Muassasar alhasanain (a.s)

Mace a Musulunci

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Mace a Mahangar Musulunci Mahangar musulunci ta girgiza duniya a wancan zamani da ta shelanta cewa; babu bambanci tsakanin mace da namiji sai da tsoron Allah a daidai wannan lokaci a duk fadin duniya daga gabas har yamma babu inda mace take da wata kima ko wani hakki muhimmi a cikin al'ummarta. Haka nan ya zo a Kur'ani mai girma fadin Allah madaukaki: "Ya ku mutane! mu mun halicce ku maza da mata… mafi girmanku a wajan Allah shi ne mafi tsoronku gare shi...".
Mace da namiji a musulunci duk daya ne sai dai a ayyuka da Allah ya bambanta su daidai gwargwadon yadda dabi'ar halittarsu take, amma ta bangaren ruhinsu babu bambanci tsakanin mace da namiji, bambancin ya shafi bangaren jiki ne, shi ya sa a maganar zamantakewar aure mace ba ta da ikon fita waje in dai ba da izinin miji ba, sai kuma lalura kamar ciwo, ko fita ta wajibi kamar neman ilimi da makamantan wannan.
Haka nan musulunci ya duba maslaha a cikin dokokinsa; misali a hukuncin gado musulunci ya kiyaye masalahar duka ne domin dukiyar miji tana komawa kan matarsa da 'ya'yansa ne, amma ta mace ta kebanta da ita ne, kuma bai wajabta mata yaki ba sai ya wajabta shi a kan namiji, haka nan ciyarwa tana kan namiji ne, amma ba a taba jin wani ya ce an zalunci shi namijin ba daga masu son sukan Addini madaukaki na musulunci wadanda ba su fahimci hakikanin dan Adam da sirrin halittarsa ba.

Matsalar Kasashen Musulmi
Matsalar da take faruwa a kasashen musulmi ta al'ada ce ba musulunci ba, misali a wasu wurare idan mace ta yi zina aibi ne da gori ga 'ya'yanta, sabanin namiji. Haka ma auren dole ba kasafai a kan yi wa namiji ba, amma mace da yawa ya kan faru a kanta, wannan kuwa yana komawa al'adu ne ba musulunci ba.
Amma a mahanga ta musulunci duk wanda ya yi laifi shi mai zunubi ne, kuma ya yi abin kunya, ba bambanci tsakanin namiji da mace, haka nan a nufi da hakkin zabi musulunci bai bambanta namiji da mace ba. Musulunci ya daidaita mace da namiji a irada, da iko, da mallaka, da girmamawa, da rike mukami, da kasuwanci, da ibada, da Ilimi, da hankali, da hakkoki, sai ya kebance namiji da wani abu kamar iko a gida da shugabancin iyalinsa, kamar yadda ya kebance ta da hakkin renon danta da shayar da shi, da alfahari, amma da sharadin ya zama gaskiya take fada kamar maganar da take nuna tana alfahari da cewa tana da matsayi da kima gun mijinta. Amma namiji waje daya ne ya halatta ya yi takama da alfahari wato a wajan yaki a gaban makiya, kamar ya yi wa kansa kirari.
Ya kamata ne mu yi bincike a kan dokokin musulunci wanda yana da mas'aloli sama da dubu dari da ishirin da hudu, da tunani cikin irin maslahar da take kunshe a cikinsa ga rayuwar dan Adam da hikimar Allah a ciki, ta nan ne za mu iya gane kiyaye hakki da matsayi da suka shafi mace da babu kamarsa a wani Addini.
Dokokin 'yan'adamtaka da suke kunshe cikin musulunci ba a iya samun irinsu a wani addini, misali; wane Addini ne ya zo da cewa mace ita take da iko ta aurar da kanta ga wanda take so in banda Musulunci, shi ya sa ma aka shardanta yardarta ba ta wani ba, kuma ita ce zata ce: "Na aurar da kaina" . Haka nan tana iya shardanta wa mijin cewa a saki idan ta ga dama tana da hakkin sakin kanta , kuma tana da hakkin yin aiki idan bai sabawa hakkinsa ba kamar likitanci, da injiniyanci, da kasuwanci, kuma tana iya rike duk wani mukami da ake da shi a kasa.
Saboda haka wane Addini ne yake da nazari mai cike da kamala da kula da hakki na mace kamar musulunci? Idan da za ka duba a aikace zaka ga cewa yawancin addinai sun kasa aiki da nazarinsu kan rayuwa, amma musulunci shi ne addini da zai aikatu a aikace kuma ya kai dan Adam ga kamala babu bambantawa namiji ne shi ko mace. Musulunci yana kiyaye maslaha ne na dukkan bangaren mata da maza a dokokinsa, misalin dokar halarcin auren mace sama da daya, da babu wannan doka da mata sun samu kunci a cikin rayuwa kamar maza, kuma da an sami yaduwar fasadi mai yawa a kasashe.
Shari'a ta sanya dokokin daidai da dabi'ar kowanne, misalin saki a bisa ka'ida ta farko yana hannun namiji ne sai dai idan da sharadi tsakaninsu na cewa tana iya sakin kanta , saboda mace idan ta fusata tana da saurin yanke hukunci, saboda haka don maslaha sai musulunci ya sanya irin wannan abubuwa a hannun namiji, shi ya sanya sau da yawa ka kan ji mace ta ce ka sake ni mana amma namiji ya fita sha'anin wannan maganar domin ya san tana cikin fushi ne, da zata sauko, da a ce an sake ta din wannan yana iya jawo mata bakin ciki da ba zata taba mantawa da shi ba musamman idan tana da 'ya'ya. Haka ne musulunci ya gina dokokinsa bisa hikima da maslaha domin cimma hadafi na gina al'umma ta gari mai iya isa zuwa kamala da Allah ya ke so ta kai zuwa gare ta.

Wasu Al'adun Musulmi
Da musulmi sun kiyaye Addininsu kamar yadda Allah ya saukar da shi da ba su samu kunci a kan aiki da Addininsu ba ko sau daya, Allah (s.w.t) yana cewa: "Ba a sanya muku wani kunci ba a cikin Addini" . Amma duba ka ga abin da nisantar Addinin ya janyo wa Duniyar musulmi. A nan zan kawo wasu misalai ne na kuntata wa kai da al'umma take jefa kanta a ciki ta hanyar sabawa takalifin da Allah ya dora mata da daukar sabanin hakan a matsayin addini, ko kuma riko da wasu al'adu. A irin wadannan misalai kana iya ganin yadda musulmi suka sha bamban da koyarwar msulunci ta ainihi kuma suka yi hannun riga da dokokinsa ingantattu sakamkon kauce wa wasiyyar Annabin rahama da suka yi ta biyayya ga Littafin Allah da Ahlul Bait (a.s).
Misali na daya: Wani abin tausayi na wani abu da ya faru sakamakon jahilci da al'adu da abokina ya ba mu labari yana mai cewa: A wani watan Ramadan mai tsananin zafi, ga rana, akwai wata mata da ta haihu daga danginsu, sai dattijon gidansu ya hana a ba ta abinci da ruwa, ya ce: Duk wanda ya ba ta ruwa Allah ya tsine masa! wai tana cikin watan azumi ne, alhalin ga shi ta haihu. Ya ce: Tana ihu tana cewa: A ba ni ruwa! Wuta ce a cikina!! Ya ce: Da magariba ta yi aka ba ta ruwa, yana ratsa makogaronta sai ta fadi sumammiya kuma ta dade ba ta motsa ba.
Misali na biyu: Haka nan na yi tafiya a 1994 a kan hanya na ga abin tausayi, ga tsananin zafi a wani watan azumi, a cikin motarmu akwai wata mata mai shayarwa tana da jariri, nonon da zata ba shi ya yi karanci sabaoda yunwa da kishirwa da suke tare da ita, ga danta yana ta kuka. Sai na ce: Ai kuwa na ji wani malami yana cewa: Idan mace ta kai wannan hali tana iya sha don danta. A nan ne wani makiyayi dattijo da dansa rike da sanduna a kujerar gabana suka waiwayo, idanuwan nan sun yi ja kamar yana shirin cira sanda ya buga mini, yana magana da kausasawa da musuntawa, sai idanuna suka cika da hawaye saboda tausayi. Tsohon nan da mutanen cikin mota sai daka mata tsawa suke yi wai ta lallashe shi ya yi shuru! shi kuwa yaro yana ta kuka, ba nono sai dai ta ba shi ruwa, su kansu ruwan da na taba jarkar da karen motar ya mika mata don ta ba wa yaron sun yi zafi sosai.
Na san ni matafi yi ne idan na yi azumi bai yi ba domin ina bin tafarkin Ahlul Baiti (a.s) ne, kuma na ga zan iya shan ruwa domin ba kodayaushe ne nake zama akwai mutane ba, ga shi kuma na yi ta fiya ta halal kafin rana ta karkata . Da Azahar aka sauka salla na kewaya da tulun kasa dan karami, cike da ruwa don kama ruwa, na sha rabi na yi tsarki da rabi, na koma na karo domin in sha sai na hango matan nan a mota tana ta jijjiga yaron nan, sai tausayi ya sake kama ni, haka nan aka jahilci Addini aka cutar da mata da yara.
Misali na uku: A shekarar 1990 ne a wani wata mai albarka na azumi ne na wata yarinya ce da take neman wani gida, sai na kawo ta wani waje da aka samu wani ya san gidan, amma zata dan jira kadan. Yarinyar ta kasance tana lumfashi daidai saboda zafi da wahalar tafiya, tana mai kakaro yawo fari fat tana tofarwa, tana tsaye sai ta kusa faduwa. Da aka tambaye ta sai ta ce azumi ne ya wahalar da ita. Sai na ce: Don Allah ku ba ta ruwa ta sha don ko ba komai ita matafiyiya ce babu wajabci a kanta. Sai wani cikin fushi ya ce: Sai dai kai ka ba ta, wani ma mamaki yake da ni ma'abocin addini da na san hukuncinsa amma zan ce a ba ta ruwa!
Irin wadannan misalai suna da yawa a kowane bangare na rayuwar musulmi da ya hada da cinikayya, da zamantakewar al'umma, da zamantakewar aure, da auratayya, da ibada, da tattalin arziki, da siyasa. Yawancin irin wannan a kasashen musulmi yana tasowa ne daga rashin sanin musulunci da hukunce-hukuncensa ko kuma cakuda shi da al'adu, shi ya sa ma ba ya shafar mace kawai har ma da namiji. Al'ummarmu tana da bukatar ta mike ta san hukuncin addini kamar yadda Allah ya aiko Manzo (s.a.w) da shi, wannan kuwa yana bukatar jan aiki a kan malamai da ita al'ummar.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai

Rabi'ul Awwl 1424 H.K
Khurdad 1382 H.SH
Mayu 2003, M

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)