Imam Ali al'Hadi (a.s), sai Imam Hasan al'Askari (a.s), sai Imam Muhammad al'Mahadi (a.s).

 

Sakon Imam Ali (a.s) zuwa ga Malik Ashtar

Nahjul-balaga: Wasika / 53.

[Shi ne mafi tsayin sako da aka rubuta kuma wanda ya fi kowanne tattaro kyawawan sakonni]

 

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai

Muhimman abubuwa Hudu ga Jagora (Hadafin Jagoranci)

Wannan shi ne abin da bawan Allah sarkin muminai Ali (a.s) ya umarci Malik dan al'Haris al'Ashtar da shi a sakonsa zuwa gareshi yayin da ya sanya shi shugaban Masar: Hada harajinta, da yakar makiyanta, da gyara mutanenta, da raya kasarta.

 

Asasin Fikirar Tunani da Ayyukan Jagora

Ya umarce shi da jin tsoron Allah da zabar biyayyarsa, da biyayya ga umarninsa a littafinsa: daga farillansa da sunnoninsa wacce babu wanda zai rabauta sai da biyayyarta, kuma babu wanda zai tabe sai da musanta ta da tozarta ta. Kuma (ya umarce shi da) taimakon Allah matsarkaki da zuciyarsa da hannunsa da harshensa, domin shi Ubangiji (sunansa ya girmama) ya lamunce wa wanda ya taimake shi da taimakonsa, da daukaka wanda ya daukaka shi.

 

Tsarkakewar Jagora ga Kansa

Kuma ya umarce shi da ya kame kansa gun sha'awowi, ya rike kansa gun burace-burace, domin rai mai umarni ce da mummuna sai dai wanda Allah ya yi wa rahama.

 

Kular jagora ga na kasa da shi

(Yaya kuma ya kamata jagora ya kalli kansa?)

Sannan ka sani ya kai Malik ni na aika ka zuwa gari ne da ya kasance adalci da zalunci sun gudana a karkashin wasu dauloli kafin zuwanka, kuma mutane zasu duba lamarinka kamar yadda kai ma kake duba lamarin masu mulki kafin kai, kuma zasu fadi abin da kake fada kan wadancan a kanka.

Kuma kawai ana gane salihai ne da abin da Allah yake gudanarwa garesu ta harsunan bayinsa, don haka tanadin aiki na gari ya kasance shi ne mafi soyuwar tanadi gunka.

Ka mallaki son ranka, ka hana kanka abin da bai halatta gareka ba, ka sani hana rai shi ne yi mata adalci cikin abin da ta so da wanda ta ki.

 

Son Jagora ga Jama'arsa

(Wajibi ne son jama'ar kasa dukansu ya kasance shi ne mafi girman siffar jagora)

Ka sanya wa zuciyarka tausayin al'umma da kauna da tausayawa garesu, kada ka zama wani zaki mai cutarwa garesu da ake farautar cinsu, domin ka sani su (jama'a) iri biyu ne, ko dai dan'uwanka a addini, ko kuma tsaranka a halitta, suna samun yin kuskure, kuma cututtuka suna samun su, kuma ana ganin ayyukansu na gangan da na kuskure, sai ka ba su afuwarka da yafewarka kamar yadda (kai ma) kake so Allah ya ba ka afuwarsa da yafewarsa, ka sani kai kana samansu, mai jagorancin lamari duka (shugaban kasa) yana samanka, kuma Allah yana saman wanda yake jagoranka. Kuma tabbas ya wadatar da kai lamarinsu, ya kuma jarrabe ka da su (don ya ga yaya zaka yi adalci ga kanka da kawukansu).

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)