Muassasar alhasanain (a.s)

Ayar Soyayya

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

AYAR SOYAYYA

 
 
Mu'assasar Al-Balagh
Tsarawar: Hafiz Muhammad Sa'id
 
Kur’ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
 
Ayar Soyayya
(قُلْ لا أَسْألُكُم عَلَيْهِ أجْراً إلاّ المَوَدَّةَ في القُربى ومنْ يَقْتَرِفْ حسنةَ نزِدْ لهُ فيهَا حسْنًا إنّالله غفورٌ شَكُور)
"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa "Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).
Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta( )".
Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".
A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu( )".
Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa: "Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (s.a.w.a.), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu".
Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma( )wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.
To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (s.a.w.a), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:
1. Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.
2. Babu shakka cewa Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa: "Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".
Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31). "...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)
Da kuma fadinSa cewa: "...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina...". (Surar Nur, 24: 63). "Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah..." (Surar Ahzabi, 33: 21).
3. Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu".
Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce.
Imam Shafi'i yana cewa:
Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina
Ka kira mazaunin al-Nahidhi
Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina
Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa
Idan Rafdhu( ) shi ne son Zuriyar Muhammadu
To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne( ).

Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu( )".
A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (a.s.) cewa wata rana yayin da yake huduba wa mutane ya ce: "Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".
(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (….ومن يقترفْ حسنة) "…kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau…) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti( )".
Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.
Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (s.a.w.a.) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.
Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (s.a.w.a) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake nufi shi ne kiyaye tafarkin al'umma da tsare hanyarta ta akida da shari'a, domin al'umma ta fuskanci Ahlulbaiti bayan da Alkur'ani ya fuskantar da ita zuwa gare su.
Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (s.a.w.a.) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.
Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kan Ahlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.
Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.
 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)