Muassasar alhasanain (a.s)

Asasin Shi'anci 2

1 Ra'ayoyi 04.0 / 5

DA SUNAN ALLAH MAI RAHA MA MAI JIN KAI

 ASASIN SHI’ANCI 2

CI GABAN (ASASIN SHI’ANCI)  DAGA MAKALA TA FARKO:-

ªMaganganu da Ra’ayoyi

Wasu marubuta kuma ba sa ganin cewa an samo Shi’anci tun zamanin Manzon Allah (s.a.w) ba face dai a bayansa. Ga sunayensu da abubuwan da suka fadi:

1- Ibn Khaldun

Ibn Khaldun ya tafi kan cewa Shi’anci ya bayyana ne lokacin Shura, wato akwai wasu sahabbai da suke tare da Ali, suna ganin shi ne yafi cancantar halifanci sama da waninsa, lokacin da aka hana shi aka ba wa waninsa sai suka nuna rashin amincewarsu, daga cikinsu akwai Zubair, Ammar bn Yasir, Mikdad bn Aswad da sauransu sai dai jama’a sun tsaya kyam suka gargade su kan hakan, ba su ci gaba da boren nasu ba[1].

Wannan ra’ayi ba karbabbe ba ne saboda Shi’anci tun zamanin Manzon Allah (s.a.w) ya faro da kuma bayyana a fili. Tun a wancan lokacin wasu manyan sahabbai wadanda suke kan gaba a harkar Shi'anci suka kafa wa halifa Abubakar hujjoji masu muhimmancin gaske da suke nuni da abin da ‘yan Shi'a suka tafi a kai na cancantar halifanci da Imam Ali (a.s) yake da shi. A nan gaba za mu ambace su.

2- Ibn Hazm

Ibn Hazm ya tafi kan cewa Shi’anci ya bayyana ne bayan kashe halifa Usman yana mai cewa: daga nan sai Usman ya dare karagar halifanci na tsawon shekaru sha biyu har ya mutu. Bayan mutuwarsa ne aka samu sabani daga nan ne al’amarin rafilawa ya faro[2].

3- Usman bn Abdullah al-Hanafi

Usman bn Abdullah al-Hanafi ya goyi bayan ra’ayin Ibn Hazm yana cewa: Rarrabuwan kan al’umma ba ta faru ba lokacin Abubakar da Umar da Usman, face dai bayan kashe Usman inda Rafilawa suka bayyana[3].

Wadannan ra’ayuyyuka na Ibn Hazm da al-Hanafi ba su dogara da wata hujja ta ilimi ba saboda Shi’anci ya bayyana ne tun zamanin Manzon Allah (s.a.w), gwamnatin Shi'a ne ta kafu bayan kashe Usman lokacin da aka zabi Ali (a.s) a matsayin halifa. A wannan lokacin ne adalci da daidaito tsakanin al'umma ya yadu irin wanda jama’a ba su taba ganin irinsa ba. Hakan ya sanya yaduwar Shi’anci da kaunar Ahlulbaiti (a.s) a dukkan duniyar musulmi.

4- Ibn Nadim

Ibn Nadim yana ganin Shi’anci ya samo asali ne lokacin da Dalha da Zubair suka saba wa Imam Ali (a.s) lokacin da suka bukaci (fansar) jinin Usman, yayin da ya yake su da kawo karshen borensu. Wadanda suka bi Aliyu ana kiransu da ‘yan Shi'a. Ali ya kasance yana ce musu: ‘Yan Shi’ana, sannan kuma ya sa musu sunan kungiyar tsarkaka, kungiyar waliyai… kungiyar sahabbai[4].

A baya dai mun ambaci dalilan bayyanar Shi’anci a zamanin Manzon Allah (s.a.w), don haka tawayen Dalha da Zubair da A’isha ga hukumar Imam Ali (a.s) ba shi da wata alaka da kafuwar Shi’anci.

5- Taha Husain

Dakta Taha Husain yana cewa: Lalle kalmar Shi'a da ma’anarta na hakika a wajen malaman fikihu da akida da tarihi ba ta kasance ba lokacin rayuwar Ali, face dai an samo ta ne jim kadan bayan rasuwarsa.

Ma’anar kalmar Shi'a a lokacin Ali ita ce dai tsohuwar ma’anarta ta lugga da ta zo cikin Alkur’ani mai girma cikin fadin Allah Madaukakin Sarki cikin Alkur’ani cewa:

﴿وَدَخَلَ الْمَدِينَةَ عَلَى حِينِ غَفْلَةٍ مِّنْ أَهْلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيْنِ يَقْتَتِلانِ هَذَا مِن شِيعَتِهِ وَهَذَا مِنْ عَدُوِّهِ فَاسْتَغَاثَهُ الَّذِي مِن شِيعَتِهِ عَلَى الَّذِي مِنْ عَدُوِّهِ فَوَكَزَهُ مُوسَى فَقَضَى عَلَيْهِ

“Kuma sai ya shiga garin a lokacin da mutanen garin suka shagala, sai ya samu, a cikin garin, wadansu maza biyu suna fada, wannan daga kungiyarsa, kuma dayan daga makiyansa, sai wannan da yake daga kungiyarsa ya nemi agajinsa, sai Musa ya yi masa kulli ya kashe shi…[5], da kuma fadinSa Madaukakin Sarki cikin Suratus Saffat:

﴿وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَ

“Kuma lalle daga kungiyarsa, hakika, Ibrahim yake”[6].

Ma'anar Shi'a cikin wadannan ayoyi guda biyu da wasunsu ita ce kungiya ta wasu mabiya da mataimaka da suka daidaita kan wani ra’ayi da tafarki. Mutumin da ke cikin ‘yan Shi’an Musa ya kasance daga cikin Bani Isra’ila ne shi kuwa mutumin da ke cikin makiyan Musa ya kasance daga cikin Misirawa ne.

Don haka ne tsoffin malaman tafsiri wadanda suka dauko tafsirinsu daga fakihai cikin sahabbai suke cewa: Ibrahim ya kasance daga cikin ‘yan Shi’an Nuhu wato yana kan tafarkinsa da riko da shi kamar yadda wadannan malaman tafisiri suka fadi. ‘Yan Shi’an Ali a lokacin halifancinsa su ne sahabbansa da suka yi masa mubaya’a kuma suka bi ra’ayinsa, shin wadanda suka yi yaki tare da shi daga cikinsu ko kuma wadanda ba su yi ba. Lafazin Shi'a lokacin Ali ba ta takaita kan sahabbansa su kadai ba, saboda shi kansa Mu’awiyyah yana da ‘yan Shi’ansa su ne wadanda suka bi shi na daga mutanen Sham da wasunsu.

Taha Husain ya kara da cewa:

Don haka lokacin Ali Shi'a ba ta da ma’anarta da aka sani a wajen malaman fikihu da na akida, face dai a lokacin ta kasance lafazi ne kawai kamar sauran lafuzza da take nufin ma’anarta na kurkusa da ake amfani da ita ga dukkanin bangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna. Ni ban ga wani tsohon nassi da ke jingina lafazin Shi'a ga Ali ba kafin abkuwar fitina, kafin abkuwar fitinan Ali ba shi da wasu jama’a (‘yan Shi'a}bayyanannu da suka bambanta da wasunsu.

Ya ci gaba da cewa:

Ma’anar dukkan hakan shi ne cewa Ali (a.s) ba shi da wata jama’a ta ‘yan Shi'a da suka bambanta da sauran al’umma kafin abkuwar fitina, sannan ba shi da wasu mabiya (‘yan Shi'a) da ma’anar da malaman fikihu da akida suka sani lokacin halifancinsa[7].

Akwai wadansu abin lura cikin maganganun Dakta Taha Husain kamar haka:

Na farko – Fadinsa cewa: 'Lalle kalmar Shi'a da ma’anarta na hakika a wajen malaman fikihu da akida da tarihi ba ta kasance ba lokacin Ali, face dai an samo ta ne jim kadan bayan rasuwarsa…' lalle akwai abin dubi cikin wannan zance, saboda Shi'a da ma’anarta da aka sani ta faro ne zamanin Ma’aiki (s.a.w). Akwai manya-manyan sahabbai da suka yi amanna da imamanci Imam Amirul Muminin Ali (a.s) bugu da kari kan hadisan da muka ambata da suke ishara da daukakan ‘yan Shi’an Ali (a.s) da kuma irin matsayi mai girman gaske da suke da shi a wajen Allah Madaukakin Sarki.

Na biyu – Ya ce shi bai san wani tsohon nassi da ya jingina lafazin Shi'a ga Ali (a.s) kafin abkuwar fitina ba...' A baya mun ambaci fitattun nassosi daga Ma’aiki (s.a.w) wadanda suka sanya lafazin Shi'a ga mabiya Ali (a.s) suka kuma ba su siffofi masu girma da daukaka, lamarin dai shi ne mai girma bai yi bincike sosai ba ne da ya gansu.

Na uku – Ya ce wai Imam Ali (a.s) ba shi da wata jama’a ta ‘yan Shi'a fitattu kafin fitina da ma bayanta a lokacin halifancinsa, hakan ma dai akwai abin dubi cikinsa saboda Imam Ali (a.s) yana da zaunannun ‘yan Shi'a, daga cikin manyan sahabban Manzon Allah (s.a.w) irinsu Ammar bn Yasir da Abu Zar da Hijr bn Adi da Maitham al-Tammar, da Rashid al-Hijri da sauransu. Sayyid Muhsin al-Amuli cikin littafinsa ‘A’ayan al-Shi'a’ ya ambaci cewa mafi yawa daga cikin sahabbai sun kasance tare da Imam Ali (a.s) a lokacin waki’ar Siffin. Akwai sahabbai Ansarawa (mutanen Madina) 87 tare da shi da kuma sahabbai 900 wadanda suka shaidi Bai’at al-Ridhwan. Adadin sahabban da suke tare da shi sun kai 2,800. Bisa ga abin da al-Amuli ya fadi Imam Ali (a.s) yana da sanannu kuma fitattun ‘yan Shi'a.

6 - Barnar Delweis

Shi kuwa baturen nan Bernar Delweis yana ganin Shi’anci ya kafu ne bayan kashe Imam Amirul Muminin Ali (a.s) da shahadar Imam Husain (a.s) wadannan abubuwa biyu suna da tasiri wajen bayyanar Shi’anci mai akidar yunkuri da bayyanar Imam Mahdi. Wannan ra’ayi ne maras tushe saboda kamar yadda muka ambata Shi'a ta kafu ne tun zamani Ma’aiki (s.a.w), sai dai kawai ta yadu ne lokacin halifancin Imam Ali (a.s) saboda mutane sun ga adalcin da ya aiwatar da kuma damuwar da yake nunawa ga manufar al’umma gaba daya, da kuma irin ilimin da yake da shi, ta yadda hatta mafi yawa daga cikin musulmi sun yi amanna da cewa ya gaji dukkan kamala ta annabawa da ilmummukansu.

Malik al-Ashtar cikin hudubarsa yana cewa:

“Ya ku mutane! Wannan – wato Imam Ali (a.s) – shi ne wasiyyin wasiyyai kuma magajin ilimin Annabawa”[8].

Kamar yadda daga cikin muhimman dalilan yaduwar Shi’anci tsakanin musulmi shi ne shahadar jikan Ma’aikin Allah (s.a.w) wato Imam Husain (a.s) wanda ya fuskanci azzalumin sarkin lokacinsa Yazid bn Mu’awiyyah da nufin kafa hukumar Alkur’ani da adalcin Musulunci da rarraba alherorin Ubangiji ga fakirai da marasa shi da kawo karshen dukkan nau’oi na koma baya a duniyan musulmi. Saboda tabbatar da wannan gagarumar manufa ne ya yi shahada amincin Allah Ya tabbata a gare shi cikin mafi munin yanayi da tarihi bai taba ganin irinsa ba. Hakan ya sosa zukatan duniya, da dama suka rungumi Shi’anci da koyarwar Ahlulbaiti (a.s).

A nan ne za mu dakata kan magana kan kafa Shi’anci, a bahasi na gaba kuma za mu ambaci hujjojin da suke tabbatar da abin da muka fadi na cewa Shi’anci ya kafu ne tun zamanin Manzon Allah (s.a.w).

 

AMINCIN ALLAH YA TABBATA GA MANZO DA ALAYENSA TSARKAKA

Munir Muhammad Said

 

 

[1]- Al-Abr.

[2]- Al-Fasl fi al-Milal wa al-Nihal, 2/80.

[3]- Al-Firak al-Mutafarrika baina Ahl al-Zaigh wa al-Zandikah, shafi na 6.

[4]- Al-Fehris, shafi na 175.

[5]- Suratul Kasas 28:15.

[6]- Suratus Saffat 37:83.

[7]- Al-Fitnat al-Kubra, 2/601-603.

[8]- Tarikh al-Ya’akubi, 2/151.

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)