Muassasar alhasanain (a.s)

Munanan Halaye

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Dabi'u Munana Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai don ya cika kyawawan dabi'u, Ubangijin kasa da sama ya siffanta shi da "Hakika kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" . Wanda mutane masu neman daukaka suke koyi da shi.
Da Allah ne muke neman taimako a kan kawukanmu da kuma dukkan abin da ya halitta gaba daya, tsira da aminci su tabbata a kan wanda ubangijin halitta ya siffanta shi da cewa shi yana da kyawawan dabi'u, sai ya aiko shi domin ya cika mafi kyawawan dabi'u, Annabin rahama da mutuntaka Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s).
Al'amarin kyawawan dabi'u al'amari ne na 'yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama'a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu'amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah ya yi umarni.
Don haka ne ma kyawawan dabi'u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu'amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu'amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka'idar "Yin mu'amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu'amala da kai". Ko kuma "Kamar yadda ka yi za a yi maka" .
Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi'a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al'ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.
Wannan shi ne abin da ake kira "Kyawawan dabi'u wato Akhlak" Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha'inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi'u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi'u na nazari.
Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da 'yan'uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi'u na aiki.
Da mun kula mun yi la'akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi'u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi'u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: "Lallai kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" .
Ashe kenan kyawawan dabi'u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen 'yan Adam Muhammad (s.a.w).
Wannan makala da ta kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan Adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi'un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko'ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci, ta hanyar mutane da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga garesu.
Musulunci addinin kyawawan dabi'u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna.
Muna rokon Allah madaukaki mai rahama ya sa mu dace da bin dabi'un musulunci, ya kuma ba mu ikon bayyanar da su ga mutane a wannan gajeriyar makala, ta zama kofa ga kowane mutum; domin shiga da sanin kyawawan dabi'un musulunci. Kuma muna rokon Allah ya karbi wannan aiki da kuma neman addu'a daga muminai, ya kuma sanya ladan rubuta wannan makala ga kakannina kamar Shaikh Sa'id da malam Husain da shaikh Usman.

Munanan Dabi'u
Mummunar dabi'a ita ce, karkacewar mutum daga tafarkin ayyuka na gari, da yake sanya shi ya zama mai hali maras kyau, mai kausasawa ga mutane, da kuma tsanantawa garesu.
Munanan halayen suna sanya mutum ya zama abin ki wajan mutane da ubangijinsa. Kuma wannan kan iya sanya masa kunci a rai da kekashewar zuciya, da takura a rayuwa, da wulakantar da kai, da zubewar mutunci, da sauran abubuwan da sukan iya koma masa da sharri.

Dalilan Munanan Halaye
1. Talauci: Zogi da zafin rashi sukan iya bata dabi'un mutum.
2. Bakin ciki madawwami da daukar duniya da zafi, wannan yana sanya mutum ya zama mai munanan halayen.
3. Wadata da Jin isa: wannan ma yakan sanya girman kai, kuma kur'ani mai girma a surar Alak ya yi nuni da wannan.
4. Matsayi kamar mulki ko shugabanci, wannan ma yakan iya kawo karkacewa daga kyawawan dabi'u.
5. Kadaitaka da warewa daga cikin mutane, wannan ma yana iya kai mutum ga yakunewar fuska saboda tunani da bakin ciki da yakan iya kai wa ga lalacewar halaye .
6. Sha'awa: wannan ma tana iya sanya mutum ya zama mai yawan fushi da rawar jiki, da yawan bakin ciki, da kuma kokarin kutsawa cikin haram.
7. Raunin da yakan samu mutum har ya taba lafiyarsa ta yadda jijiyoyinsa sukan ba shi sako na gajiyawa har ya zama mutum maras hakuri da juriya, da yawan fada da mutane, ko takurawa kananan yara, ko kuma gazawa ga tafiyar da al'amarin al'umma.
Maganin Munanan Dabi'u
1. Nisantar masu munanan halayen.
2. Tuna muninsu da sakamakonsu na duniya da lahira.
3. Tuna kamalar annabawa da kyawawan dabi'unsu da kokarin koyi da su.
4. Tarbiyyar kai wajan nisantarsu har ya zama jiki, a nan yana iya lura da duk mummunan aiki ya auna kansa ya gani shin ya bar shi ko kuwa!.
5. Tunani kodayaushe game da halin da ya samu Kansa a kai da kokarin samun mafita kyakkyawa.
6. Tuna alherin da yake cikin kyawawan dabi'u, kamar dadewa a duniya, da yalwar arziki.
Saboda haka wannan ya rage naka mai karatu, sai ka yi kokari domin Allah ba ya canja abin da yake ga mutane sai sun canja abin da yake ga kawukansu.

Kwaskwarima Da Ado
Bahasi na gaba mai zuwa zai kasance ne game da kwaskwarima, domin rai tana bukatar wanka da sabulu na ma'ana don wanke kazantar ma'ana da kawar da daudar ma'anoni da takan nesantar da mutum daga siffantuwa da kyawawan dabi'u. Kuma tana bukatar ado kamar yadda jiki yake bakata, kamar a sanya mata turare na ma'ana domin nisantar daudar ma'anoni da kazantar munanan halaye don cimma burin kai wa ga kamala da siffantuwa da kyawawan dabi'u.
Abu ne sananne ga mutane cewa; idan mutun yana warin dauda sai ya shafa mai, ya sanya kaya masu kyau, ba tare da ya yi wanka ba ya kawar da kazanta da daudar da suke jikinsa, wannan ba ya hana warinsa ya fito a fili.
Amma da zai yi wanka da sabulu, sannan sai ya shafa mai ya sanya turare, ya kawo kayansa masu kyau ya sanya sai ya zama gwanin sha'awa. Haka ma munanan dabi'u da kyawawa suke, wato sai an yi kwaskwarima ta hakika sannan sai kuma a kawo kayan ado da kayan kanshi a sa.
Mun kira wanka da kawar da dauda da kazanta daga jiki ba tareda an shafa mai an sanya turare ba da kwaskwarima, domin yin hakan ba ya zama cikar yin ado, domin idan wani ya yi wanka amma sai ya yi furu-furu saboda rashin shafa mai, kuma ya kawo kayan da ya cire masu dauda ya sake sanyawa a jikinsa har yanzu bai yi adon da ake bukata ba, don haka wanka da kuma kwalliya da ado a hade su ne suke cika kamalar tsafta. Amm dole ne sai an fara yin abin da muke kira kwaskwarima sannan sai kuma a yi ado.
Misali, idan mutum ya bar karya kamar ya wanke daudar jikinsa ne, idan kuma ya yi gaskiya kamar wanda ya sanya kayan ado da na kanshi ne. Shi ya sa, da yana karya, yana kuma gaskiya, da sunansa makaryaci, kamar yadda wancan yake warin dauda duk da kuwa ya sanya kayan ado domin bai yi wanka ba. Ko kuma ya yi wanka amma sai ya mayar da kayan dauda a jikinsa wadanda suke wari. Shi ya sa barin mummuna muke cewa da shi kwaskwarima, aikata kyakkyawa kuma muke cewa da shi yin ado.
Musulunci yana mai matukar kiran mutum domin ya yi kwaskwarima ya wanke daudar nan ta cututtukan rai; kamar karya, da sata da ha'inci, da riya, da sauransu. Kuma hadisai da dama sun zo suna masu hani da tsanani a kai da gargadi domin barin wadannan miyagun halayen.

Karya
Karya ita ce; bayar da labarin da ya saba da hakikanin abin da ya wakana. Kuma tana daga mafi munin sabo kuma uwa ce ta zunubai, kuma tana daga manyan zunubai masu zubar da mutunci.

Nau'o'in Karya
Daga cikin nau'o'in karya akwai:
1. Shaidar zur
2. Rantsuwar karya
3. Saba alkwari

Kashe-kashen Karya
Sannan kuma karya tana iya kasancewa:
1. Ta aiki
2. Ta zance
3. Ta zuciya, kamar sabawa gaskiya a niyya

Karya tana da muni kwarai kuma tana iya kai wa ga abubuwa kamar haka:
1. Tawayar arziki
2. Mummunan zato
3. Zubar da mutunci
4. Jubar da kwarjini
5. Rashin aminci da juna
6. Rashin yarda da alkawarinsa
7. Bata lokaci wajan ware gaskiya da karya
8. Sanya rashin yarda da juna tsakanin mutane
9. Rashin karbar maganar makaryaci ko shaidarsa
10. Tsinuwar Allah a kan makaryaci koda kuwa da wasa yake
Imam Ali (a.s) yana cewa: Wulakanci a duniya da azaba a lahira su ne sakamakon karya. Ya ce: yawan karya tana bata addini, tana kuma girmama zunubi. Ya ce: karya tana kai wa ga munafunci. Ya ce: mai karya abin tuhuma ne a maganarsa koda kuwa hujjarsa tana da karfi. Ya ce: mai karya yana samun abubuwa guda uku sakamakon karyarsa; fushin Allah da wulakancin mutne da kuma kin mala'iku gare shi .
A wasu littattafai ya zo kamar haka ne:
1. Karya ita ce fadin shaidar zur kamar yadda ya zo a kur'ani mai girma
2. Mai karya ba shi da imani
3. Karya sabo ne mai girma
4. Mai karya la'ananne ne
5. Makaryaci fuskarsa zata bakanta
6. Karya ta fi shan giya muni
7. Warin baki a ranar lahira
8. La'anar Allah da mala'iku a kan makaryaci
9. Karya rusa imani ne
10. Karya tana hana zakin imani a zuciya
11. Makaryaci yana cike da kiyayya da mugun nufi a zuciyarsa
12. Makaryaci ba shi da mutunci
13. Karya ita ce mabudin kowane sharri da sabo
14. Karya ita ce mafi munin riba
15. Karya aikin 'yan wuta ne
16. Karya tana sanya mantuwa
17. Karya tana daga manyan sabo
18. Ana haramta wa makaryaci sallar dare
19. Ana haramtawa makaryaci arziki
20. Karya tana kawo tabarwar Allah da wulakancinsa
21. Karya tana nisantarwa daga imani
22. Bai kamata ba a yi abota da makaryaci
23. Allah ba ya shiryar da makaryaci
24. Makaryaci yana tashi ba a surar mutane ba

Abubuwan Da suke Sanya Yin Karya
1. Kwadayi
2. Al'ada
3. Hassada da kiyayya
4. Jahiltar sakamakon karya
5. Mummunar dabi'a da rashin tarbiyya
6. Tawayar mutuntaka, da rashin ganin kimar kai .
7. Lalacewar al'ummar da makaryaci yake rayuwa; kamar zama da makaryata

Maganin Karya
Da akwai abubuwa da suka zo daga littattafai da dama da suke nuna mana hanyoyi da kuma yadda ake maganin karya, wacce take cuta ce mai munin gaske kamar haka;
1. Sanin falalar gaskiya da darajar yin ta
2. Nisantar hanyoyin da zasu kai mu ga karya
3. Barin tarayyar makaryata ko abokanta da su
4. Kokarin karfafa imani da siffantuwa da kyawawan dabi'u
5. Sanin cewa karya abin ki ne kuma abin la'anta ne wajan Allah (s.w.t)
6. La'akari cikin duk abin da zamu furta mu yi magana da shi ko aikata shi
7. Sanin munin karya da kaskancinta da kuma sakamakonta na duniya da lahira
8. Kula da kai da yi mata hisabi kullum da yi mata ukuba a kan yin karya domin ya gani cewa ya tabbatar da barin karya
Inda Karya Ta Halatta
Akwai wuraren da aka halarta yin karya domin wata maslaha babba da ta sanya rinjayar da yin karyar da halarcinta, wadannan wurare sun hada da;
1. Kariya
Kamar kare dukiya da rayuka da mutunci, kamar idan azzalumi zai kwace masa dukiya ko kuma ya kashe shi ko ya kulle shi, ta yadda idan ya yi karya zai iya kubuta daga sharrinsa.
2. Daidaita masu sabani
Idan ya zamanto ba za a iya daidaita tsakanin mutane biyu ko al'umma biyu ba sai ta hanyar yin karya, to wannan yana halarta yin ta.

Zamu ci gaba

13 Rabi'ul awwal 1427
23 Parbardin 1385
12 Afrilu 2006

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)