Muassasar alhasanain (a.s)

Tattaunawa Ta Tara

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
TATTAUNAWA TA TARA A yau na bude wannan shafin "nana_fatima" sai na ga wannan abin mamaki na hujumi kan masoya Ahlul Baiti (a.s) sai na ga ya kamata in tofa albarkacin bakina; musamman duba zuwa ga cewa; wasu miyagun akidu sun shigo da suke nuni da raini ga Ahlul Baiti (a.s) da matsayinsu. Mai magana ya yi wa rubutunsa taken: ((HATTARA DAI MUSULMI 2!!)) sannan sai ya ci gaba da cewa: ((A rubutu na da ya gabata ya tada hankalin da yawa daga mabiya Addinin Shi'a na wannan majalisa kai harma da yan'uwa Musulmi wayanda basu gama gano sharrin Addinin Shi'a ba har suke daukarsa wani bangare ne daga Addinin Musulunci kamar yadda yahudawa da kiristoci suke rayawa cewa su addinaine haka shian'ci yake a matsayin addini mai zaman kansa)).
Don haka nake cewa da shi: Babu wani wanda hankalinsa ya tashi sai kai da ka ga amsa gamsasshiya kan abin da kake kira sunnanci bisa karya, domin sunnaci yana girmama Ahlul Baiti (a.s) amma sai muka ga naka sunnacin yana kyamar tafarkinsu. Da haka ne sai muka gane irin naka sunnacin yana goyon bayan Banu Umayya ne makiya aali Muhammad (s.a.w).
Sannan rashin basira ya sanya ka ganin Shi'a suna ganin kansu a matsayin wani addini mai zaman kansa alhalin Shi'a su ne hakikanin musulmi masu biyayya ga manzon Allah da dukkan abin da ya zo da shi, wannan ne ma ya sanya su duk wani abu da wani ya haramta indai ba manzon Allah (s.a.w) ba ne to a wurinsu batacce ne domin shi ne Allah ya aiko. Idan ka isa ka kawo hukuncin manzon Allah guda daya da Shi'a suka canja!
Sannan ba mu yarda da mugaladar da kake yi ba ta wakiltar sunnanci wallahi babu wani wakiltar sunnaci da kake yi domin Sunna suna son gidan Annabi (s.a.w) kuma suna girmama Shi'a mabiyansu. Amma idan kana nufin Sunna (la'antar Imam Ali (a.s)) da ake kira Sunna da kuma jama'a (wato ittifakinsu kan kin jagorancin alayen Muhammad (s.a.w) da yardarsu da jagorancin Banu Umayya wanda Hajjaj yake cewa shekarar arba'in ita ce shekarar Sunna) to na yarda kai mai kare Sunna ne, domin asalin "Sunna da jama'a" ke nan. Kuma da wannan ne sauran ahlussunna ba su yarda cewa su Ahlussunna walja'ama ba ne, har ma ya kasance kalma ce da ake gaya wa 'yan hadisi a akida masu tunanin hashawiyya kan Allah.
Amma rashin gano sharrin Shi'anci daga sauran musulmi wannan yana nuna kyakkyawar niyyarsu ga son Ahlul Baiti (a.s) da tafarkinsu ne sabaninka da ire-irenka, amma kuma daukar addini mai zaman kansa wannan ka yi wa Shi'a kage ne, sai ka nemi afuwarsu ko ka koma da nauyin zunubin haka ranar kiyama randa babu wani wanda zai maka afuwa sai abin da ka girba.
Amma da yake cewa: ((Wannan ra'ayi nawa zan kareshi a yau da tarin dalilai da zan kawosu a kasa kuma insha Allahu har mai ruduwa zai gane cewa Shi'a addini ne wanda yayi hannun riga da Addinin Allah na Musulunci, nayi alkawarin a wannan rubutun nawa bazan kawo wata hujja ba ko guda daya daga litattafan Musulunci, zan shiga littattafan addinin Shi'a ne na kawo hujjojina, inaso ku bini cikin nutsuwa. Dalilan da suka nuna Shi'a addini ne mai zaman kansa ba kungiya bace daga kungiyoyin Musulunci)). Sannan sai ya ba shi take kamar haka:
((1) Sabaninsu da Musulmi Akan Allah (SWT): yana mai yin bayani kamar haka: ((Ni'imatullahi Jaza'iri Azzindiki yace acikin littafinsa Anwarul Nu'umaniyyah Mujalladi na biyu shafi na 278 "Babu hada da "Musulmi ba" akan Allah ko akan Annabi ko akan Imami saboda su "Musulmi" suna cewa Allansu shi ne ya aiko Muhammadu da Annabta kuma Abubakar ya zama halifan Annabin, mu kuwa "Yan Shi'a" mun san wannan ba Ubangijinmu bane kuma Annabin nasu ba Annabinmu bane, mu muna cewa du ubangijin da Halifan Annabinsa ya zama Abubakar to Ubangiji ba Ubangijinmu bane kuma Annabinmu ba Annabinmu bane". To ai Magana ta kare domin ga daya daga cikin masadir na Addinin Shi'a ya fayyace komai to ni Adamu meye laiifin da nayi dan na fadi abin da na gani a rubuce ko bani da hakkin fadar ra'ayi na, ayi mini adalci mana)).
Sai in ce masa: Ka kawo magana da a irinta ne Imam Ali (a.s) yake gaya wa Hawarijawa cewa "Kalmar gaskiya da ake nufin barna da ita" yayin da suke cewa "Babu hukunci sai ga Allah", domin ka kawo magana amma ba ka kawo fuskar maganar ba: domin wannan ya yi kama da ka ce ne "Ubangijin da Annabi Isa (a.s) dansa ne to wannan ba ubangijinmu ba ne" kamar yadda Imam Ridha (a.s) yake gaya wa wani kirista cewa: "Isanku" a maganar da yake yi da shi a wata munakasha, wato ba Isanmu (a.s) ba. Ka sani haka wannan magana take: Mu ba yi imani da ubangiji ko annabin da ba shi da hadafi ba, ta yadda zai tafi ya bar al'umma bai nuna musu wanda zasu yi riko da shi ba, har ya sanya kashe-kashe tsakaninsu kuma daga baya suka yi rigima a Sakifa aka kuma wulakanta 'ya'yan annbinsa duk saboda wannan lamarin, sannan kuma masu karbar jagorancin al'umma suka nuna ba su san ma makomar al'umma ba da nadamar abin da suka yi na jagoranci da cewa kuskure ne kuma sharri ne da Allah ya kare musulmi sharrinsa, sannan daga karshe kuma ta sabbaba nisantar Kur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w) da aalyanesa.
Mu mun yi imani da Allah (s.w.t) da Annabi (s.a.w) masu hadafi ne wadanda suka komar da mutane zuwa ga littafin Allah da aalayen Annabi Muhammad (s.a.w) kuma suka shiryar da al'umma ta yadda babu wani abu sai da suka yi bayaninsa a addini, suka shelanta musu Ali (a.s) a matsayin mai maye gurbin Annabi (s.a.w).
Amma da kake cewa: ((2) Waye Allah a Addinin Shi'a
Nasu Allah sun bayyana mana shi a littattafansu babu wani boye – boye, kuma idan ka kalli siffofinsa da yadda suke kwatantashi zaka ga yasha banban da Allah mai girma da daukaka, ga wasu yan misalai. Muhd Takiyyi (LA) ya fada a littasinsa Sahifatul Abraru Mujalladi na biyu shafi na 140 "Allah " na addinin Shi'a" yana ziyartar Husaini dan gidan Ali ya mika masa Hannu suyi musafaha ya zauna akan gadonsa". Tirkashi aiki ga mai kare ka kunji fa irin nasu Allan, haka Ziya'uddini Mahmud yace a littafinsa Kitabul Usulul Sitta Ashara shafi na 204 "Allah "na addinin shi'a" yana sauka a ranar Arfa a farkon zawali akan rakuminsa yana kewaya tsakanin mutane dama da hagu cinyoyinsa suna taba mutanan na Arfa" to duk wanda yayi imani da irin wadannan bayanan da suka gabata ba Musulmi bane, Kur'aninmu mus'hafi Usman da Hadisanmu da maganganun malamai da yawan gaske sun tabbatar da haka, kai du mutumin da hankalinsa yake garau ai yasan haka)).
Sai in ce maka: A nan ma ka ci kasa, kuma ka fadi warwas: ina ganin yana da kyau ka yi ilimi tukun sannan sai ka yi magana, ka daina magana kamar Aku da sai dai ya maimaita lafuzzan masu suka, bai san me suke nufi ba, Ka sani mawallafin wannan littafin abin da ya nakalto ya nakalto ne alhalin yana mai dogaro da abin ya karbo daga malamansa kuma ya rubuta, wannan kuwa yana nuna adalcinsa ga Sunnanci, ka sani Jaza'iri ya zamanto Shi'a ne daga baya, domin da farko ya kasance malami ne a sunnacin kafin ya karbi mazhabar Shi'a.
Koda yake wasu abubuwan da ka kawo suna nuna son rai ne, domin duk jahilci akwai sanin kage babu kyau, idan dai kana neman tsarki ga Allah to ka koma koyarwar Ahlul Baiti (a.s), ina ganin kana son nuna abin da ka yi imani da shi game da Allah ne sai kake neman dorawa kan Shi'a. Hakika kun kawo cewa Ahmad Bn Hambal yana gaisawa da Allah da hannu kamar yadda ya zo daga Manakibu Ahmad na Ibnul Jauzi.
Amma game da gaisawa da hannu da kuma rungumar juna da ubangijin talikai kun kawo cewa hakan zai yi da shi da Umar kamar yadda kuka karbo daga Ka'abu cewa farkon wanda zai yi rungume Ubangiji a ranar lahira shi ne Umar, kuma farkon wanda zai yi hannu da shi Umar. Almustadrak 3, shafi: 84. Ibn Majah 1, shafi: 39. da Kanzul Ummal, j 1, shafi: 578.
Hada da cewa mu ba ma kawar da ruwaya game da siffofin Allah madaukaki sai idan ta ci karo da Kur'ani da hankali, sannan kuma a mayar da ita ga muhkamar aya, kuma ta kasance babu tashbihi kuma babu ta'adili sai dai tanzihi.
Irin mahangarku game da Allah madaukaki da a koyarwarku da aka dauke shi da matsayin siffofi da ba su cancanci she ba, har kana da bakin magana kan masu tsarkake shi daga tashbihinku, kuna dauki Allah kamar haka:
Kamarsa da Annabi Adam (a.s) da tsayinsu irin daya (fatawa bn Baz, j 4, shafi: 226)
Kasancewarsa wani saurayi ne mai takalma biyu, mai gashi har baya, da korayen kafafu, yana da takalman silifa biyu na zinare, da wata ado ta zinare a fuska. (Ta'alikin Albani ga sunnar ibn Abi Asim No. 471)
Zaman Ubangiji kan al'arshi kuma yana da girma daidai al'arshin ne, sai dai al'arshin ya fi shi girma da kadan kamar girman 'yan yatsu hudu ne. (firdausil akhbar, j 1, shafi: 219). A littafin Akadul farid (j 6, shafi; 208) kuma macijiya ta kanannade al'arshin. Wannan kuwa yana nuna ta fi al'arshin tsawo sosai.
Zaman Allah kan kursiyyu: (tafsiru Dabari: j 3, s: 7)
Al'arshinsa kuwa yana kan dabbobi ne, daya mutum daya sa, daya mikiya, daya zaki. (hayatul haiwan, j 2, s: 428) da (Jahiz, kitabul haiwan, j 6, shafi: 221). Da wasu littattafai kamar al'isaba 549. tafsirud Dabari.
A wurinku duk Allah zai rube ya halaka –wal'iyazu bil-Lah! Sai kawai fuskarsa zata rage. Albani (fatawa albani: shafi: 522, 523) wani abin mamaki Albani ya yi kakkausan suka ga Buhari saboda ya yi tawilin fuska da mulkin Allah (s.w.t). a wannan ayar: "Kulli shai'in halikun illa wajhah" wanda kuwa ubangijinsa zai halaka gaba daya sai fuska ba dai ubangijin da ya aiko manzanni ba ne ubangijinsa! A nan muna iya gani a fili yake cewa: "Kuna hana tawili amma kuna yin sa inda kuka ga dama, kun gwammace ku sanya Allah zai mutu ya halaka ya kare da ku yi tawili, amma saboda gyara makantar Bn Baz kun yi tawilin "Faman kana fi hazihi a'ama, fahuwa fil akhirati a'ama wa'adhallu sabila" domin ku yi kariya daga makantarsa a lahira. Don me ba ku mayar da ayoyin siffofin Allah zuwa ga muhkamata ba, amma kuka mayar da siffofin dan Adam zuwa ga muhkamata kamar "innaha la ta'amal absar…" domin ku yi kariya ga malaminku.
Da ya hau kan al'arshi saboda nauyinsa sai da arshi ya yi kara. Wal'iyanzu billah!!!
Irin wadannan siffofin ne da kuka ba wa su Ka'abu dama da Tamin bn Aus, da Abdullahi bn Salam suka kawo koyarwar kiristanci da yahudanci cikin akidunku sakamakon kun yi nisa da alayen Annabi sai kuka fada cikin wadannan tarkuna.
Ya zauna kan al'arshi ya dora kafa daya a kan daya yana mai jingina kan al'arshi ya kishingida sannan daga baya sai nauyinsa ya tsattsaga sammai. (tafsirud Dabari, j 25, shafi: 6).
Allah yana da 'yan yatsu hudu, ko biyar ko shida da sabanin malamanku a kai. Duba daya daga ciki a Buhari, j 5, shafi: 33. da kitabut tauhid, shafi: 225, amma shafin ya yi daidai da wanda Muhammad Salim malamin Azhar ya gyara.
Akidarku ta cewa; ana ganin Allah da idanu kamar wata. Buhari; 1, s: 195.
Pop ya soki Kur'ani saboda tsarkake Allah ya goyi bayan akidarku ta sanya shi jiki saboda ta yi daidai da kiristanci. Duba littafin Al'uburu ilar Raja' a hirarsa da dan jaridar Italia.
Ubangijinku saurayi ne mai nadadden gashi dunkulalle.
Babban malam Ayatul-Lahi Kurani Allah ya tsawaita rayuwarsa yana cewa: "Kun ba wa Allah madaukaki gabobi: sau da yawa "yadullahi fauka aidihim" kuka ki tawilinta da cewa lallai dai hannu ne sosai. Amma duk da tsananin kin tawili da kuke yi idan aka zo da wani abu da ranku ba ta so sai ka ga tawili sosai: ga shi manzon Allah yana cewa: "man kuntu maulahu fa Aliyyu maulahu" "Duk wanda nake jagoransa to Aliyyu (a.s) ma jagoransa ne" a nan kam sai ga tayar da jijiyar wuya domin yin tawili iyakacin karfinku".

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
May, 1, 2009

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)