Muassasar alhasanain (a.s)

Jiga-Jigan Addini

Hadafin Halittar Mu

Hadafin Halittar Mu

Idan muka kalli abin da ke kaikawo a wannan duniyar zamuga wasu daga cikin mutane a wannan duniyar bautar gumaka suke yi, wasu daga cikinsu bautar dabbobi sukeyi, idan mukalli afrikanmu akwai addinai masu tarin yawan gaske, a bangaren Amerika suma idan muka waiwaya zamuga suma haka akwai masu bautar gumaka kai harda masu bautar ma

Bayanai

Hujja Kan Tauhidi

Hujja Kan Tauhidi Hujja kan Tauhidi Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (s.w.t) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

Bayanai

ME YASA YAN SHIA SUKE KIRAN SUNAN YAYAN SU DA ABDU ALI KO ABDU ZAHRA

ME YASA YAN SHIA SUKE KIRAN SUNAN YAYAN SU DA ABDU ALI KO ABDU ZAHRA Allah ne kawai ya halasta a bauta masa, Allah nacewa acikin Alqur’ani ﴿ بَلْ اللَّهَ فَاعْبُدْ ﴾ , amma me yasa yan shia suke san ya wa yayan su suna irin abu Ali  ko  Abuzzahra ko kuma Abdul imam? Amma kuma in muka duba zamu ga cewa su imamai da yan shia ke takama dasu basu taba sanya irin wanna sunayen wa yayan su ba. Kuma idan aka ce Abul husai ana nufin hadimin ( خادم الحسين ) Husain ne

Bayanai

Asasin Addini da Rassansa

Asasin Addini da Rassansa Asasin Addini da Rassansa Allah ya shaida cewa; Lalle ne babu abin bautawa sai shi, kuma mala’iku da ma’abota ilimi sun shaida, (ubangiji) yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face shi, Mabuwayi, Mai hikima. Lalle ne addini a wurin Allah shi ne musulunci …[1] Shimfida Da Sunan Allah Mai Rahamn Mai Jin kai Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin annabawa da manzanni da alayensa tsarkaka Muhimmancin bahasi kan akidar musulunci yana kafuwa ne a kan asasin da samuwar musulumi take doruwa a kansa ne, sakamakon haka ne ya sanya zamu ga kur’ani ya sanya akida ita ce kashin bayan kaiwa zuwa ga Allah (s.w.t).

Bayanai

Cigaban Rayuwa Bayan Mutuwa

Cigaban Rayuwa Bayan Mutuwa Mun Tabbatar Da Asali Guda Biyu A Bahsoshin Da Suka Gabata 1-Hakikanin dan Adam shi ne ruhinsa. 2-Mutuwa ba shi ba ne karshen rayuwa, kawai wata kofa ce domin shiga wata duniya, sannan mutum bayan mutuwa zai rayu har abada. Sannan sai asali na uku wanda kuma ya fi sauran muhimmanci a cikin wannan Bahasi,

Bayanai

Hakikan Mutuwa

Hakikan Mutuwa

Bayanai

Rayuwa Bayan Mutuwa

Rayuwa Bayan Mutuwa Shin mutuwa shi ne karshen rayuwa, ta yadda fitilar rayuwar mutum zata dushe da zarar ya mutu, wato bayan mutuwa babu komai sai rashi? Ko kuwa mutuwa wata kofar shiga wata duniya ce wacce take tafi wannan duniyar daraja da haske, kuma hakikanin al'amari ma shi ne, mutum ya tsallake wata gada ce ta yadda ya fadacikin wata sabuwar rayuwa?

Bayanai

Adalcin Allah a Al'umma

Adalcin Allah a Al'umma "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa sai Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)

Bayanai

Hakkokin Allah2

Hakkokin Allah2 Hakkokin Allah Ci gaba daga fayel na farko: Malamai sun yi nuni da hanyoyi masu yawa domin tabbatar da samuwar Allah madaukaki wanda zamu iya yin ishara da wasu daga ciki da suka hada da samuwar halitta da kuwa samuwar tsarin da take a kansa,

Bayanai

Hakkokin Allah

Hakkokin Allah Hakkokin Allah (s.w.t) Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsu"

Bayanai

Ajali da Wa'adi

Ajali da Wa'adi Ajali Ko Cikar Wa'adi Sau da yawa akan yi magana kan ajali a matsayin wani abu da Allah ya sanya shi a matsayin hanyar katse rayuwar mutum ta wannan duniyar da ciratarsa zuwa lahira ko kuma duniyar barzahu.

Bayanai

Tabbatar Kiyama

Tabbatar Kiyama Hafiz Muhammad hfazah@yahoo.com Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bayanai

Zuriyar Annabi

Zuriyar Annabi ZURIYAR ANNABI       Mu'assasar Al-Balagh Tsarawar: Hafiz Muhammad Sa'id   Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .   Ahlul-baiti (Zuriyar Manzon Allah) Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ni mai bari muku nauyaya biyu ne tare da ku, littafin Allah da dangina, mutanen gidana (ahlulbaiti) wadanda in kun yi riko da su ba za ku taba bata ba a bayana har abada, kuma lalle ne su biyun ba za su rabu da juna ba har su riske ni a bakin tafki". Ahlulbaiti (a.s) makaranta ce mai haske kuma taurari ne a sararin samaniyar addinin Musulunci madaukaki. Su ne ja-goranci cikakke mai koyi da Manzon Allah (s.a.w.a.), sun sha daga ilminsa a gidansa suka tashi, sannan suka rayu bisa tafarkinsa. Suna masu kira zuwa ga Littafin Allah da kuma riko da sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). Suna nuna misalai madaukaka ta hanyar halayensu, suna kira zuwa ga gaskiya, ba sa karkace mata ko da kamar dan yatsa. Kamar yadda hadisin Manzon tsira ya bayyana mana su (Ahlulbaiti) tagwaye ne na Alkur'ani mai girma, ba sa rabuwa domin su ne hakikanin tamka na Alkur'ani da duk abin da yake tattare da shi na ilminsa da tarbiyyarsa. Domin haka Alkur'ani ya ambace su a sarari: ( إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً ) "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen Babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33) Domin yawan ayoyin da suka sauka game da Ahlulbaiti (a.s) da kuma hadisai bayyanannu wadanda aka yi furuci da su, lallai Ahlulbaiti (a.s) sun zama abin kauna ga zukatan musulmi na kasashe da zamunna daban-daban, suna kwarara zuwa gare su domin su sha daga tabkin ilminsu kuma su nemi karuwa daga hasken masaniyyarsu. Duk wanda ya kyautata karatun tarihin Ahlulbaiti (a.s) da aikin da suka yi na ilmi, zai san rawar da suka taka, wacce ita ce ta kan gaba, zai kuma san aiki mai girma da suka yi. Lallai sun yi matukar dagewa wajen kiyaye tsarkakar shari'a da kuma tsare asalin akidar Musulunci har ma suka sadaukar da kansu da yin jihadi domin tabbatar da ka'idojin nan madaukaka a aikace da ja-gorancin al'umma bisa shiriyar wadannan ka'idojin. A kullum tarihin Ahlulbaiti (a.s) madaukaka yana bayyana a matsayin rayayyiyar baiwa wadda take da tasiri ga tunanin al'umma da kiyayewarta, tana wadatar da rayuwarta tana kuma daukaka wayewarta. Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) su ne kudubin al'umma, su ne rumfa matattara mai hada kan al'umma don gyara. A cikin wannan matakaicin littafin, mun yi kokarin bayyana sashin abubuwan da rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ya kunsa da kuma abin da ya ta'allaka da martabarsu da rawar da suka taka a tarihi. Game da gabatar da wannan littafin, muna kwadaitar da 'yan'uwa musulmi da su samu fa'idantuwa da shiryarwa ta Ahlulbaiti (a.s) da aiki da ita da komawa wajen wannan ja-gaban da kuma koyi da shi da tsayawa sahu guda don fuskantar 'yan rahoton nan masu kokarin raba kan musulmi da wargaza hadin kansu, a dai-dai lokacin da al'ummarmu ta Musulunci take shiga gumurzu mai tsanani tsakaninta da 'yan mulkin mallaka da 'yan gurguzu da yahudawan sahayoniyya, wannan gumurzun kuwa sakamako ne na tabbatar da sakon Musulunci da kuma (kokarin) rayuwa karkashin inuwar adalcin Ubangiji. Muna kuma kira ga al'ummar musulmi da su fuskantar da dukkan karfinsu wajen kira zuwa ga Musulunci da kare tsarkakan abubuwansa da tauye damar wadanda suka saba shuka sabani da watsa gubar banga-ranci tsakanin al'ummar musulmi. Ya ku al'ummar Annabi Muhammadu mai girma! Ya masoya Ahlulbaiti! Ya zama wajibi a gare ku da ku hada kai da kuma karfinku waje guda, domin kuwa wannan al'umma, al'umma ce guda, kuma daukakarku da kara-marku ba sa tabbata sai da riko da sakon Musulunci da kuma aiki da Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). "Kuma ka ce: ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9:105) Ahlulbaiti (a.s.) suna ne mai haskakawa, kuma daukaka ce madawwamiya, sannan suna ne da yake abin kauna ne ga duk rai mai kaunar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma ya yi imani da shi, kuma yake rayuwa bisa shiriyarsa (s.a.w.a). Hakika musulmi sun san wannan madaukakin suna cikin tarihi da kuma cikin martabar nan da take rataye da Alkur'ani mai girma, tun lokacin da Alkur'anin ya yi furuci da wannan sunan mai albarka, kuma ya sanyawa wannan tauraruwan (Ahlulbaiti) lakabin da babu irinsa a duniyar dan Adam: ( إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً ) "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33) Da saukar wannan aya mai albarka wani tafarki ya ayyana a matsayin wani abin dogaro da mafuskanta a rayuwar Musulunci. Alkur'ani ya juya fuskoki zuwa ga wannan tafarki tare da tabbatar da dukkan haske a bisa wannan a kan gaba wajen ja-goranci. Har ila yau ya bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) za su taka a rayuwar al'ummar musulmi, ya kuma kebance su da nufin tsarkakewa, abin karfafawa daga Gwani, Masani. Lalle wannan aukuwa mai girma tana da wata kebantacciyar ma'ana a rayuwar al'umma da gina tarihinta da wayewarta. Wannan ma'ana kuwa dukkan masu bincike da tahkikin Musulunci da kuma fagen rayuwar siyasar wannan al'umma sun san da ita. Hakika wadannan ayoyin sun ayyana wata cibiyar harkar tarihi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.), harkar da ta dace da al'ada da tsarin hujjar da Musulunci ke dogara da shi. Wannan ya biyo bayan baiwar da Allah Ya yi wa tatattun nan masu albarka (Ahlulbaiti), baiwa ta tsarka-kewa daga zunubai da sabo da kuma laifi. Hakika Alkur'ani mai girma ya tabbatar musu da mafificiyar darajar falala da kuma mafi girman martabobin cancanta, da'a da shugabanci a rayuwa ta Musulunci wacce falsafarta a rayuwa ita ce: "Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa". (Surar Hujurat, 349:13) Babu shakka duk wanda ya bibiyi Alkur'ani mai girma da sunnar Annabi (s.a.w.a) tsarkakkiya zai samu cewa mutanen gidan Annabi mai daraja (s.a.w.a) suna da matsayi kebantacce da muhalli mabayyani. Za a ga cewa shugabannin wannan al'umma da malamanta da masu fassara da masu ruwaya da ma'abuta tarihi da malaman fikihu da masu yawan ibada duk suna ba da labarin wannan matsayi na Ahlulbaiti (a.s) ta dukkan fuskoki da hanyoyi. Lallai littattafan hadisi, tarihi, tafsiri da na adabi da wake da darajoji wadanda musulmi daga mazhabobi da hanyoyin ilmi daban-daban suka wallafa, sun bayyana kebantaccen matsayin da muhalli muhimmi na Ahlulbaiti (a.s). Wadannan littattafai suna magana a kan daukakar wannan itaciya mai albarka. Ana auna imanin mumini ne da kaunar Annabi (s.a.w.a) da Ahlubaitinsa da rige-rigen sanar da al'umma darajojin Alayen Manzo masu daraja da nutsar da kaunarsu cikin rayuka, da bayyana gajin hakuri da jin ciwon halayyar wadanda suka yi gaba da mutanen gidan Annabi mai daraja, kuma suka cutar da su da ababen kunya da kuma bala'u. Lallai mutanen wannan gida tamkar tauraruwa ce wacce babu kamarta, domin ilmin da suke dauke da shi da kuma takawa da halayen kwarai da darajoji madau-kaka da kare Musulunci da ilminsu da kuma daukar takobi da yaki da zalunci da keta haddi. Domin haka ne musulmi suka dace a kan cewa babu wani daga cikin wannan al'ummar da ya mallaki mukami da daukaka da daraja irin wanda Allah Ya kebance Ahlulbaiti da su…su kadai Allah Ya kebance da tsarkakewa daga dauda da zunubi: "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" Kuma su kadai ne Allah Ya kebance da wajabta kaunarsu a kan wannan al'ummar Ya kuma sanya kaunar ta su wani hakki na Annabi (s.a.w.a) a kan al'umma:"...Ka ce: "Ban tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta...". (Surar Shura, 42:23) Kuma su kadai ne Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta yi musu salati a cikin salloli biyar, Yana gwama ambatonsu da ambaton ManzonSa (s.a.w.a): "Lalle Allah da Mala'ikunSa suna yin salati wa Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56) Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riga ya koyawa al'um-marsa yadda za ta yi salati a gare shi da alayensa yayin da suka tambaye shi: Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Rasulallah? Sai ya ce da su: "Ku ce: Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma" To babu wanda yake da wadannan darajoji da siffofi cikin wanna al'umma face su. Wannan shi ya sanar da mu daukakar Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da wajibcin kaunarsu da koyi da su da kuma tafiya bisa turbarsu. Ba don kome ne Alkur'ani ya jaddada a kan mutanen wannan gida, ya kuma bayyana matsayi da mukaminsu ba, sai domin a yi koyi da su bayan Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma riko da sonsu da karbar (dukkan ilmi da shiriya) daga gare su. Babu abin da yasa Alkur'ani ya sanar mana da Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar da ya nuna mana su face domin wasu dalilai na akida da abin da ya danganci sakon Musulunci kaco-kam, dalilan da suke sa dukkan wani musulmi ya dora tunani mai zurfi da lura da kuma kokarin riskar da kwakwalwarsa hakikanin wannan jama'a (Ahlulbaiti) da take a kan gaba wajen karbar sako. Wannan jama'a kuwa ita ce Allah Ya yi wa baiwar matsayi na shugabanci a cikin al'umma, bayan Alkur'ani da Manzo (s.a.w.a) sun yi masu wannan gabatarwa. A nan gaba za mu bijiro da gabatarwar da Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki da shuwagabannin musulmi da malamansu da masu adabi suka yi wa wannan itaciya mai albarka, zuriyar mai tsarki, wacce ita ce madugun al'umma.   Ahlul-bait a kur'ani Mai Girma Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka: 1. Amfani da sunansu na isdilahi wanda shi Alkur'-anin ya sanya musu. Wani lokaci yakan ambace su da Ahlulbaiti kamar yadda ya zo cikin Ayar Tsarkakewa, wani lokaci kuma yana ambatonsu da al-Kurba kamar yadda ya zo cikin ayat al-Muwadda (ayar kauna). Ayoyi masu yawa sun sauka da wadannan ma'anoni sannan Sunna ta yi bayaninsu ga al'umma a lokacin da ayoyin suke sauka daga bisani kuma masu fassara da masu ruwaya suka nakalto bayanin cikin littattafansu manya da kanana. Kiyaye da kuma rubuta dukkan ababen da suka kebanta ga Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan saukan ayoyi da dama da suke ambaton falalar Ahlulbaiti (a.s), matsayinsu, yabo da fuskantar da al'umma zuwa gare su; wani zubin a ambaci darajojin a hade, kamar yadda ya zo cikin Ayar Mubahala (Surar Ali Imrana, 3: 61) da Ayar Ciyarwa cikin Surar Dahri da sauransu. Wani zubin kuwa a rarrabe kamar yadda ya zo cikin Ayar Wilaya (Surar Ma'ida, 5: 55). Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi: A NAN MUNA BUKATAR MAI KARATU YA DUBA SAURAN FAYALOLI MASU MAGANA KAN WANNAN MAUDU'IN.    

Bayanai

Matsayin Ahlul-baiti-2

Matsayin Ahlul-baiti-2 Kur'ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)

Bayanai

Matsayin Ahlul-baiti-1

Matsayin Ahlul-baiti-1 Kur'ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bayanai

Imamanci da Jagoranci

Imamanci da Jagoranci Imamancin Imamai Mun yi imani cewa Imamanci wato; halifancin Annabi (S.A.W) yana daga cikin Usuluddin shika-shikan addini wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su,

Bayanai

Ayar Wilaya

Ayar Wilaya Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bayanai

Ayar Tsarki

Ayar Tsarki Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bayanai

Ayar Soyayya

Ayar Soyayya AYAR SOYAYYA Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bayanai

Ayar Salati

Ayar Salati AYAR SALATI "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima"

Bayanai

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)