Muassasar alhasanain (a.s)

Mauludin Annabi

1 Ra'ayoyi 02.0 / 5

Da SunanSa Mad'aukaki Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa
MAULUDIN ANNABI MUHAMMAD (s.a.w) Mauludi: Wani buki ko taro ne domin tunawa da ni'imomin Allah da ya yi mana da rahamarsa da ya saukar zuwa ga bayinsa domin shiriya ga dukkan talikai. Magana kan mauludin Annabi (s.a.w) da sak'on da ya zo da shi abu ne mai matuk'ar k'ima da daraja wanda babu wani abu da ya kai shi muhimmanci, domin kuwa yana nufin bayanin sak'on da d'an Adam ba zai samu tsira ba sai ya yi rik'o da shi. Don haka zamu yi gajeren bayani kan Mauludin Annabi (s.a.w), da Sak'onsa, da kuma Musulmi.
Sai dai an samu wasu masu k'arancin diraya da fahimtar littafin Allah da sunnar Annabinsa (s.a.w) suna ganin munin Mauludi. Jama'a ce da ta tasirantu da koyarwar Banu Umayya masu gaba da Manzon Allah (s.a.w) masu jin haushin shelanta "Ash'hadu anna Muhammdar Rasulul-Lah" da ake yi a kan mimbari sau biyar a kowace rana. (Sharhu Nahajul Balaga: Ibn Abil Hadid; 1/113, 1263. Muwaffak'iyyat: Ibn Bukair. Murujuz Zahab: 1/341. Tahzibut Tahzib: 7/319).
Don haka babu mamaki idan an samu masu rik'o da koyarwar da ta samu daga wannan asalin suna k'iyayya da tunawa da mafi girman ni'ima da Allah ya yi wa bayinsa ta samar da Manzon Allah (s.a.w). Dalilan da ake kafawa domin nuni ga halascin mauludin Annabi (a.s) duk ishara ce kawai ga mai hankali, domin wanda yake musun Mauludi shi ne ake neman ya kawo dalili kan haramcinsa:
A cikin Kur'ani Mai daraja da Sunnar Ma'aiki an yi nuni da abubuwan da suke haramu, kuma Mauludi ba ya daga cikinsu. Don haka mai son k'aryata Mauludi shi ne mai buk'atar ya kawo dalili kan wannan haramcin, domin haramun a bayyane take kuma tana da iyaka, amma abubuwan da aka halatta suna da fad'i kuma ba su da iyaka.
Daga cikin dalilan akwai ayoyi kamar haka: "Ba mu kasance masu azabtar da mutane ba sai mun aiko wani d'an sak'o". Da yake nuni da cewa; Duk abin da babu wani haramncinsa da muka sani a shari'a to halal ne yin sa, sannan a hankalce akwai munin azabtarwa ba tare da bayani ba". Wad'annan lamurran an san su da "Bara'a shar'iyya da ak'aliyya" a cikin ilimin Usulul Fik'hi, da suke nuni da cewa; Duk abin da ba a san haramcin ba daga nassin shari'a kuma babu wani abu da yake nuni da shi, to halal ne. Wad'annan abubuwan fararru sababbi suna da yawa matuk'a kamar; Mauludin Annabi, da Musabak'ar Kur'ani, da kafa k'ungiyoyi domin ayyukan alheri, da wasannin motsa jiki.
Sannan kuma ga wata ayar tana cewa: "...Kuma ba a sanya muku wahala a cikin addini ba..." (Hajji: 78), da take nuni da cewa; Babu wani k'unci da dabaibayi da aka yi mana a kan halaccin abubuwan da haramcinsu ko halaccinsu bai bayyana ba. Don haka hannyenmu a sake suke babu wani k'aidi da k'untata wa kawuka. Sannan kada wani ya ce: Ai tana d'auke hukunci ne ta mayar da shi yalwa ga abin da ya ta'azzara ko ya wahalar? Sai na ce: A nan ma akwai k'unci domin duk haramta alheri a cikinsa akwai k'unci, kuma duk halal a cikinsa akwai yalwatawa, don haka wannan ayar tana shafar abin da muke magana a kai.
Ayar nan da take cewa: "Kuma amma ka zantar da ni'imar Ubangijinka" (Dhuha: 11). Musulmi bai san wata ni'ima da zai ambace ta ya ji dad'i da tafi samuwar Annabi (s.a.w) ba, kamar yadda Allah (s.w.t) bai k'ayyade mana nau'in ni'imomin ba, don haka ne ma ya ce: "Ni'imar Ubanginka" ba tare da ya k'ayyade su ba, sai k'ayyade su ya sanya shi a hannun mutane, domin su ne suka san ni'imomin da ya yi musu. Sai dai ya bayyana musu wasu daga ciki amma fa ba domin ba su san su, sai domin ya k'arfafa wa hankali abin da yake riskarsa domin tunatar da shi ni'imominsa.
A wata ayar kuwa mad'aukaki yana cewa: "Babu wani alheri a cikin ganawarsu -taronsu- sai wanda ya yi umarni da sadaka ko wani kyakkyawa, ko gyara tsakanin mutane...". Ashe akwai wani alheri da ya fi taruwa da tuna wa mutane ni'imomin Allah da rayuwar annabinsu, da nuna musu kyakkyawan koyi a cikinsa?! Yanzu akwai wani mai basira da zai haramta taruwa irin wannan?!
Da wani zai yi raka'a d'ari biyu kowace rana ba tare da ya jingina ta da wata aya ko ruwaya ba, sai dai kawai domin yana son ya aikata alheri don samun lada. Sai ka ga mai irin wannan tunanin musun Mauludi ya ce: Ba komai, da hujjar cewa kyakkyawan abu ne. Sai dai a nan wani yana iya cewa: Ai sallar asham a zahiri kyakkyawa ce domin ibada ce, amma sai ga shi a shari'a tun farko manzon Allah (s.a.w) ya hana ta, sai dai Halifa na biyu ne ya dawo da ita kuma ya yi mata kirari da "Madalla da wannan bidi'a!. Don me Mauludi ba zai zama irin wannan ba!?
Sai in ce masa: Abin da manzon Allah (s.a.w) ya hana shi ne yin ta jam'i a masallatai a dararen Ramadan, da umarnin da ya yi na su yi ta d'aid'aiku -a gidajensu- domin jam'i a sallar nafila ba ya inganta . Don haka ne ma Imam Ali (a.s) ya hana jam'in ta a masallatai a lokacin da ya zo Kufa ya ga mutane suna yi yayin da ya aika Imam Hasan (a.s) ya shelanta haramcinta bisa sunnar Annabi (s.a.w), sai masallaci ya kaure da ihun Wayyo zai kashe sunnar Umar! (Muntahal Mad'alib: Allama Hilli; 358-360). Duba littattafai kan sallar Tarawihi kamar: (Buhari, da Muwatta, da Muslim).
Sai dai Halifa na biyu ya mayar da ita farkon dare, kuma ya sanya mata jam'i, sab'anin umarnin manzon Allah (s.a.w) da ya hana jam'inta ya sanya k'arshen dare ya fi farkonsa. Sai lamarin sallar asham ta bidi'a ya yi kama da mai yin sallar azahar raka'a takwas ne da nufin ninka ladanta, a maimakon ya yawaita ladansa sallarsa zata b'ace ne.
Da wannan ne magana zata fito a fili cewa: Babu wani abu da yin sa yake haram shari'a ba ta yi bayaninsa ba ko da kuwa a zahirinsa wani yana ganin kyawunsa. Don haka idan wani abu ya zo mana wanda muke kokwanton muninsa ko kyawunsa, da hukuncin wad'annan ayoyin da wasunsu ma yana nuna babu laifi a kan yin sa. Sannan mai Mauludi yana kafa hujjarsa da dokokin shari'a ne tabbatattu wad'anda suke iya tabbatar da duk wani alheri ko wane iri ne kuwa har zuwa k'arshen duniya ba tare da da'awar nassi ba.
Sau da yawa da za a canja wa bikin Mauludi suna da wa'azin k'asa, ko tunatarwa, ko ambaton rayuwar Manzo, da mai k'in sa ya karb'a yana mai yarda. Amma saboda kawai an sanya masa kalmar sunan "Murnar Haihuwar Annabi" to sai ya zama laifi babba da zukata suke bak'in ciki da shi. "... Ka ce: Ku mutu da bak'in cikinku"!.
Idan ka ce: Wasu suna aikata haramun lokacin Mauludi, kamar kawo 'yan mata su yi rawa a gaban samari da sauran jama'a? Sai in ce maka: Ya kamata ne ka yi fad'a da haramun da aka sanya a cikin wannan taro, da k'ok'arin ganin an fitar da ita daga ciki, ba fad'a da asalin taron ba. Domin wani lokaci a tarurrukan wa'azi har fad'a ne yake kaurewa, amma ba ya haramta yin taron wa'azi!.
Da zamu tsawaita magana kan Mauludi ne da yana buk'atar littafi ne cikakke, sai dai zamu dakata hakan. Duba a ci gaban mak'alar a bayani mai suna: Sak'on Annabi Muhammad (s.a.w)

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Thursday, March 11, 2010

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)