Muassasar alhasanain (a.s)

Kyawawan Halaye

1 Ra'ayoyi 01.0 / 5

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Dabi'u Na Gari Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai don ya cika kyawawan dabi'u, Ubangijin kasa da sama ya siffanta shi da "Hakika kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" . Wanda mutane masu neman daukaka suke koyi da shi.
Da Allah ne muke neman taimako a kan kawukanmu da kuma dukkan abin da ya halitta gaba daya, tsira da aminci su tabbata a kan wanda ubangijin halitta ya siffanta shi da cewa shi yana da kyawawan dabi'u, sai ya aiko shi domin ya cika mafi kyawawan dabi'u, Annabin rahama da mutuntaka Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s).
Al'amarin kyawawan dabi'u al'amari ne na 'yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama'a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu'amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah ya yi umarni.
Don haka ne ma kyawawan dabi'u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu'amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu'amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka'idar "Yin mu'amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu'amala da kai". Ko kuma "Kamar yadda ka yi za a yi maka" .
Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi'a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al'ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.
Wannan shi ne abin da ake kira "Kyawawan dabi'u wato Akhlak" Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha'inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi'u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi'u na nazari.
Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da 'yan'uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi'u na aiki.
Da mun kula mun yi la'akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi'u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi'u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: "Lallai kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" .
Ashe kenan kyawawan dabi'u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen 'yan Adam Muhammad (s.a.w).
Wannan makala da ta kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan Adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi'un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko'ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci, ta hanyar mutane da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga garesu.
Musulunci addinin kyawawan dabi'u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna.
Muna rokon Allah madaukaki mai rahama ya sa mu dace da bin dabi'un musulunci, ya kuma ba mu ikon bayyanar da su ga mutane a wannan gajeriyar makala, ta zama kofa ga kowane mutum; domin shiga da sanin kyawawan dabi'un musulunci. Kuma muna rokon Allah ya karbi wannan aiki da kuma neman addu'a daga muminai, ya kuma sanya ladan rubuta wannan makala ga kakannina kamar Shaikh Sa'id da malam Husain da shaikh Usman.
Kyawawan Dabi'u
Kyawawan dabi'u su ne ruhin shari'a, kuma asasin addini, babu wani Annabi da ya zo sai da ya yi kira tsakanin mutane da kyawawan dabi'u, da kuma tilascin tsarkake su daga abin da yake iya kai su ga aikata munanan dabi'u, da kuma nesantar da su daga abin da yakan iya lalata hadafinta, sai ya zana mana tafarki da hanya, ya gina mana dokoki da zamu yi amfani da su domin kawo canji ga mutum zuwa ga mafi kamalar samuwa wacce mutum zai dogara da ita domin ya kai ga matsayi mai girma na kyawawan halayen, ya kuma zamanto daga zababbu tsarkaka daga bayinsa.

Ilmin Kyawawan Dabi'u
Ilmin kyawawan dabi'u ilmi ne da yake da ma'auni da za a iya dogara da shi, shi ne tattararrun dokoki da ya kamata dabi'ar dan Adam ta kasance a kanta bisa wadannan dokokin kamar yadda aka gindaya a zance ko a aiki ko a zuciya. Da wadannan ma'aunai zamu zana hanyar kyawawan dabi'u abin yabo, mu kuma yi kokarin iyakance hadafinsu da abubuwan da suka ginu a kan su.

Kyawawan Dabi'un Musulunci
Dabi'un musulunci su ne tattararrun zantuttuka da ayyuka na zahiri da na badini da suka doru bisa ka'idoji, da kuma ayyuka madaukaka da ladubban da suka doru a kansu, wadanda suka dogara a kan akida da shari'ar musulunci da dogaro mai karfi daga kur'ani mai girma da sunnar Manzon Allah (s.a.w) da imamai tsarkaka (a.s). Kyawawan dabi'u a musulunci ba komai ba ne sai bangare na addini, kai shi ne kashin baya da ruhin addini ma .


Hadafin Kyawawan Dabi'u
Hadafin kywawan dabi'u shi ne kare ayyukan mutum, na zahiri da na badininsa da kuma tsarkake tunaninsa da samuwarsa daga karkacewa; wato hadafin shi ne samar da mutum ko kuma al'ummar da take takawa zuwa ga kamala, ta kuma tsayar da adalci, da rikon amana, da taimakekeniya, da kuma kama hannun juna domin kare rayuwar al'umma daga fadawa cikin fasadi da zalunci da sauran miyagun al'adu da dabi'u.
Da lizimtar kyawawan dabi'u ne mutum ko al'umma zata samu kariya daga karkacewa da kuma lizimtar tafarkin shiriya na gaskiya. Hadafin ilimin kywawan dabi'u bai takaita a kan daidaikun mutane kawai ba, ya hada har da al'ummu da jama'u daban-daban, ta yadda kyawawan dabi'u zasu mamaye rayuwarta da siffofinta domin kai wa ga mafi daukakar ci gabanta.
Wani baiti yana cewa:
Al'umma kawai ita ce kyawawan dabi'unta matukar ta wanzu.
Idan kuwa al'umma ta kau to kyawawan dabi'unta ne suka kau.

Madogarar Asasin Kyawawan Dabi'u
Kafin mu yi magana kan asasin akhlak na musulunci zamu yi nuni zuwa ga cewa akwai abubuwa da yawa wadanda suke madogarar asasin kyawawan dabi'u, daga ciki akwai:
- Zuciyar mutum wacce take tunkuda shi zuwa tafarkin alheri, kuma take hana shi aikata sharri da mummuna.
- Dabi'ar zuciya da take tunkuda mutum zuwa ga sadaukar da dukkan maslaharsa saboda maslahar mutane.
- Hankali da yake son kamala, ya ke kuma riskar mummuna da kyakkyawa a aikace.
Dangane da akhlak na musulunci muna ganin yana da manyan madogara na asasi guda biyu manya, su ne:
1- Hankali
2- Annabin rahama (s.a.w) da Ahlul baiti (a.s)

1- Hankali
Hankali; Ana auna ayyuka da hankali ne, kuma da shi ne mutum yakan kai zuwa ga sa'ada da kamalar rayuwa ta lahira, da hankali ne muke riskar dalilin halitta, da kuma riskar abubuwa masu daraja, muke kuma kokari zuwa ga mafi kyau ma fi wanzuwa, da shi ne muke neman tafarkin sani, da hanyoyin ibada, Imam Assadik (a.s) ya ce: "Mafi kamalar mutane hankali shi ne mafi kyawunsu dabi'a" .
Dogaro da wannan hadisin muna iya cewa; hankali na aiki shi ne abin nufi, ba hankali na nazari ba, in Allah ya yarda idan na kammala littafina wanda yake magana kan kashe-kashen hankali da matsayin kowanne, to a nan mun kawo bayani game da hankali dalla-dalla.
Hankali a nazarinmu shi ne madogara ta asali na kyawawan dabi'u, idan aka rasa shi sai dabi'ar halin dabbanci ta mamaye mutum.

2- Annabi Mai Girma Da Ahlul Bait (a.s)
Annabi mai girma ya zo ne domin ya tsarkake mu ya cika mana kyawawan dabi'u yayin da yace: "Kawai an aiko ni ne domin in cika kyawawan dabi'u" .
Shi ne mafi kamalar mutane, kuma babu wani daga halittu da ya kai inda ya kai, shi ya sanya ubangiji madaukaki ya fada yana mai yabonsa: "Lallai kai kana kan halayen dabi'u masu grima ne" .
Abin da ya hau kanmu shi ne mu yi riko da kyawawan dabi'unsa, mu yi koyi da shi domin shi ne abin koyi kuma madogara garemu a kyawawan dabi'u, har ma a kowane fage.
Amma Ahlul Baiti (a.s) su ne wadanda suka gaji ilimn annabawa da na karshensu Muhammad (s.a.w), kuma mutane sun gani kuma sun ji kyawawan dabi'un alayensa (a.s) wancce take iya tuna musu kyawawan dabi'unsa (s.a.w). Da sannu zamu ambaci wasu daga kyawawan dabi'unsu a wannan littafin namu;
Daga ciki;
"Ya zo cewa imam Hasan da Husain (a.s) sun wuce wani tsoho yana alwala bai iya ba, sai suka yi kamar suna 'yar jayayya a kan cewa; wanene yafi iya alwala a cikinsu, wannan kuwa sun yi haka ne domin su koya masa yadda ake yin alwala, sai kowanne ya ce kai ne ba ka kware ba sosai, sai suka ce: ya kai wannan tsoho yi mana hukunci, sai kowannensu ya yi alwala sannan sai suka ce: Waye a cikinmu ya fi iyawa? Sai ya ce: Ai duk kun iya alwala, sai dai wannan tsoho jahili shi ne bai iya ba, yanzu kam ya koya daga gareku" .
Lura da yadda Ahlul Bait (a.s) suka shiryar da wannan tsoho domin ya zama mana darasi a wajan yadda ake mu'amala tare da manyan mutane.


Kyawawan Dabi'u
Kyawawan dabi'u su ne halayen rai da suke sanya ta aikata kyakkyawa ga mutane, da kuma dadada musu a magana, da aiki, da nufi, da kuma dudanya, da sakin fuska, da makamantansu.
Muna iya cewa kyawawan dabi'u sun shafi gyara kai ne domin a samu daidaikun mutane na gari a cikn al'umma don samar da jama'a saliha mai wadata.
Allah da Manzonsa sun yabi kyawawan dabi'u da kalmomi masu girma, Allah yana cewa: Lallai kai kana da halayen kirki nagari manya. Kyawawan dabi'u suna da alamomi kamar sakin fuska, da magana mai dadi, da zaman lafiya da mutane .


Kwaskwarima Da Ado
Bahasi na gaba mai zuwa zai kasance ne game da kwaskwarima, domin rai tana bukatar wanka da sabulu na ma'ana don wanke kazantar ma'ana da kawar da daudar ma'anoni da takan nesantar da mutum daga siffantuwa da kyawawan dabi'u. Kuma tana bukatar ado kamar yadda jiki yake bakata, kamar a sanya mata turare na ma'ana domin nisantar daudar ma'anoni da kazantar munanan halaye don cimma burin kai wa ga kamala da siffantuwa da kyawawan dabi'u.
Abu ne sananne ga mutane cewa; idan mutun yana warin dauda sai ya shafa mai, ya sanya kaya masu kyau, ba tare da ya yi wanka ba ya kawar da kazanta da daudar da suke jikinsa, wannan ba ya hana warinsa ya fito a fili.
Amma da zai yi wanka da sabulu, sannan sai ya shafa mai ya sanya turare, ya kawo kayansa masu kyau ya sanya sai ya zama gwanin sha'awa. Haka ma munanan dabi'u da kyawawa suke, wato sai an yi kwaskwarima ta hakika sannan sai kuma a kawo kayan ado da kayan kanshi a sa.
Mun kira wanka da kawar da dauda da kazanta daga jiki ba tareda an shafa mai an sanya turare ba da kwaskwarima, domin yin hakan ba ya zama cikar yin ado, domin idan wani ya yi wanka amma sai ya yi furu-furu saboda rashin shafa mai, kuma ya kawo kayan da ya cire masu dauda ya sake sanyawa a jikinsa har yanzu bai yi adon da ake bukata ba, don haka wanka da kuma kwalliya da ado a hade su ne suke cika kamalar tsafta. Amm dole ne sai an fara yin abin da muke kira kwaskwarima sannan sai kuma a yi ado.
Misali, idan mutum ya bar karya kamar ya wanke daudar jikinsa ne, idan kuma ya yi gaskiya kamar wanda ya sanya kayan ado da na kanshi ne. Shi ya sa, da yana karya, yana kuma gaskiya, da sunansa makaryaci, kamar yadda wancan yake warin dauda duk da kuwa ya sanya kayan ado domin bai yi wanka ba. Ko kuma ya yi wanka amma sai ya mayar da kayan dauda a jikinsa wadanda suke wari. Shi ya sa barin mummuna muke cewa da shi kwaskwarima, aikata kyakkyawa kuma muke cewa da shi yin ado.
Musulunci yana mai matukar kiran mutum domin ya yi kwaskwarima ya wanke daudar nan ta cututtukan rai; kamar karya, da sata da ha'inci, da riya, da sauransu. Kuma hadisai da dama sun zo suna masu hani da tsanani a kai da gargadi domin barin wadannan miyagun halayen.

Ado Da Kaye
Kamar yadda muka yi nuni cewa mutum yana bukatar yin kwaskwarima kafin ya yi ado, sa'annan muka yi nuni da wasu daga kwaskwarima kamar yadda ake iya gani a bahasin da ya gabata, a yanzu kuma lokacin ya yi da zamu yi nuni da wasu daga abubuwan da ya kamata a yi ado da su domin mutun ya kai ga kamalar siffantuwa da kyawawan dabi'u da suka cancanci dukkan mutum kamili na gari ya siffantu da su.
Addinin musulunci ya zo ne domin cika wadannan kyawawan dabi'u, kuma shi addini ne na kamala da kiran mutane da kyawawan dabi'u ba da zancenmu ba ko fatar baki kawai, mafi yawan musulmin farko da suka musulunta sun karbi addinin ne ta hanyar kyawawan dabi'un annabi mai girma da suka gani.

Tuba
Tuba ita ce barin sabo na aiki ko na zance ko na tunani wacce take tare da barin sabo a lokacin tuba da niyyar barinsa a lokaci mai zuwa, da nadamar abin da ya rigaya, kuma da mayar da hakkin da aka ci a baya.
Tana daga cikin mafi girman dabi'a kyawawa, kuma kofa ce da Allah ya bude ta ga bayinsa har alkiyama ta tashi, da Allah ya rufe kofarta da babu wani daga bayinsa da zai rabauta.
Tuba wajibi ne a hankalce da shar'ance daga dukkan sabo karami ko babba, na abin da ya shafi hukuncin Allah ne ko na hakkin mutne ne. Rashin tuba yana kai wa ga tabewar mutum duniya da lahira da kutsawa cikin sabo iri-iri.
Tuba tana da falala mai yawa da ba ta kirguwa, tana jawo son Allah ga mutum, tana canza sabo da mummuna ya koma kyakkyawa, mala'iku suna yabon mai tuba suna yi masa addu'a, masu tuba 'yan aljanna ne, tuba tana jawo tsawon rayuwa da yalwar arziki, mai tuba karbabbe ne wajan Allah, Allah yana yafewa mai tuba ko menene zunubinsa, sannan kuma dukkan bala'o'i da dan Adam yake gani sakamakon rashin tuba ne.

Sharuddan Tuba
" Nadamar abin da ya bari na alheri
" Nadamar abin da ya yi na sabo
" Mayarwa bayi hakkokinsu
" Rama duk wani wajibi da ya bari
" Zagwanyar da naman jikinsa da ya ginu da haram
" Dandanawa jiki zafin biyayya kamar da yadda ya dandani dadin sabo

Gaskiya
Gaskiya ita ce; yin daidai da hakikanin al'amari a zance, da aiki, ko nufi, kuma tana daga cikin siffofi madaukaka da suke da falala mai yawa wadanda ya wajaba ga mutum ya siffantu da su. Ayoyin kur'ani da ruwayoyi masu yawa sun zo game da yabon masu gaskiya.

Kashe-Kashen Gaskiya
" Gaskiya ta zance; kamar bayar da labarin hakikanin abin da ya faru a magana
" Gaskiya ta niyya da nufi; kamar tsarkake zuciya da aiki don Allah, ko nufin aikata alheri da gaske
" Gaskiya a ayyuka kamar cika alkawari da daukar matakai na daidai
Gaskiya tana daga cikin abubuwan da ake kimanta mutum da ita a wajan Allah (s.w.t), imam Sadik (a.s) yana cewa da mu: "Kada ku yaudaru da sallarsu, ko da azuminsu, saudayawa mutum yakan saba da salla da azumin har idan ya bar su sai ya ji ba dadi, amma ku jarrabi mutane da gaskiyar magana da bayar da amana ".
A wata ruwayar yana cewa: "Wanda harshensa ya yi gaskiya aikinsa zai tsarkaka" .

Kaskan Da Kai
Kaskan da kai; shi ne mutum ya ga kansa ta fuskacin kallo na kyawawan dabi'u, kamar kyautata alaka da mutane da rashin daga musu kai, da rashin ganin kansa sama da su, da sallama ga mutane. Kuma ruwayoyi masu yawa sun zo game da yabon wannan siffa mai kyau ta kamala.

Sakamakon Kaskan Da Kai
" Yaduwar soyayya da kauna tsakanin mutane
" Samun kwarjini da girma tsakanin mutane
" Aminci da zaman lafiya tsakanin mutane
" Biyayya da godiya ga mahallici mai girma
" Samun yaduwar kyawawan dabi'u abin yabo

Kaskan da kai yana daga siffofi madaukaka kamar yadda muke iya gani, amma a wasu wurare bai halatta a kaskantar da kai, kamar kaskan da kai ga mai kudi ba don komai ba sai don dukiyarsa, ko sarki domin sarautarsa kawai ko domin neman duniya a wajan wani. A irin wadannan wurare kaskan da kai yakan zama abin ki.
Kaskan da kai sifface da Ahlul Bait (a.s) suka shahara da ita suna masu koyi da kakansu Manzon rahama (s.a.w), ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w) shi ne ya fi kowa kaskan da kai, idan ya shiga waje yana zama karshen inda wurin zama ya kai, ya kasance yana kama aiki ga iyalansa a cikin gidansa, yana tatsar nono, yana dinke tufafi, yana gyara takalmansa, yana yin aikinsa da kansa, yana daukar kayansa kamar cefane daga kasuwa zuwa gida, yana zama tare da talakawa, yana cin abinci tare da miskinai.
Ya kasance (s.a.w) idan wani ya yi sirri da shi ba ya kawar da kansa sai wancan ya kawar da kansa, idan wani ya gaisa da shi ba ya cire hannunsa har sai wancan ya cire, wani bai zo masa ya tashi ya bar shi ba har sai shi wancan ya tashi, kuma yana fara wa da sallama ga wanda ya hadu da shi, yana fara mika hannu domin gaisawa ga sahabbansa, ba a taba ganin ya mike kafarsa ba tsakanin sahabbansa, yana girmama wanda ya shiga wajansa, ya kasance yana rarraba ganinsa tsakanin sahabbansa, ya kasance mafi yawan mutane a murmushi, mafi tsarkinsu zuciya .
Wata rana Imam Husain (a.s) ya wuce wasu miskinai suna cin abinci a kan wata tabarma tasu sai ya yi musu sallama, sai suka yi masa tayi sai ya zo ya zauna tare da su ya ce: Ba don abincinku sadaka ba ne da na ci tare da ku. Sannan sai ya ce: Ku tashi zuwa gidana, sai ya ciyar da su ya tufatar da su, kuma ya yi umarni aka ba su dirhamomi .
Imam Rida (a.s) wata rana ya sanya an kawo shimfidar abinci, ya tara masu yi masa hidima daga bakaken fata, (domin su ci) sai aka ce da shi, da ka ware wa wadannan abincinsu daban, sai ya ce: Kul! Hakika ubangiji daya ne, uwa daya ce, uba daya, kuma sakamako da ayyuka ne .

Shiryawa Da Daidaitawa Tsakanin Mutane
Abin da ake nufi da daidaita tsakanin mutane shi ne kusantar da su da kawar da abin da yake tsakaninsu na gaba da yankewa juna, da dawo da soyayyar da take a tsakaninsu. Wannan siffa ce madaukakiya da take kishiyantar annamimanci da haifar da fitina tsakanin mutane, kuma daidaita tsakanin mutane ya hada har da dukkan sabanin da yakan iya faruwa tsakanin dauloli, da kabilu, da kasashe, da kungiyoyi, kuma da tsakanin iyalai da daidaikun mutane.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Mutum bai taba aikata wani aiki mafi alheri ba bayan tsayar da farillai fiye da gyara tsakanin mutane, ya fadi alheri, ya haifar da alheri .

Rikon Amana
Rikon amana ita ce; kiyaye hakkoki kamar yadda Allah ya yi umarni, kuma wannan al'amari ne mai fadi da ya hada da hakkokin Allah kamar amanar addini, da ta kawukanmu, da kiyaye umarninsa da haninsa. Akwai kuma ta hakkokin mutane, kamar kiyaye dukiyoyinsu, da amanar makwabtaka, da ta 'ya'ya, da kula da iyali, ko na ma'abota amana. Kiyaye amana yana janyo alheri mai yawa, da arziki da wadata, da kubuta a duniya da lahira.

Tsafta
Tsafta ita ce; tsarkake jikin mutum da tufafinsa da dukkan abin da ya damfaru da shi na daga gidansa da wajan zamansa, da abin hawansa, da hanyarsa, da makarantarsa, da makamantan wannan. Allah mai tsafta ne mai tsarki, kuma yana son mai tsafta.
Musulunci ya tanadi hukunce-hukunce da suke karfafa yin tsafta da suka zo a babobin fikihu, kuma da akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo suna karfafa yin tsafta har sai dai suka sanya ta wani bangre ce ta imani, kuma ya karfafi mutane a kan yin tsaftar ruhi, da ta jiki, da ta waje. Idan muka duba tsaftar ruhi zamu samu a cikinta an yi umarni da wanke rai daga dauda abin da muka kira shi a baya da kwaskwarima, kuma da yin ado da kyawawan dabi'u kamar bahasin da muke cikinsa yanzu.
Ba sai mun kawo ruwayoyi ba a kan wadannan abubuwa da muke kiransu da ado ko abin da muka kira su da kwaskwarima, amma zamu iya nuni da wadansu abubuwan da ruwayoyin suka kawo, wadanda wasunus ruwayoyin suka yi nuni da suna kawar da talauci kamar haka;
a) Share gida
b) Kada a kwana a gida akwai shara
c) Aske gashin gaba da ciki da hammata
d) Yanke farce da datse gashin baki
e) Asuwaki da taje gashin kai
f) Tsarki don fitar bawali da maniyyi da jini
g) Tsarki domin fitar bayan gida
h) Wanke jiki ko kuma yin wanka

Fa'idojin Tsafta
Yin tsafta yana da amfani mai yawa ga mai tsafta kuma da jama'ar da take tare da shi, kuma yana sanya kusancin na kusa da shi gareshi, sannan yana kiyaye hakkin na jikinsa kamar matarsa ko mijinta da yin tsafta, da sauran amfononi da suke masu yawa na duniya ko na lahira, muna iya kawo wasu daga fa'idojin tsafta a takaice kamar haka:
a. Allah da Manzo suna son mai tsafta
b. Jin nishadi mai girma da jin dadin rai
c. Girmama mutane ga mai tsafta da kusantarsa
d. Rashin kyamar mutane ga mai tsafta
e. Girmama mala'ikun da suke tare da mai tsafta
f. Soyayyar mai tsafta a zukata
g. Mai kazanta yana cutar da mutane da warinsa
h. Tsafta tana kawar da cututtuka na jiki
i. Tsafta lada ce domin koyi da sunnar annabi ce
j. Tsafta tana nuna kimar mutum ne

Zamu ci gaba
13 Rabi'ul awwal 1427
23 Parbardin 1385
12 Afrilu 2006
 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)